Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Yi Amfani da ‘Yancinka a Hanyar da Ta Dace

Ka Yi Amfani da ‘Yancinka a Hanyar da Ta Dace

“Inda ruhun Ubangiji yake, nan akwai ‘yanci.”2 KOR. 3:17.

WAƘOƘI: 6265

1, 2. (a) Wane ra’ayi ne mutane suke da shi a kan batun ‘yancin yin zaɓi? (b) Mene ne Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da batun ‘yancin yin zaɓi, kuma waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

GA ABIN da wata mata ta gaya wa abokinta game da tsai da shawara: “Ka dai gaya min abin da ya kamata in yi, ba sai ka sa na yi tunani ba. Hakan zai fi mini sauƙi.” Matar ta gwammace a riƙa gaya mata abin da ya kamata ta yi, maimakon ta yi amfani da kyautar da Mahaliccinta ya ba ta, wato, ‘yancin yin zaɓi. Kai kuma fa? Shin kana jin daɗin yanke shawara da kanka ko kuma ka gwammace wasu su riƙa gaya maka abin da ya kamata ka yi? Yaya kake ɗaukan batun yin amfani da ‘yancin yin zaɓi?

2 Mutane sun daɗe suna ja-ni-in-ja-ka a kan wannan batun. Wasu sun ce Allah ya riga ya ƙaddara kome da za mu yi, saboda haka, ba mu da ‘yancin yin zaɓi. Wasu kuma sun ce kafin a ce muna da ‘yanci na gaskiya, wajibi ne mu sami ‘yancin yin duk abin da muka ga damar yi. Kafin mu san gaskiyar wannan batun, wajibi ne mu nemi shawarar Kalmar Allah, wato, Littafi Mai Tsarki. Me ya sa? Domin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah ya halicce mu a hanyar da za mu iya yin zaɓi kuma ya ba mu damar yin hakan. (Karanta Joshua 24:15.) Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya ba da amsa ga tambayoyi kamar su: A wace hanya ce ya kamata mu yi amfani da ‘yancinmu na yin zaɓi? Shin akwai wasu  abubuwan da ba mu da ‘yancin yi? A wace hanya ce yin amfani da ‘yancin yin zaɓi zai nuna ko muna ƙaunar Jehobah sosai? Ta yaya za mu nuna cewa muna girmama zaɓin da wasu suka yi?

MENE NE ZA MU IYA KOYA DAGA MISALIN JEHOBAH DA KUMA YESU?

3. Wane misali ne Jehobah ya kafa a yadda yake yin amfani da ‘yancinsa na yin zaɓi?

3 Jehobah ne kaɗai yake da ‘yancin yin kome kuma babu abin da zai hana shi yin hakan, amma ya kafa mana misalin yadda yake amfani da wannan ‘yancin. Alal misali, da son ransa ya zaɓi al’ummar Isra’ila ta zama “al’umma keɓaɓiya a gare shi.” (K. Sha. 7:6-8) Wannan zaɓin ba abin da ya rufe ido kawai ya canka ba ne. Amma ya zaɓe su ne domin ya yi wa amininsa Ibrahim alkawari tun da daɗewa. (Far. 22:15-18) Jehobah yana yin zaɓin da ya jitu da halinsa na ƙauna da kuma adalci a kowane lokaci. Horo da ya yi wa Isra’ilawa sa’ad da suka yi watsi da bauta ta gaskiya sau da sau ya nuna mana hakan. A duk lokacin da suka tuba, Jehobah yana nuna musu ƙauna da jin ƙai kuma ya ce: “Zan warkar da ɓaraicinsu, zan ƙaunace su [“da son raina,” NW ].” (Hos. 14:4) Hakika, wannan misali ne mai kyau na yin amfani da ‘yancin yin zaɓi a hanyar da ta dace!

4, 5. (a) Wane ne halitta na farko da Allah ya ba shi ‘yancin yin zaɓi, kuma yaya ya yi amfani da wannan ‘yancin? (b) Wace tambaya ce ya kamata kowannenmu ya yi?

