Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shin Kasancewa da Tawali’u Tsohon Yayi Ne?

Shin Kasancewa da Tawali’u Tsohon Yayi Ne?

“Wurin masu-tawali’u akwai hikima.”MIS. 11:2.

WAƘOƘI: 3869

1, 2. Me ya sa Allah ya ƙi sarki Saul? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

SARKI SAUL yana da tawali’u sa’ad da ya soma sarauta. (1 Sam. 9:1, 2, 21; 10:20-24) Amma daga baya, ya yi wasu abubuwa da suka nuna cewa shi mai girman kai ne. A lokacin da Filistiyawa suka zo su yaƙi Isra’ilawa, Samai’ila ya gaya wa sarki Saul cewa zai zo ya yi hadaya ga Jehobah kafin su yi yaƙin. Amma da suka jira kuma suka ga kamar Sama’ila ya makara, sai Isra’ilawa suka soma jin tsoro. Da Saul ya ga haka, sai ya yi hadayar da bai kamata ya yi ba kuma Jehobah bai ji daɗi hakan ba sam.1 Sam. 13:5-9.

2 Da Sama’ila ya dawo daga Gilgal, sai ya gaya wa sarki Saul cewa abin da ya yi bai dace ba. Maimakon Saul ya roƙi gafara, sai ya soma kāre kansa yana ba da wasu hujjoji cewa bai yi laifi ba. (1 Sam. 13:10-14) Wannan abin da ya yi ya ɓata sarautarsa har ma da dangantakarsa da Jehobah. (1 Sam. 15:22, 23) Ko da yake shi mai tawali’u ne sa’ad da ya fara sarauta amma daga baya ya kasance mai girman kai.1 Sam. 31:1-6.

3. (a) Yaya mutane da yawa suke ɗaukan tawali’u? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu sami amsoshinsu?

 3 A duniyar nan da ake yawan gāsa, mutane suna ganin cewa idan suka kasance da tawali’u, ba za su yi suna ko nasara a rayuwa ba. Hakan ya sa sun zama masu girman kai. Alal misali, wani ɗan wasan fim da ya zama ɗan siyasa ya ce: “Tawali’u ko sauƙin kai bai shafe ni ba, kuma ba zan taɓa zama mai sauƙin kai ba.” Me ya sa yake da muhimmanci Kirista ya kasance mai tawali’u? Mene ne tawali’u ya ƙunsa kuma mene ne bai ƙunsa ba? Ta yaya za mu kasance da tawali’u duk da matsi da kuma kaluɓale? A wannan talifin, za mu sami amsoshin tambayoyi biyu. A talifi na gaba za a tattauna tambaya ta uku.

ME YA SA TAWALI’U YAKE DA MUHIMMANCI?

4. Mene ne mutum mai girman kai zai iya yi?

4 Littafi Mai Tsarki ya nuna bambancin da ke tsakanin tawali’u da girman kai. (Karanta Misalai 11:2.) Shi ya sa Dauda ya roƙi Jehobah ya kiyaye shi “daga wurin masu-girman kai.” (Zab. 19:13) Me zai iya nuna cewa mutum yana da “girman kai”? Mutum mai girman kai yakan yi abubuwan da ba a ba shi izinin yinsu ba kuma fahariya ce take sa shi ya yi hakan. Da yake mu ajizai ne, mukan yi fahariya a wasu lokuta. Kuma kamar yadda misalin Sarki Saul ya nuna, idan muka ci gaba da yin abubuwa da fahariya, za mu ɓata dangantakarmu da Allah. Littafin Zabura 119:21 ya ce Jehobah yana: “Tsauta ma masu-girman kai.” Me ya sa?

5. Me ya sa fahariya take da muni sosai?

5 Yin fahariya ya fi yin kura-kurai muni. Waɗanne dalilai ne suka nuna hakan? Da farko, idan muna fahariya yana nuna cewa ba mu ɗauki Jehobah a matsayin Maɗaukaki ba. Na biyu, idan muka yi abin da ba a ba mu izinin yinsa ba, za mu samu saɓani da mutane. (Mis. 13:10) Na uku, a lokacin da mutane suka gane cewa muna da fahariya, za mu sha kunya sosai. (Luk. 14:8, 9) Masu fahariya ba sa samun ribar kome, shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce mu kasance masu tawali’u.

