Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Dogara ga Jehobah Kuma Ka Yi Alheri

Ka Dogara ga Jehobah Kuma Ka Yi Alheri

‘Ka dogara ga Jehobah kuma ka yi nagarta [alheri] . . . ka lizimci aminci.’ZAB. 37:3.

WAƘOƘI: 13363

1. Jehobah ya halicce mu da ikon yin mene ne?

JEHOBAH ya halicce mu a hanyar da za mu iya yin tunani don mu magance matsalolinmu kuma mu yi shiri don abubuwan da za su iya faruwa a nan gaba. (Mis. 2:11) Ya ba mu ikon yin abubuwan da za su iya taimaka mana mu cim ma maƙasudanmu. (Filib. 2:13) Allah ya halicce mu yadda za mu iya sanin abin da ya dace da wanda bai dace ba. Shi ya sa idan muka yi abin da bai dace ba, zuciyarmu za ta riƙa damun mu.Rom. 2:15.

2. Yaya Jehobah yake son mu yi amfani da baiwar da ya ba mu?

2 Jehobah yana son mu yi amfani da baiwar da ya ba mu a hanyar da ta dace. Me ya sa? Domin yana ƙaunar mu kuma ya san cewa idan muka yi amfani da waɗannan baiwa, za mu amfana sosai. Jehobah ya gaya mana sau da sau a Littafi Mai Tsarki cewa mu riƙa yin amfani da baiwa da ya ba mu a hanyar da ta dace. Alal misali, a cikin Nassosin Ibrananci, ya ce: “Tunanin mai himma zuwa yalwata kaɗai suke nufa,” kuma a wani  wuri ya ce: “Dukan abin da hannunka ya iske na yi, ka yi shi da ƙarfinka.” (Mis. 21:5; M. Wa. 9:10) A cikin Nassosin Helenanci na Kirista kuma ya ce: “Yayin da muke da dama fa, bari mu aika nagarta zuwa ga dukan mutane,” kuma ya daɗa cewa: “Yayin da kowa ya karɓi baiko, kuna yi wa junanku hidima da shi.” (Gal. 6:10; 1 Bit. 4:10) Babu shakka, Jehobah yana son mu yi iya ƙoƙarinmu don mu amfani kanmu da kuma wasu.

3. Wace kasawa ce mutane suke da shi?

3 Duk da haka, Jehobah ya san cewa muna da kasawa kuma ba za mu iya kawar da ajizanci da zunubi da kuma mutuwa da kanmu ba. Ban da haka ma, ba za mu iya tilasta wa mutane su yi abin da muke so ba, don kowa yana da ‘yancin yin abin da yake so. (1 Sar. 8:46) Ko da muna da ilimi sosai ko wata baiwa, mu yara ne a gaban Jehobah.Isha. 55:9.

Sa’ad da kake fuskantar matsaloli, ka dogara ga Jehobah kuma ka yi alheri

4. Me za mu tattauna a wannan talifin?

4 A dukan abubuwan da muke yi, ya kamata mu dogara ga Jehobah don ya ja-gorance mu, ya tallafa mana kuma ya taimaka mana mu iya yin abubuwan da suka fi ƙarfin mu. Amma muna bukata mu yi iya ƙoƙarinmu don mu magance matsalolinmu kuma mu taimaka ma wasu. (Karanta Zabura 37:3.) Babu shakka, muna bukata mu dogara ga Jehobah kuma mu yi nagarta. Ƙari ga haka, muna bukata mu kasance da “aminci.” Don haka, bari mu tattauna wasu darussa da za mu koya daga labarin Nuhu da Dauda da kuma wasu bayin Jehobah masu aminci da suka dogara gare shi kuma suka ɗauki matakin da ya dace. Kamar yadda za mu gani, hakan ya ƙunshi sanin abin da za su iya yi da wanda ba za su iya yi ba da kuma ɗaukan matakin da ya dace.

SA’AD DA MIYAGU SUKA KEWAYE MU

5. Mene ne ya faru a zamanin Nuhu?

5 Nuhu ya yi rayuwa a lokacin da duniya ta “cika da zalunci.” (Far. 6:4, 9-13) Ya san cewa Jehobah zai kawo ƙarshen muguwar duniyar a lokacin. Duk da haka, Nuhu ya yi baƙin ciki sosai don yadda mugunta ta yi yawa. A lokacin, Nuhu ya fahimci cewa akwai wasu abubuwan da zai iya yi da waɗanda ba zai iya yi ba.

