Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA MUTUM ZAI YI DON YA DAINA KIN MUTANE

4 | Ka Nemi Taimakon Allah don Ka Daina Kin Mutane

4 | Ka Nemi Taimakon Allah don Ka Daina Kin Mutane

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce:

“Halin da ruhun Allah yake haifar shi ne ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da aminci, da tawali’u, da kuma shan ƙarfin sha’awar jiki.”​GALATIYAWA 5:​22, 23.

Abin da Ayar Take Nufi:

Da taimakon Allah mutum zai iya daina ƙin mutane. Ruhu mai tsarki da Allah yake bayarwa zai iya taimaka mana mu zama da halaye masu kyau ko da muna ganin ba za mu iya canja halinmu ba. Don haka, abin da zai fi mana alheri shi ne mu dogara da Allah, maimakon mu yi ƙoƙarin daina ƙiyayya da kanmu. Idan muka dogara da Allah, mu ma za mu ga gaskiyar abin da manzo Bulus ya faɗa cewa: “Cikakken ikon da ya fi duka daga wurin Allah ne, ba daga wurinmu ba.” (2 Korintiyawa 4:7) Har ma za mu iya cewa: “Taimakona zai fito daga wurin Yahweh.”​—Zabura 121:2.

Yadda Za Ka Bi Wannan Ayar:

“Jehobah ya gyara ni. Na canja daga azzalumi zuwa mutum mai son zaman lafiya.”—WALDO

Ka roƙi Jehobah ya ba ka ruhu mai tsarki. (Luka 11:13) Ka ce ya taimake ka ka kasance da halayen kirki irin nasa. Ka bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da halaye da suke kawar da ƙiyayya, irin su ƙauna da salama da haƙuri da kuma kamun kai. Ka yi ƙoƙarin nuna waɗannan halayen a rayuwarka. Kuma ka riƙa yin tarayya da mutanen da su ma suke yin hakan. Waɗannan mutane za su ‘iza ka ka nuna ƙauna kuma ka yi nagarta.’​—Ibraniyawa 10:24.