Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Sani?

Ka Sani?

Wane ’yanci ne manzo Bulus ya samu domin ya zama ɗan ƙasar Roma?

Bulus ya ce: “A ɗaukaka ƙarata gaban Kaisar!”

Zama ɗan ƙasar Roma yana ba mutum ’yanci da kuma zarafi da yawa a kowane wuri da ya shiga a cikin daular. Duk mutumin da ke da ’yancin zama ɗan ƙasar Roma yana ƙarƙashin dokar ƙasar ne ba na biranen da ke ƙasar ba. Sa’ad da aka tuhume shi da aikata laifi, za a iya shari’anta shi a birnin, amma yana da ’yancin ɗaukaka ƙara zuwa babban kotun ƙasar. Idan kuma an yanke masa hukuncin kisa, zai iya ɗaukaka ƙarar zuwa wajen sarkin ƙasar.

Irin wannan ’yancin ne ya sa wani ɗan siyasa a ƙarni na farko kafin haihuwar Yesu, mai suna Cicero ya ce: “Kama ɗan ƙasar Roma laifi ne; yi masa duka mugunta ne; kashe shi kuma ɗaya ne da wani ya kashe mahaifinsa ko mahaifiyarsa ko kuma wani danginsa.”

Manzo Bulus ya yi wa’azi sosai a Daular Roma. Ya yi amfani da ’yancinsa na ɗan ƙasar Roma a hanyoyi uku: (1) Ya gaya wa alƙalan Filibi cewa sun taka ’yancinsa ta wajen yi masa duƙa. (2)  Sa’ad da yake Urushalima, ya faɗi cewa shi ɗan ƙasar Roma ne domin kada a doke shi. (3) Ya ɗaukaka ƙararsa zuwa gaban Kaisar, wanda shi ne sarkin Roma, domin ya yanke hukuncin da kansa.—Ayyukan Manzanni 16:37-39; 22:25-28; 25:10-12.

Ta yaya ake biyan makiyaya a zamanin dā?

Allon dutsen da aka rubuta kwangilar tumaki da kuma awaki da aka saya, a wajen shekara ta 2050 K.Z.Y.

Yakubu uban iyali ya yi kiwon garken kawunsa Laban shekara 20. Yakubu ya fara yi wa Laban aiki na shekara 14 domin ya ba shi ’ya’yansa biyu ya aura, bayan haka, sai ya yi aiki na shekara 6 domin ya sami tumaki. (Farawa 30:25-33) Littafin nan Biblical Archaeology Review ya ce: “Marubuta a zamanin dā da kuma waɗanda suka karanta Littafi Mai Tsarki sun san da irin wannan yarjejeniyar, kamar wanda Yakubu da Laban suka yi.”

Duwatsun da aka rubuta kwangila a zamanin dā da aka tono a birnin Nuzi da Larsa da kuma wasu wurare a ƙasar Iraƙi sun nuna irin wannan yarjejeniyar. A irin wannan kwangilar, ana rarraba tumaki kowace shekara. Makiyaya suna karɓan riƙon tumaki kuma ana rubuta adadinsu da shekarunsu da kuma jinsinsu. Bayan shekara guda, mai tumakin yana karɓan ulu da madara da kindirmo da kuma ƙananan tumaki da dai sauransu. Duk ƙarin da aka samu na makiyayin ne.

Ƙaruwar da aka samu ya dangana ga adadin tunkiyar da aka ba makiyayin. Ana sa rai cewa tunkiya ɗari za su haifi ’ya’ya 80. Makiyayin zai biya idan wani tunkiya ko rago ya ɓace. Saboda haka, yana bukata ya kula da dabbar da yake kiwo.