Ba ya so ya ji wa’azin (Ka duba sakin layi na 6-9))

6, 7. (a) Mene ne Nuhu ba zai iya yi ba? (b) Ta yaya yanayinmu ya yi daidai da na Nuhu?

6 Abin da Nuhu ba zai iya yi ba: Ko da  yake Nuhu ya yi wa’azin saƙon da Jehobah ya ba shi, bai tilasta wa mutanen zamaninsa su karɓi saƙon ba, kuma bai iya ya sa Rigyawar ta zo kafin lokacin da Allah ya ƙayyade ba. Amma Nuhu ya tabbata cewa Jehobah zai cika alkawarinsa na kawar da mugunta kuma ya san zai yi hakan a lokacin da ya dace.Far. 6:17.

7 Mu ma muna rayuwa ne a duniyar da take cike da mugunta kuma mun san cewa Jehobah ya yi alkawarin halaka ta. (1 Yoh. 2:17) Amma ba za mu iya tilasta wa mutane su karɓi saƙon ‘bishara ta Mulkin’ ba. Kuma ba abin da za mu iya yi da zai sa “ƙunci mai-girma” ya soma kafin lokacin da Allah ya ƙayyade. (Mat. 24:14, 21) Kamar Nuhu, muna bukatar bangaskiya don mu kasance da tabbaci cewa Allah zai ɗauki mataki nan ba da daɗewa ba. (Zab. 37:10, 11) Mun tabbata cewa Jehobah ba zai ƙara ko ɗaya rana a kan lokacin da ya ce zai hallaka wannan muguwar duniyar ba.Hab. 2:3.

8. Ta yaya Nuhu ya mai da hankali ga abubuwan da zai iya yi? (Ka duba hoton da ke shafi na 7.)

8 Abin da Nuhu zai iya yi: Maimakon Nuhu ya yi sanyin gwiwa don abubuwan da bai zai iya yi ba, ya mai da hankali ga abubuwan da zai iya yi. Kuma da yake shi “mai-shelar adalci” ne, ya idar da saƙon da Allah ya ba shi. (2 Bit. 2:5) Babu shakka, yin hakan ya taimaka wa Nuhu ya kasance da bangaskiya sosai. Ban da haka ma, ya yi amfani da ƙarfinsa da kuma hikimarsa don ya yi aikin da Allah ya ba shi na sassaƙa jirgi.Karanta Ibraniyawa 11:7.

9. Ta yaya za mu iya bin misalin Nuhu?

9 Mu ma mun shagala da yin “aikin Ubangiji,” kamar yadda Nuhu ya yi. (1 Kor. 15:58) Wannan aikin ya haɗa da gina da kuma gyara wuraren ibada, taimakawa a manyan taro da ofisoshin Shaidun Jehobah ko kuma ofisoshin fassara. Mafi muhimmanci ma, muna wa’azi da ƙwazo don mun san cewa wannan aikin zai sa mu kasance da bege game da nan gaba. Wata ‘yar’uwa mai aminci ta ce: “Idan kana gaya wa mutane game da albarkar da Mulkin Allah zai kawo, za ka fahimci cewa mutane ba su da bege kuma suna ganin ba za su iya rabuwa da matsaloli ba.” Babu shakka, yin wa’azi yana sa mu riƙa tuna da begenmu.  Ban da haka ma, yana taimaka mana mu riƙa bauta wa Jehobah duk da matsalolin da muke fuskanta.1 Kor. 9:24.

SA’AD DA MUKA YI ZUNUBI

10. Ka bayyana zunubin da Dauda ya yi.

10 Jehobah ya ce Sarki Dauda ‘mutum ne da yake ƙauna ƙwarai.’ (A. M. 13:22) Dauda ya bauta wa Allah da aminci, amma a wasu lokuta, ya yi zunubi mai tsanani. Ya yi zina da Bath-sheba kuma ya ƙulla a kashe mijinta Uriah a yaƙi don ya ɓoye zunubinsa. Abin taƙaici shi ne, Uriah ne ya kai wasiƙar da ke ɗauke da saƙo cewa a kashe shi. (2 Sam. 11:1-21) Amma asirin Dauda ya tonu. (Mar. 4:22) Mene ne Dauda ya yi sa’ad da aka fallasa shi?

