Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

Na Yi Rayuwar Banza Sosai a Dā

Na Yi Rayuwar Banza Sosai a Dā
  • SHEKARAR HAIHUWA: 1952

  • ƘASAR HAIHUWA: AMIRKA

  • TARIHI: MAI ZAFIN RAI

RAYUWATA A DĀ:

Na yi girma a birnin Los Angeles, Kalifoniya a ƙasar Amirka kuma na zauna a unguwar da ke cike da ’yan iska da kuma masu shan miyagun ƙwayoyi. Iyayena sun haifi yara shida kuma ni ne na biyu a cikinsu.

Mahaifiyarmu ta rene mu a wani coci mai suna evangelical church. Amma sa’ad da nake tsakanin shekara sha uku zuwa sha tara, na soma yin rayuwar banza. A ranar Lahadi nakan yi waƙa a cocinmu. A wasu ranakun kuma sai in je fati, in sha miyagun ƙwayoyi kuma in yi lalata.

Ina yawan fushi da kuma zafin rai. Ina amfani da kowane abu don in ji ma mutane rauni. Abin da na koya a coci bai taimaka mini ba sam. Nakan ce, “Ramako na Ubangiji ne, kuma da ni zai cim ma hakan!” Sa’ad da nake makarantar sakandare a ƙarshen shekara ta 1960, na shiga wani rukunin da ke yaƙi don ’yancin ɗalibai. Wani rukunin siyasa da ke yaƙi don ’yancin masu farar hula da ake kira Black Panthers ne ya rinjaye ni yin hakan. A lokatai da yawa mukan ta da rigima har ma a rufe makarantar na ɗan lokaci.

Ban gamsu da zanga-zanga da nake yi ba, saboda haka, na soma aikata laifi don ina ƙiyayyar mutane. Alal misali, akwai lokacin da muka kalli wani fim da ya nuna yadda ’yan Amirka suke wulaƙanta ’yan Afirka a dā. Da muka ji haushi, sai muka yi wa turawan da ke gidan siliman dūkan tsiya. Bayan haka, sai muka shiga unguwoyi muna neman turawan za mu yi wa dūka.

Da na kusan shekara ashirin, ni da ƙannena biyu da kuma yayana mun ƙware sosai a aikata manyan laifuffuka. Saboda haka, muna yawan samun saɓani da hukuma. Ƙanina yana cikin wani sanannen rukuni mai ta da rikici, kuma ni ma ina bin su. Rayuwata sai daɗa muni take yi.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA:

Ina da abokin da iyayensa Shaidun Jehobah ne. Sun gayyace ni zuwa taronsu kuma na je. Wannan ne ƙaro na farko da na ga cewa halin Shaidun Jehobah dabam ne. Na lura cewa kowa yana amfani da Littafi Mai Tsarki a taron kuma matasa ma suna yin jawabai! Na yi farin cikin sanin cewa sunan Allah Jehobah ne kuma na ji suna amfani da shi. (Zabura 83:18) Babu wata wariya a ikilisiyar duk da cewa mutanen daga kabilu dabam-dabam ne.

Da farko na so halartan taron Shaidun Jehobah amma ban so yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su ba. Akwai wata rana da na je taron  Shaidun Jehobah da yamma, amma abokaina kuma sun je fati. A wurin suka kashe wani matashi don ya ƙi ya ba su kwat ɗinsa. Washegari, sai suka yi ta cika baki game da kisan da suka yi. Sa’ad da aka kai su kotu, ba su ɗauka cewa sun aikata babban laifi ba. A sakamakon haka, an yi wa yawancinsu ɗaurin rai da rai. Na yi farin ciki cewa ban bi su a wannan ranar ba. A lokacin ne na tsai da shawarar canja rayuwata da kuma soma nazarin Littafi Mai Tsarki.

