Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Abin da Mutum Zai Yi don Ya Daina Kin Mutane

Abin da Mutum Zai Yi don Ya Daina Kin Mutane

Kalmar Allah, wato Littafi Mai Tsarki, za ta iya taimaka wa mutum ya gyara halinsa. (Ibraniyawa 4:12) Mutane da yawa sun daina nuna ƙiyayya domin sun bi abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Bari mu bincika abubuwa huɗu daga Littafi Mai Tsarki da suka taimaka wa mutane su daina ƙiyayya.