4 A lokacin da Jehobah ya soma halittar abubuwa, ya zaɓa ya ba mala’iku da ‘yan Adam ‘yancin yin zaɓi. Halitta na farko da Jehobah ya zaɓa ya ba shi ‘yancin yin zaɓi shi ne Ɗan fari na Allah, wato, “surar Allah marar ganuwa.” (Kol. 1:15) Maimakon ya goyi bayan tawayen Shaiɗan, tun kafin Yesu ya zo duniya, ya zaɓi ya riƙe amincinsa ga Ubansa. Kuma sa’ad da yake duniya, Yesu ya yi amfani da ‘yancinsa na yin zaɓi wajen ƙin barin Shaiɗan ya shawo kansa. (Mat. 4:10) Yayin da Yesu yake yin addu’a a daren da aka kashe shi, ya nuna cewa ya riga ya ƙudura ya yi nufin Allah har ƙarshe. A cikin addu’ar ya ce wa Ubansa: “Ubana, in ka yarda, ka kawar mani da wannan ƙoƙo: amma dai ba nawa nufi ba, naka za a yi.” (Luk. 22:42) Ya kamata mu bi misalin Yesu mu yi amfani da ‘yancinmu na yin zaɓi don mu girmama Jehobah da kuma yin nufinsa. Amma hakan zai iya yiwuwa?

5 Hakika, zai yiwu mu bi misalin Yesu domin mu ma Allah ya halicce mu a cikin surarsa da kamanninsa. (Far. 1:26) Amma ba kome ba ne muke da ‘yancin yi kamar Jehobah. Kalmar Allah ta nuna cewa Jehobah ya hana mu yin wasu abubuwa. Alal misali, ya kamata matan aure su bi shugabancin mazajensu, yara kuma su yi biyayya ga iyayensu. (Afis. 5:22; 6:1) A wace hanya ce ya kamata hakan ya shafi yadda muke amfani da ‘yancinmu na yin zaɓi? Zaɓin da muka yi a wannan batun zai iya sa mu sami rai na har abada ko kuma mu hallaka.

YIN AMFANI DA ‘YANCIN YIN ZAƁI A HANYAR DA TA DACE DA WADDA BA TA DACE BA

6. Ka ba da misalin da ya nuna cewa ba kome muke da ‘yanci yi ba.

6 Shin za mu iya ce muna da ‘yanci na gaskiya idan ba za mu iya yin duk abin da muka ga damar yi ba? E. Me ya sa? Ana iya kāre mutum daga hatsari ta wurin hana shi yin wani abu. Alal misali, a ce muna da ‘yancin yin tafiya da mota a kan wani babban titi zuwa wani gari mai nisa. Amma kowa da ke tafiya a kan wannan babban titin yana da ‘yancin bin inda ya ga dama, kowa yana da ‘yancin yin gudu iyakar yadda ya ga dama, kuma babu dokokin hanya a kan wannan titin. Shin, hankalinka zai kwanta ne idan kana bin wannan hanyar? Da kyar. Kafin dukanmu mu ji daɗin ‘yanci  na ƙwarai, wajibi ne a hana mu yin wasu abubuwa. Bari mu tattauna wasu misalai a cikin Littafi Mai Tsarki da za su ƙara taimaka mana mu ga muhimmancin yin amfanin da ‘yancin yin zaɓi da Jehobah ya ba mu daidai gwargwado.

7. (a) Ta yaya ‘yancin yin zaɓi da Adamu yake da shi ya bambanta shi da sauran halittun da ke Adnin? (b) Ka bayyana ɗaya daga cikin hanyoyin da Adamu ya yi amfani da ‘yancinsa na yin zaɓi.

7 Kamar yadda ya yi wa mala’iku, a lokacin da Allah ya halicci Adamu, Ya ba shi ‘yancin yin zaɓi. Hakan ya sa Adamu ya bambanta da sauran halittun da ke cikin lambun. Bari mu tattauna wani misali na yadda Adamu ya yi amfani da ‘yancinsa a hanyar da ta dace. An halicci dabbobi kafin Adamu. Amma Jehobah ya ba wa Adamu damar ba waɗannan dabbobin sunaye. Allah “ya kawo su wurin mutumin ya ga” sunayen da mutumin zai kira kowannensu. Adamu ya lura da halayen dabbobin kuma ya ba su sunayen da suka dace da su, kuma Jehobah bai canja sunayen da Adamu ya ba su ba. Amma “iyakar abin da mutumin ya kira kowane rayayyen halitta, shi ne ya zama sunansa.”Far. 2:19.

