Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kiyayya Tana a Ko’ina a Duniya

Kiyayya Tana a Ko’ina a Duniya

Mutane a duk duniyar nan suna fama sosai don ƙiyayya.

Labaran yadda ake nuna ƙiyayya sai daɗa karuwa suke. Wasu suna hakan ta kalamansu a intane ko kafofin sada zumunta, da saƙonni da suke turawa da dai sauransu. Ban da haka ma, ana nuna bambanci kuma ana yin zagi da barazana da ɓarna sosai a yau. Ƙiyayya tana a ko’ina!

Wannan mujallar ta bayyana abin da mutum zai yi don ya daina nuna ƙiyayya. Hakan abu ne mai yiwuwa sosai don akwai mutane da yawa a faɗin duniya da suka daina nuna ƙiyayya. Kuma a kwana a tashi, ƙiyayya za ta zama labari.