MENE NE KASANCEWA DA TAWALI’U YA ƘUNSA?

6, 7. Yaya mai tawali’u zai riƙa yin abubuwa?

6 Kirista mai tawali’u ba ya yin fahariya amma yana ganin wasu sun fi shi. (Filib. 2:3) Mutum mai tawali’u ya san abubuwan da zai iya yi da abubuwan da ya cim ma da kuma kura-kuransa. Ban da haka ma, yakan karɓi shawara daga mutane. Kasancewa mai tawali’u yana faranta wa Jehobah rai.

7 A cikin Littafi Mai Tsarki, tawali’u yana nufin sanin abubuwan da za mu iya yi da waɗanda ba za mu iya yi ba. A asalin yaren da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, an mai da hankali a kan yadda wannan halin zai sa mu bi da mutane da ladabi kuma mu riƙa nuna musu alheri.

8. Ta yaya za mu san cewa mun soma yin abubuwa da fahariya?

8 Ta yaya za mu soma tunani ko kuma yin abubuwa da fahariya? Ka yi la’akari da wasu abubuwan da za su sa mu gane hakan. Idan muna fahariya don ayyukan da muke yi a ƙungiyar Jehobah. (Rom. 12:16) Ko kuma mu riƙa yin wasu abubuwa don mu yi suna a gaban mutane. (1 Tim. 2:9, 10) Ƙari ga haka, za mu iya cusa wa mutane ra’ayinmu  kuma mu tilasta musu su bi. (1 Kor. 4:6) A yawancin lokaci yayin da muke yin hakan, ba za mu iya sanin cewa muna wuce gona da iri ba.

9. Me ya sa wasu suka soma yin fahariya? Ka ba da misali.

9 Kowannenmu zai iya soma yin fahariya idan ya bar ayyukan jiki suka shawo kansa. Halaye kamar su son kai da kishin wasu ko kuma yawan fushi sun sa mutane da yawa su soma fahariya. Wasu a Littafi Mai Tsarki kamar su Absalom da Uzziah da kuma Nebuchadnezzar sun bar sha’awoyin jiki su shawo kansu kuma Jehobah ya ƙasƙantar da su saboda hakan.2 Sam. 15:1-6; 18:9-17; 2 Laba. 26:16-21; Dan. 5:18-21.

10. Me ya sa bai dace mu riƙa shar’anta mutane ba? Ka ba da misali.

10 Akwai wasu dalilai kuma da za su iya sa mutane su soma yin fahariya. Ka yi la’akari da wasu labaran Littafi Mai Tsarki da ke Farawa 20:2-7 da kuma Matta 26:31-35. Shin ayyukan jiki ne ya sa Abimelech da Bitrus suka yi fahariya? Shin don ba su da cikakken bayani ko kuma sun yi hakan ne ba tare da tunani ba? Da yake ba za mu iya sanin abin da ke zuciyar mutane ba, zai dace mu guji shar’anta su.Karanta Yaƙub 4:12.

SANIN MATSAYINMU

11. Ta yaya tawali’u yake taimaka mana mu san cewa kowannenmu yana da aiki a ƙungiyar Jehobah?

11 Idan muka san ayyukanmu a ƙungiyar Jehobah, za mu kasance da tawali’u. Jehobah ya ba kowannenmu abin da zai yi a ƙungiyarsa da yake shi mai tsari ne. Kowa a ikilisiya yana da amfani domin dukanmu muna bukatar juna. Jehobah ya nuna mana alheri shi ya sa ya ba mu baiwa da kuma basira dabam-dabam. Za mu iya amfani da waɗannan baiwa don mu girmama Jehobah kuma mu taimaka ma wasu. (Rom. 12:4-8) Idan muna da tawali’u, za mu yi amfani da kyautar da Jehobah ya ba mu yadda yake so.Karanta 1 Bitrus 4:10.

