Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ZAI YIWU A SAKE RAYUWA—BAYAN MUTUWA?

Mene ne Ke Faruwa da Mu Bayan Mutuwa?

Mene ne Ke Faruwa da Mu Bayan Mutuwa?

“Na ɗauka cewa idan mutum ya mutu yana iya zuwa wurare uku, wato sama ko gidan wuta ko kuma purgatori. Na san cewa ban cancanci zuwa sama ba kuma ban yi abubuwan da suka isa in shiga gidan wuta ba. Ban san ainihi abin da purgatori yake nufi ba. Ban taɓa ganin kalmar a cikin Littafi Mai Tsarki ba, ƙage ne kawai.”—In ji Lionel.

“An koya mini cewa dukan waɗanda suka mutu suna zuwa sama amma ban gamsu da hakan ba. Na ga kamar mutuwa ce ƙarshen kome, wato babu wani bege ga matattu.” —In ji Fernando.

Ka taɓa yin irin wannan tambayar: ‘Mene ne ke faruwa da mutane sa’ad da suka mutu? Matattu suna shan azaba a wani wuri ne? Za mu sake ganinsu kuwa? Ta yaya za mu tabbata da hakan?’ Don Allah ka yi la’akari da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da wannan batun. Bari mu fara bincika yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta mutuwa. Bayan haka, sai mu tattauna begen da Littafi Mai Tsarki ya yi magana a kai.

 Mene ne yanayin matattu?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Masu-rai sun san za su mutu: amma matattu ba su san kome ba, ba su kuwa da sauran lada; gama ba a ƙara tuna da su ba. Dukan abin da hannunka ya iske na yi, ka yi shi da ƙarfinka; gama babu wani aiki, ko dabara, ko ilimi, ko hikima, cikin kabari inda za ka.” *Mai-Wa’azi 9:5, 10.

Kabari wuri ne da ake saka mutane sa’ad da suka mutu, ba wuri ne na zahiri ba domin mutanen da suke wurin ba su san kome ba kuma ba sa aiki. Wane ra’ayi ne Ayuba mai aminci yake da shi game da Kabari? Ya yi asarar dukiyarsa da ’ya’yansa a rana ɗaya kuma Shaiɗan ya addabe shi da gyambuna. Ya roƙi Allah: “Da fa za ka yarda ka ɓoye ni cikin Lahira [‘Kabari,’ New World Translation].” (Ayuba 1:13-19; 2:7; 14:13) Hakika, Ayuba bai ɗauka cewa Kabari gidan wuta ba ne inda wahalar da yake sha za ta daɗa ƙaruwa ba. Maimakon haka, ya san cewa wurin hutu ne.

Akwai wata hanya kuma da za mu iya koya game da yanayin matattu. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da labaran mutane takwas da suka tashi daga mutuwa da za mu iya yin bincike a kansu.—Ka duba akwatin nan “ Tashin Matattu Takwas da Aka Ambata a Littafi Mai Tsarki.”

Babu ko ɗaya cikin mutane takwas da aka ambata da ya je sama ko kuma gidan wuta. Da a ce waɗanda aka tashe su sun je irin waɗannan wuraren, kana ganin da ba su ba mutane labari ba? Kuma da ba a rubuta hakan a cikin Littafi Mai Tsarki don mutane su karanta ba? Ba a rubuta kome game da hakan a cikin Littafi Mai Tsarki ba. Babu shakka, waɗannan mutane takwas ba su ce kome ba game da wannan batun. Me ya sa? Domin a lokacin da suka mutu ba su san kome ba, kamar sun yi barci ne mai zurfi. Hakika a wasu lokuta, Littafi Mai Tsarki yakan kwatanta mutuwa da barci. Alal misali, amintattun mutane kamar Dauda da Istafanus sun “yi barci,” wato sun mutu.—Ayyukan Manzanni 7:60; 13:36.

To, wane bege ne matattu suke da shi? Za su iya farka daga wannan barci kuwa?

^ sakin layi na 7 An yi amfani da kalmar nan “Kabari” a wuraren da kalmomin Ibranancin nan “Sheol” da kuma na Helenanci “Hades” suka bayyana. Wasu juyin Littafi Mai Tsarki sun yi amfani da kalmar nan “jahannama” amma Littafi Mai Tsarki bai koyar da cewa ana ƙone mutane a wuta ba.