8. A wace hanya ce Adamu ya yi amfani da ‘yancinsa a hanyar da ba ta dace ba, kuma mene ne sakamakon hakan?

8 Abin taƙaici shi ne, Adamu bai gamsu da aikin da Allah ya ba shi na yin noma da kuma kula da lambun ba. Bai gamsu da ‘yancin da Allah ya ba shi sa’ad da ya gaya masa cewa ya ‘yalwata da ‘ya’ya, ya riɓu, ya mamaye duniya, ya mallake ta; ya yi mulkin kifaye . . . , da tsuntsaye . . . , da kowane abu mai rai wanda ke rarrafe a ƙasa’ ba. (Far. 1:28) A maimakon haka, ya wuce iyakar ‘yancin da Allah ya ba shi ta wajen cin ‘ya’yan itacen da Allah ya hana shi. Wannan mummunar mataki da Adamu ya ɗauka ya jawo wa zuriyarsa matsaloli har zuwa yau. (Rom. 5:12) Idan muna tunawa da sakamakon matakin da Adamu ya ɗauka, hakan zai taimaka mana mu yi amfani da ‘yancinmu a hanyar da ta dace.

9. Wane ‘yanci ne Jehobah ya ba mutanensa, Isra’ilawa, kuma me suka yi?

9 Duka ‘ya’yan Adamu sun gāji zunubi da mutuwa daga wurinsa. Amma Allah ya ba su ‘yancin yin zaɓi. Za mu iya ganin hakan ta yadda Allah ya bi da al’ummar Isra’ila. Ta wurin bawansa Musa, Jehobah ya ba al’ummar Isra’ila ‘yanci su zaɓa ko za su zama keɓaɓɓiyar taska a gare shi ko kuma a’a. (Fit. 19:3-6) Mene ne suka yi? Da son ransu, suka yarda su zama mutanen Allah kuma dukansu suka ce: ‘Abin da Ubangiji ya faɗi duka za mu yi.’ (Fit. 19:8) Amma abin taƙaici shi ne, daga baya al’ummar ta yi amfani da ‘yancinta don yin zaɓin da bai dace ba kuma ba ta cika wannan alkawarin da ta yi. Bai kamata mu bi wannan misalin ba amma zai dace mu riƙa kasancewa da aminci ga Jehobah kuma mu bi ƙa’idodinsa ta wajen yin zaɓi mai kyau.1 Kor. 10:11.

10. Waɗanne misalai ne suka nuna cewa zai yiwu ‘yan Adam su yi amfani da ‘yancinsu na yin zaɓi a hanyar da za ta ɗaukaka Allah? (Ka duba hoton da ke shafi na 12.)

10 A littafin Ibraniyawa sura 11, an rubuta sunayen bayin Allah guda 16 da suka yi amfani da ‘yancin da Jehobah ya ba su yadda ya kamata. A sakamakon haka, sun sami albarka mai yawa da kuma begen yin rayuwa a nan gaba. Alal misali, Nuhu ya nuna cewa shi mai bangaskiya ne ta wajen bin umurnin da Allah ya ba shi na yin jirgi don ya ceci iyalinsa kuma don ya sa ‘yan Adam su ci gaba da rayuwa. (Ibran. 11:7) Ibrahim da Saratu sun yarda su yi biyayya da umurnin da Allah ya ba su su je ƙasar alkawari. A lokacin da suka soma wannan tafiya mai nisa, da sun ga dama ‘da sun koma’ birnin Ur, inda ake samun ci gaba sosai. Amma saboda bangaskiyarsu, sun mai da hankali ga  ‘amsar alkawarai’ da Allah ya yi musu; domin “wata ƙasa mafiya kyau suke biɗa.” (Ibran. 11:8, 13, 15, 16) Musa ya yi watsi da dukiyar ƙasar Masar, domin ya ‘gwammace a wulaƙanta shi tare da mutanen Allah, da ya ji daɗin nishatsin zunubi domin ‘yan kwanaki.’ (Ibran. 11:24-26) Ya kamata mu bi misalin waɗannan amintattun bayin Allah ta wajen yin amfani da ‘yancinmu na yin zaɓi a hanya mai kyau da kuma yin nufin Allah.