Da yake na saba gani ana nuna wariyar kabila, hakan ya sa ni mamaki sosai sa’ad da na lura cewa halin Shaidun Jehobah dabam ne. Alal misali, akwai lokacin da wani bature ya tafi ƙasarsu kuma ya bar yaransa a hannun wani baƙin fata don ya kula da su. Ban da wannan ma, na ga wani iyalin turawa sun ce wa wani matashi baƙin fata da ke neman gida ya zo ya zauna da su. Hakan ya sa na gaskata cewa Shaidun Jehobah ne suka yi daidai da kwatancin Yesu a littafin Yohanna 13:35 cewa: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” Wannan ya sa na yarda cewa na sami addini na gaskiya.

Nazarin Littafi Mai Tsarki da nake yi ya sa na fahimta cewa ya kamata in canja ra’ayina. Na yi ƙoƙari sosai in canja salon rayuwata don in yi zaman lafiya da mutane kuma na tabbata cewa wannan ita ce hanyar da ta dace. (Romawa 12:2) Da sannu-sannu na samu ci gaba kuma a watan Janairu na shekara ta 1974, na yi baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah.

Na yi ƙoƙari sosai in canja salon rayuwata don in yi zaman lafiya da mutane kuma na tabbata cewa wannan ita ce hanyar da ta dace

Amma har bayan na yi baftisma, na ci gaba da yin ƙoƙari don in rage zafin rai. Alal misali, na taɓa bin wani ɓarawo da ya saci rediyo a motata sa’ad da nake wa’azi. Da ya ga cewa na yi kusa da shi, sai ya yar da rediyon ya gudu. Sa’ad da na gaya wa waɗanda muke wa’azi tare da su abin da ya faru, sai wani dattijo a cikinsu ya tambaye ni, “Stephen, da a ce ka kama shi me za ka yi masa?” Tambayar ta sa in san cewa ina bukatar in yi ƙoƙari don in zauna lafiya da mutane.

A watan Oktoba ta 1974, na soma hidima ta cikakken lokaci, ina yin sa’o’i ɗari a kowane wata don koya wa mutane Littafi Mai Tsarki. Daga baya, an gayyace ni yin hidima a hedkwatar Shaidun Jehobah da ke Brooklyn, a Amirka. A shekara ta 1978, na koma birnin Los Angeles don in kula da mahaifiyata da ke rashin lafiya. Bayan shekara biyu, sai na auri wata mai suna Aarhonda. Ta taimaka mini sosai wajen kula da mahaifiyata har zuwa lokacin da ta rasu. Bayan haka, sai aka gayyace mu zuwa Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead kuma da muka sauke karatu, an tura mu zuwa ƙasar Panama, inda muka yi hidima a matsayin masu wa’azi a ƙasashen waje.

Tun da na yi baftisma, na fuskanci wasu yanayoyin da za su iya sa in yi faɗa. Amma na yi ƙoƙarin guje wa mutanen da suke so su sa ni fushi ko kuma ina yin amfani da wata dabara don kada abin ya jawo faɗa. Matata da mutane da yawa sun yaba mini don yadda na bi da waɗannan yanayoyin kuma yadda na bi da yanayin ya ba ni mamaki sosai. Na san cewa ba da ikona nake yin waɗannan canje-canjen ba. Maimakon haka, na tabbata cewa Littafi Mai Tsarki ne ya taimaka mini in yi hakan.—Ibraniyawa 4:12.

YADDA NA AMFANA:

Littafi Mai Tsarki ya taimaka mini in yi rayuwa mai ma’ana kuma in zauna lafiya da mutane. Na daina dūkan mutane yanzu, amma ina taimaka musu su san Allah. Har ma na yi nazarin Littafi Mai Tsarki da wani da muke yawan faɗa da shi sa’ad da muke makaranta. Bayan da ya yi baftisma, mun soma zama a daƙi ɗaya da shi. Har wa yau, mu abokai ne sosai. Tun daga lokacin har zuwa yau, mun yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane sama da 80 kuma sun zama Shaidun Jehobah.

Ina godiya ga Jehobah sosai don ya taimaka mini in yi rayuwa mai ma’ana da farin ciki a tsakanin ’yan’uwana Shaidun Jehobah.