Me za mu iya koya daga misalin Yesu sa’ad da aka ba mu ƙarin aiki? (Ka duba sakin layi na 12-14)

12, 13. Me ya kamata mu tuna idan yanayinmu yana canjawa a kai a kai a ƙungiyar Jehobah?

12 Babu shakka, aikin da Allah ya ba mu zai iya canjawa bayan wani lokaci. Ka yi la’akari da misalin Yesu. Da farko, yana tare da Jehobah. (Mis. 8:22) Bayan haka, sai ya taimaka wajen halittan wasu mala’iku da sama da ƙasa da kuma mutane. (Kol. 1:16) Daga baya, Yesu ya zo duniya, aka haife shi jariri marar wayo kafin ya girma. (Filib. 2:7) Ya koma sama bayan da ya ba da ransa a matsayin fansa, kuma Allah ya naɗa shi Sarki a shekara ta 1914. (Ibran. 2:9) Kuma za a sake canja hidimarsa. Bayan Yesu ya yi sarauta na shekara dubu, zai ba Jehobah sarautar don “Allah ya zama duka cikin duka.”1 Kor. 15:28.

13 Shawarwari dabam-dabam da muke yi a rayuwa zai iya sa yanayinmu ya canja. Alal misali, kai marar aure ne kafin ka yi aure, ko ba haka ba? Shin kana da yara yanzu? Kuma da shigewar lokaci, shin ka sauƙaƙa rayuwarka kuma ka soma hidima ta cikakken lokaci? Dukan abubuwan da aka ambata ɗazu suna zuwa da nawaya. A wasu lokuta, canjin yanayi zai iya sa mu faɗaɗa hidimarmu ko kuma mu rage abubuwan da muke yi a hidimarmu ga Jehobah. Shin kai matashi ne ko kuma tsoho? Shin kana rashin lafiya ne ko kuma kana da ƙoshin lafiya? A koyaushe Jehobah yana neman hanyar da zai yi amfani da  mu yadda ya dace a hidimarsa. Yana son mu riƙa yin abubuwa daidai gwargwado kuma yana jin daɗin hidimar da muke yi masa.Ibran. 6:10.

14. Ta yaya tawali’u zai taimaka mana mu kasance da farin ciki a duk yanayin da muka sami kanmu?

14 Yesu ya kasance da farin ciki a ayyukan da ya yi kuma mu ma za mu iya yin hakan. (Mis. 8:30, 31) Mutum mai tawali’u yana kasancewa da wadar zuci don ayyukan da yake yi a ikilisiya. Ba ya neman matsayi ruwa a jallo ko kuma ya ji kishin wasu don ayyuka ko matsayin da suke da shi. Maimakon haka, yakan mai da hankali ga ayyukan da yake yi kuma yana jin daɗin yinsu don ya san Jehobah ne ya ba shi ayyukan. Ban da haka ma, yana farin ciki da baiwa ko matsayin da Jehobah ya ba wasu. Kasancewa masu tawali’u yana taimaka mana mu girmama mutane kuma mu tallafa musu.Rom. 12:10.

ABIN DA TAWALI’U BA YA NUFI

15. Wane darasi za mu koya daga misalin Gideon?

15 Wani misali mai kyau na wanda ya kasance da tawali’u shi ne Gideon. Da farko da mala’ikan Jehobah ya zo masa, Gideon ya gaya masa cewa shi mafi ƙanƙanta ne. (Alƙa. 6:15) Bayan da Gideon ya karɓi aikin da Jehobah ya ba shi, ya mai da hankali don ya fahimci abin da zai yi kuma ya dogara ga Jehobah don ya taimaka masa. (Alƙa. 6:36-40) Gideon yana da gaba gaɗi sosai. Ya mai da hankali sa’ad da yake yin  aikin da Jehobah ya ba shi kuma ya yi hakan da basira. (Alƙa. 6:11, 27) Bai yi amfani da matsayinsa don ya yi suna ba. A maimakon hakan, bayan da ya idar da aikin da aka ba shi, sai ya koma gida.Alƙa. 8:22, 23, 29.

