Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Sani?

Ka Sani?

Kamar yadda yake a cikin Littafi Mai Tsarki, mene ne kalmar nan bāba take nufi?

Hoton Bāba a Asiriya

A wasu lokuta, ana amfani da kalmar nan bāba don a kwatanta namijin da aka yi masa dandaƙe. A dā, an yi wa wasu maza dandaƙe don sun yi wani laifi ko bayan an ci su a yaƙi ko kuma sa’ad da suka zama bayi. Ana amfani da mazan da aka yi musu dandaƙe wajen gadin matan sarki ko kuma wani attajiri. Alal misali, bāba Hegai da Sha’ashgaz sun yi aiki ne a matsayin masu gadin matan Sarki Ahasurus ko kuma Xerxes na Ɗaya.—Esther 2:3, 14.

Amma ba dukan waɗanda Littafi Mai Tsarki ya kira su bāba ne aka yi musu dandaƙe ba. Wasu masana sun ce kalmar tana da manufa da yawa, tana iya nufin wani babban ma’aikaci a fadar sarki. Wataƙila abin da ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce da Ebed-melech, abokin aikin Irmiya bāba kuma ya ce da wani Bahabashe wanda Filibus ya yi ma wa’azi ma hakan. Ebed-melech babban ma’aikacin sarki ne don yana da ’yancin zuwa wurin Sarki Zedekiya. (Irmiya 38:7, 8) Kuma an kwatanta Bahabashen a matsayin ma’ajin sarauniya da ya je “Urushalima . . . garin yin sujada.”—Ayyukan Manzanni 8:27.

Me ya sa makiyaya a zamanin dā suke ware tumaki daga awaki?

Sa’ad da Yesu yake kwatanta hukuncin da za a yi a nan gaba, ya ce: ‘Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukaka tasa . . . zai kuma ware mutane dabam-dabam, kamar yadda makiyayi ke ware tumaki da awaki.’ (Matta 25:31, 32, Littafi Mai Tsarki) Me ya sa makiyaya suke ware tumaki daga awaki?

Ana yawan yin kiwon awaki da tumaki tare da rana. Amma daddare, ana shinge su saboda namomin daji ko ɓarayi ko kuma sanyi. (Farawa 30:32, 33; 31:38-40) Ana ware tumaki daga awaki domin kada awakin su ji wa tunkiya ko kuma ’ya’yansu rauni. Littafin nan All Things in the Bible ya ce: “Makiyaya suna kuma ware tumaki daga awaki sa’ad da suke tatse nono da yanke gashinsu da kuma sa’ad da suka haihu.” Saboda haka, kwatancin Yesu sananne ne ga masu sauraronsa da ke zama a wuraren da ake kiwo kamar a ƙasar Isra’la ta dā.