11. (a) Wace albarka ce mutum zai samu daga yin amfani da ‘yancinsa na yin zaɓi? (b) Mene ne yake motsa ka ka yi amfani da ‘yancinka na yin zaɓi a hanyar da ta dace?

11 Ko da yake zai fi mana sauƙi wani ya riƙa gaya mana abin da ya kamata mu yi, hakan ba zai ba mu damar moran albarka da ke tattare da yin amfani da ‘yancinmu ba. An ambaci wannan albarkar a Kubawar Shari’a 30:19, 20. (Karanta.) Aya ta 19 ta faɗi zaɓin da Allah ya ba Isra’ilawa. A aya ta 20 kuma mun ga cewa Jehobah ya ba su damar nuna masa ainihin abin da ke zuciyarsu. Mu ma muna da damar zaɓan ko za mu bauta wa Jehobah ko a’a. Ya kamata mu yi amfani da ‘yancinmu don mu bauta wa Jehobah da kuma nuna masa cewa muna ƙaunarsa sosai!

KADA KA YI AMFANI DA ‘YANCINKA A HANYAR DA BA TA DACE BA

12. Mene ne bai kamata mu yi da ‘yancin da Allah ya ba mu ba?

12 A ce ka ba abokinka wata kyauta mai tamani sai daga baya ka gano cewa ya yi banza da kyautar ko kuma yana amfani da kyautar ya ji wa mutane rauni. Yaya za ka ji? Ka yi tunanin yadda Jehobah yake ji yayin da yake ganin yadda mutane da yawa suke amfani da ‘yancinsu na yin zaɓi a hanyar da ba ta dace ba, har ma da ji ma wasu rauni. Abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa ke nan cewa a “kwanaki na ƙarshe” mutane za su zama “marasa godiya.” (2 Tim. 3:1, 2) Kada mu yi banza da wannan kyautar da Jehobah ya ba mu ko kuma mu yi amfani da ita a hanyar da ba ta dace ba. Amma ta yaya za mu guji yin amfani da ‘yancinmu na yin zaɓi a hanyar da ba ta dace ba?

13. Ta yaya za mu iya guje wa yin amfani da ‘yancinmu a hanyar da ba ta dace ba?

13 Kowannenmu yana da ‘yanci ya zaɓi abokansa da irin adon da zai yi da irin tufafin da zai riƙa sakawa da kuma irin nishaɗin da yake so. Amma idan muna bin adon mutanen duniyar nan, wannan ‘yancin zai iya zama “mayafin ƙeta,” wato, za mu nemi hujjar yin abubuwan da ba su dace ba  domin muna ganin cewa muna da ‘yanci. (Karanta 1 Bitrus 2:16.) A maimakon mu ɗauki ‘ ’yancinmu’ a matsayin ‘hujjar biye wa halin’ duniyar nan, ya kamata mu riƙa yin zaɓin da za su taimaka mana mu “yi kome saboda ɗaukakar Allah.”Gal. 5:13, Littafi Mai Tsarki; 1 Kor. 10:31.

14. Wace alaƙa ke tsakanin dogara ga Jehobah da yin amfani da ‘yancinmu na yin zaɓi?

14 Wata hanya kuma da za mu iya amfani da ‘yancinmu na yin zaɓi a hanya mai kyau ita ce ta wurin dogara ga Jehobah da kuma bin dokokinsa. Shi ne Wanda ‘yake koya mana zuwa amfaninmu, wanda yake bishe mu ta hanyar da za mu bi.’ (Isha. 48:17) Wajibi ne mu yarda cewa, “hanyar mutum ba cikin nasa hannu take ba; mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.” (Irm. 10:23) Kada mu dogara ga kanmu kamar yadda Adamu da kuma Isra’ilawa masu tawaye suka yi. A maimakon haka, ya kamata mu ‘dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarmu.’Mis. 3:5.

