Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Shin yadda rayuwar nan za ta kasance ke nan?

Kana gani muna cika saurin mutuwa ne?

Ka taɓa yin tunani cewa ma’anar rayuwa kawai ita ce yin wasa da aiki da aure da samun yara da kuma tsufa? (Ayuba 14:1, 2) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mutane masu hikima ma sun yi irin wannan tunanin.—Karanta Mai-Wa’azi 2:11.

Shin rayuwa tana da ma’ana kuwa? Ya kamata mu fara yin wannan tambayar, Yaya rayuwa ta soma? Yadda Allah ya halicci ƙwaƙwalwarmu da kuma jikinmu ya sa mutane da yawa sun gaskata cewa akwai Mahalicci mai hikima. (Karanta Zabura 139:14.) Idan haka ne, yana da manufa mai kyau na halittar mu. Sanin wannan manufar za ta taimaka mana mu yi rayuwa mai ma’ana.

Me ya sa aka halicci mutum?

Allah ya albarkaci iyayenmu na farko kuma ya ba su aiki mai kyau. Manufarsa ita ce su cika duniya da ’ya’ya, su sa ta zama aljanna kuma su rayu har abada a cikinta.—Karanta Farawa 1:28, 31.

An jinkirta manufar Allah sa’ad da iyayenmu suka taka dokarsa. Amma Allah bai fid da rai a kanmu ba kuma bai canja manufarsa ba. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Allah yana kan aiki tuƙuru don ya ceci mutane masu aminci kuma ya aiwatar da manufarsa ga duniya. Saboda haka, Allah yana so ka ji daɗin rayuwa yadda ya nufa tun asali! (Karanta Zabura 37:29.) Yin nazarin Littafi Mai Tsarki zai sa ka koyi yadda za ka amfana daga nufin Allah.