16, 17. Mene ne mai tawali’u zai yi tunani a kai sa’ad da yake neman ƙarin hidima a bautarsa ga Jehobah?

16 Kasancewa da tawali’u ba ya nufin ƙin biɗan ƙarin hidima a bautarmu ga Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu samu ci gaba a hidimarmu ga Jehobah. (1 Tim. 4:13-15) Shin hakan ya ƙunshi canja irin hidimar da muke yi ne? A’a. Jehobah zai albarkaci hidimar da muke masa yanzu kuma zai taimaka mana mu sami ci gaba. Zai dace mu ci gaba da yin amfani da baiwa da Allah ya ba mu kuma mu riƙa yin ayyuka masu kyau.

17 Mutum mai tawali’u zai yi tunani sosai don ya ga ko zai iya yin wani aiki da aka ba shi. Zai iya tambayar kansa, shin idan na soma wannan aikin zan sami lokacin yin abubuwa masu muhimmanci ne? Shin zai iya barin wasu su yi wasu ayyukan da yake yi a yanzu don ya sami zarafin yin sabon aikin da aka ba shi? Mutum mai tawali’u zai iya barin wasu su yi aikin bayan ya yi tunani ko la’akari sosai a kan waɗannan tambayoyin. Yin addu’a da kuma sanin abin da za mu iya yi zai taimaka mana mu guji yin abubuwa da suka fi ƙarfinmu. Kuma idan mun ga ba za mu iya yin aikin ba, zai dace mu bar wasu su yi.

18. (a) Mene ne tawali’u zai taimaka mana mu yi sa’ad da muka sami ƙarin aiki? (b) Ta yaya littafin Romawa 12:3 zai taimaka wa mutum ya zama mai tawali’u?

18 Misalin Gideon ya koya mana cewa idan muka sami ƙarin aiki, zai dace mu dogara ga Jehobah don idan ba mu yi hakan ba, ba za mu yi nasara ba. Kuma Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu yi ‘tafiya da tawali’u tare da Allahnmu.’ (Mi. 6:8) Saboda haka, idan muka sami ƙarin aiki, zai dace mu yi tunani da addu’a sosai a kan abin da Jehobah yake koya mana a Kalmarsa da kuma ƙungiyarsa. Wajibi ne mu gyara halinmu don ya jitu da na Jehobah. Bai kamata mu manta cewa duk wani abu da muka cim ma a ƙungiyar Jehobah don tawali’unsa ne da kuma taimakonsa. (Zab. 18:35) Idan muka zaɓa mu riƙa bauta wa Jehobah da tawali’u, Allah zai taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace.—Karanta Romawa 12:3.

19. Waɗanne dalilai ne za su sa mu kasance da tawali’u?

19 Mutum mai tawali’u yana girmama Jehobah da yake shi ya halicce mu kuma shi ne Maɗaukaki a sama da ƙasa. (R. Yoh. 4:11) Tawali’u zai taimaka mana mu yi farin ciki a duk wani aiki da aka ba mu a hidimar Jehobah. Idan muna da tawali’u za mu riƙa daraja ‘yan’uwanmu kuma hakan zai sa mu kasance da haɗin kai. Tawali’u zai sa mu riƙa yin tunani sosai kafin mu tsai da wata shawara don mu guji yin kura-kurai. Babu shakka, waɗannan dalilan sun sa mun fahimci cewa ya kamata bayin Allah su kasance da tawali’u don Jehobah yana jin daɗin waɗanda suke da wannan halin. Shin me za mu iya yi a lokacin da yin hakan ba shi da sauƙi? Talifi na gaba zai taimaka mana mu san yadda za mu ci gaba da kasancewa da tawali’u sa’ad da muke fuskantar matsaloli.