KADA KU ƘETA ‘YANCIN WASU

15. Mene ne muka koya daga ƙa’idar da ke Galatiyawa 6:5?

15 Ba mu da ‘yanci mu hana wasu yin amfani da ‘yancinsu wajen yanke shawara. Me ya sa? Domin dukanmu muna da ‘yancin yin zaɓi kuma babu yadda za a yi dukan Kiristoci su yanke shawara iri ɗaya a kowane lokaci, ko da a batun da ya shafe halinmu ne ko kuma ibadarmu. Ka tuna da ƙa’idar da ke Galatiyawa 6:5. (Karanta.) Idan muka amince cewa kowane Kirista “za ya ɗauki kayan kansa,” hakan zai taimaka mana mu bar kowa ya riƙa yin amfani da ‘yancinsa na yin zaɓi.

Za mu iya zaɓan abin da muke so ba tare da tilasta ma wasu su bi namu zaɓin ba (Ka duba sakin layi na 15)

16, 17. (a) Ta yaya yin amfani da ‘yancin yin zaɓi ya zama matsala a ikilisiyar Koranti? (b) Ta yaya Bulus ya taimaka musu su sasanta batun, kuma me hakan ya koya mana game da ‘yancin da ‘yan’uwanmu suke da shi?

16 Ka yi la’akari da wani misali a cikin Littafi Mai Tsarki da ya nuna cewa wajibi ne mu bar kowa ya yi amfani da ‘yancinsa na yin zaɓi idan ya zo ga yanke shawara a kan batun da Littafi Mai Tsarki bai da ba doka a kai ba. Kiristoci a ikilisiyar da ke Koranti sun sami saɓani a kan batun sayan nama a kasuwa da wataƙila an yi hadaya da shi ga gumaka. Wasu sun ce: ‘Gunki ba wani abu ba ne, saboda haka zuciyarsu ba ta damunsu idan suka ci naman.’ Amma wasu da suke bauta wa gumaka a dā suna ganin cin irin wannan naman ɗaya yake da bauta wa gunki. (1 Kor. 8:4, 7) Wannan batun ya so ya kawo jayyaya a cikin ikilisiyar. Ta yaya Bulus ya taimaka wa Kiristocin da ke Koranti su kasance da ra’ayin Allah a kan wannan batun?

17 Da farko, Bulus ya tuna musu cewa abinci ba zai sa su kusaci Allah ba. (1 Kor. 8:8) Sai ya ce musu su ‘yi hankali kada wannan iko nasu ya zama abin tuntuɓe ga raunana.’ (1 Kor. 8:9) Daga baya, ya gaya wa waɗanda zuciyarsu tana saurin damunsu kada su hukunta waɗanda suka zaɓa su ci irin naman nan. (1 Kor. 10:25, 29, 30) Bulus ya nuna cewa kowane Kirista yana da ‘yancin yin zaɓi, har ma a wannan batu mai muhimmanci da ya shafi ibadarsa ga Jehobah. Saboda haka, idan ya zo ga batun da bai taka kara ya karya ba, ya kamata mu bar ‘yan’uwanmu su yi amfani da ‘yancinsu na yin zaɓi, ko ba haka ba?1 Kor. 10:32, 33.

18. Ta yaya za ka nuna cewa kana amfani da ‘yancinka na yin zaɓi a hanyar da ta dace?

18 Jehobah ya ba mu ‘yanci da gaske ta wajen barin mu mu zaɓi abin da muke so. (2 Kor. 3:17) Muna godiya saboda wannan kyautar domin yana ba mu damar nuna wa Jehobah cewa muna ƙaunarsa sosai. Bari mu ci gaba da nuna godiyarmu don wannan kyautar ta wurin yin amfani da ita a hanyar da za ta ɗaukaka Allah da kuma ta wajen barin wasu su yi amfani da nasu ‘yancin yin zaɓin.