Zunubin da muka yi a dā (Ka duba sakin layi na 11-14)

11, 12. (a) Mene ne Dauda bai iya canjawa bayan da ya yi zunubi? (b) Mene ne Jehobah zai iya yi mana idan mun yi zunubi kuma muka tuba da gaske?

11 Abin da Dauda bai iya yi ba: Dauda bai iya canja abin da ya yi ba. Kuma ba zai iya guje wa sakamakon zunubinsa ba. Hakika, zai yi fama da wasu cikin waɗannan munanan sakamakon har ƙarshen rayuwarsa. (2 Sam. 12:10-12, 14) Babu shakka, ya kamata ya kasance da bangaskiya sosai domin ya tabbatar wa kansa cewa idan ya tuba da gaske, Jehobah zai gafarta masa kuma zai taimaka masa ya jimre da mummunar sakamakon zunubinsa.

12 Da yake mu ajizai ne, muna yin zunubi. Wasu suna da tsanani, wasu kuma ba su da tsanani. A wasu lokuta, ba za mu iya canja kuskuren da muka yi ba. Abin da muke bukata shi ne, mu ci gaba da jimrewa da sakamakon. (Gal. 6:7) Amma mun gaskata da abin da Allah ya faɗa cewa, idan mun tuba da gaske, Jehobah zai taimaka mana sa’ad da muke fuskantar matsaloli, ko da hakan don zunubin da muka yi ne.Karanta Ishaya 1:18, 19; Ayyukan Manzanni 3:19.

13. Me ya taimaka wa Dauda ya sake kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah?

13 Abin da Dauda zai iya yi: Dauda ya amince Jehobah ya taimaka masa don ya gyara dangantakarsa da shi. Hanya ɗaya da ya sami taimako ita ce ta wurin amincewa da gyarar da annabi Nathan ya yi masa. (2 Sam. 12:13) Ban da haka ma, Dauda ya yi addu’a ga Jehobah, ya faɗi laifinsa kuma ya roƙe shi ya nuna masa jin ƙai. (Zab. 51:1-17) Dauda ya koyi darasi daga abin da ya faru, maimakon barin zunubinsa ya riƙa damunsa. Kuma bai sake yin waɗannan zunuban ba. Bayan wasu shekaru, Dauda ya mutu yana da aminci kuma Allah zai tuna da shi.Ibran. 11:32-34.

14. Wane darasi za mu iya koya daga labarin Dauda?

14 Wane darasi ne za mu iya koya daga labarin Dauda? Idan muka yi zunubi, ya kamata mu tuba da gaske kuma mu roƙi Jehobah ya gafarta mana. Wajibi ne mu faɗa wa Allah zunubanmu. (1 Yoh. 1:9) Ban da haka ma, muna bukatar mu nemi taimakon dattawa. (Karanta Yaƙub 5:14-16.) Idan muka ɗauki waɗannan matakan, hakan zai nuna cewa mun amince da alkawarin da ya yi cewa zai taimaka mana kuma ya gafarta mana. Ƙari ga haka, zai dace mu guji maimaita zunubin, mu ci gaba da bauta wa Jehobah kuma mu sa ido a kan abubuwan da ya yi mana alkawarinsu a nan gaba.Ibran. 12:12, 13.

A WASU YANAYI

Rashin lafiya (Ka duba sakin layi na 15)

15. Wane darasi ne muka koya daga misalin Hannatu?

15 Za ka iya yin tunanin wasu bayin Allah masu aminci da suka dogara ga Jehobah kuma suka ɗauki matakan da  suka dace. Alal misali, Hannatu ba ta iya magance matsalarta na rashin haihuwa ba. Amma ta tabbata cewa Jehobah zai iya ƙarfafa ta, saboda haka, ta ci gaba da yin ibada a mazauninsa kuma ta yi wa Allah addu’a. (1 Sam. 1:9-11) Babu shakka, wannan misali ne da ya kamata mu bi, ko ba haka ba? A lokacin da muke rashin lafiya ko fuskantar matsalolin da muke ganin sun fi ƙarfinmu, zai dace mu gaya wa Jehobah abin da yake damunmu don zai kula da mu. (1 Bit. 5:6, 7) Ƙari ga haka, zai dace mu riƙa halartan taro da yin wasu ayyukan ibada don mu sami ƙarfafa.Ibran. 10:24, 25.

Yara da suka daina bauta wa Jehobah (Ka duba sakin layi na 16)

16. Wane darasi ne iyaye za su iya koya daga misalin Sama’ila?

16 Shin akwai darasin da iyayen da yaransu suka bar Jehobah za su iya koya? Sama’ila bai tilasta wa yaransa su bi ƙa’idodin Jehobah da ya koya musu ba. (1 Sam. 8:1-3) Ya bar kome a hannun Jehobah. Amma shi kansa ya kasance da aminci ga Jehobah. (Mis. 27:11) A yau, iyaye da yawa sun sami kansu a irin wannan yanayin. Suna da tabbaci cewa Jehobah yana farin ciki idan masu zunubi suka tuba, kamar yadda mahaifin da ke labarin mubazzari ya yi. (Luk. 15:20) Duk da haka, waɗannan iyayen suna ƙoƙari su kasance da aminci ga Jehobah da begen cewa wata rana, yaransu za su dawo wurin Jehobah.

Talauci (Ka duba sakin layi na 17)

17. Me ya sa labarin gwauruwar nan yake da ban ƙarfafa a gare mu?

17 Ka yi tunanin gwauruwa matalauciya da ta yi rayuwa a zamanin Yesu. (Karanta Luka 21:1-4.) Ba za ta iya yin kome game da munafunci da ake yi a cikin haikalin ba. (Mat. 21:12, 13) Ƙari ga haka, ba za ta iya magance matsalarta na talauci ba. Duk da haka, ta “zuba anini biyu . . . iyakar abin zaman gari da take da shi.” Wannan mace mai aminci ta dogara ga Jehobah ya biya bukatunta ta wurin saka ayyukan ibada a kan gaba. Wannan tabbacin da take da shi ya motsa ta ta ba da gudummawa don bauta ta gaskiya. Mu ma mun tabbata cewa idan muka saka al’amuran Mulkin a kan gaba, Allah zai biya bukatunmu.Mat. 6:33.

18. Ka ba da misalin wani da yake bauta wa Jehobah a zamaninmu da ya kasance da ra’ayin da ya dace.

18 Wasu da yawa cikin bayin Jehobah a yau ma sun kasance da irin wannan bangaskiya kuma sun ɗauki matakan da suka dace. Ka yi la’akari da misalin wani ɗan’uwa mai suna Malcolm, wanda ya kasance da aminci har mutuwarsa a shekara ta 2015. Shi da matarsa sun yi shekaru da yawa suna bauta wa Jehobah kuma sun fuskanci matsaloli sosai. Ya ce: “Ba za mu iya sanin ainihin abin da zai faru a rayuwarmu ba. A wasu lokatai, yanayi zai iya yin wuya sosai. Amma Jehobah yana wa mutanen da suke dogara gare shi albarka.” Wace shawara ce Malcolm ya bayar? Ya ce: “Ka yi addu’a [ga Jehobah] don ya taimaka maka ka yi aiki tuƙuru da kuma nasara a hidimarsa. Ka yi tunani a kan abin da za ka iya yi, ba abin da ba za ka iya yi ba.” *

19. (a) Me ya sa jigonmu na shekara ta 2017 ya dace? (b) Ta yaya za ka yi amfani da jigon shekara ta 2017 a rayuwarka?

19 Yayin da wannan zamanin yake “daɗa” muni, za mu fuskanci matsaloli da yawa. (2 Tim. 3:1, 13) Saboda haka, bai kamata mu bar matsaloli su sa mu sanyin gwiwa ba. Maimakon haka, zai dace mu dogara ga Jehobah kuma mu ɗauki matakin da ya dace. Shi ya sa jigonmu na shekara ta 2017 shi ne: Ka Dogara ga Jehobah Kuma Ka Yi Alheri.Zab. 37:3.

Jigonmu na shekara ta 2017: Ka Dogara ga Jehobah Kuma Ka Yi Alheri.Zab. 37:3

^ sakin layi na 18 Ka duba Hasumiyar Tsaro na 15 ga watan Oktoba, 2013, shafuffuka na 17-20.