Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Sun Ba da Kansu da Yardar Rai

Sun Ba da Kansu da Yardar Rai

AKWAI ‘yan’uwa mata da yawa da ba su yi aure ba masu ƙwazo sosai da suke wa’azi a ƙasashen da ake bukatar masu shelar bishara sosai. Wasu sun riga sun yi shekaru da yawa suna hidima a waɗannan ƙasashen. Me ya taimaka musu su soma hidima a waɗannan ƙasashen? Me suka koya daga irin wannan hidimar? Waɗanne albarka suka samu daga yin wannan hidimar? Mun yi hira da wasu daga cikin waɗannan ƙwararrun ‘yan’uwa mata. Idan kina sha’awar yin hidimar da za ta sa ki yi rayuwa mai ma’ana, mun tabbata cewa za ki amfana daga abubuwan da suka faɗa. Amma bayin Allah gabaki ɗaya za su iya amfana idan suka yi tunani a kan misalinsu.

YADDA ZA KU KASANCE DA GABA GAƊI

Anita

Shin kuna shakkar ko za ku iya yin hidimar majagaba a wata ƙasa? Anita, wata ‘yar’uwa da take da shekaru 75 yanzu ta ɗauka cewa ba za ta iya yin hakan ba. Ta yi girma ne a ƙasar Turai kuma ta soma yin hidimar majagaba tun tana shekara 18. Ta ce: “Ina jin daɗin koya wa mutane game da Jehobah, amma ban taɓa tsammani cewa zan iya zuwa wata ƙasa don yin wa’azi ba. Ban taɓa koyan sabon yare ba kuma na ga cewa ba zan iya yin hakan ba. Saboda haka, na yi mamaki sosai sa’ad da aka gayyace ni in halarci Makarantar Littafi Mai Tsarki na Gilead. Na yi mamakin hakan domin ina ganin ban iya kome ba. Amma na yi tunani cewa ‘Idan Jehobah ya ce zan iya yi, to, zan ƙoƙarta in yi.’ Yanzu shekaru 50 sun shige, kuma tun daga lokacin ina yin hidima a ƙasar Jafan.” Anita tana jin daɗin ƙarfafa ‘yan’uwa mata matasa su ƙoƙarta su bi misalinta na yin hidima a ƙasar waje. Kuma da yawa a cikinsu suna yin hakan.

YADDA ZA KI ƊAUKI MATAKI

Da farko, ‘yan’uwa mata da yawa da suka yi hidima a ƙasar waje sun yi jinkirin ɗaukan wannan matakin. Amma me ya taimaka musu su yi hakan?

Maureen

Maureen, wadda take da shekaru 64 yanzu ta ce: “A lokacin da nake girma, na yi sha’awar yin rayuwa mai ma’ana, wato, rayuwar da za ta ba ni zarafin taimaka wa mutane.” A lokacin da ta kai shekara 20 sai ta ƙaura zuwa lardin Quebec, a ƙasar Kanada, inda ake bukatar masu shelar bishara da yawa. Ta ce: “Daga baya aka gayyace ni in halarci Makarantar Littafi Mai Tsarki na Gilead, amma na ji tsoron zuwa wurin, da yake ban taɓa zuwa ba. Ƙari ga haka, na ji tsoron barin mahaifiyata ita kaɗai ta yi jinyar mahaifina. Na yi ta addu’a ga Jehobah da kuka don ya nuna min abin da ya kamata in yi. Da na gaya wa iyayena abin da yake damuna, sai suka ce min in je. ‘Yan’uwa a cikin ikilisiya  sun taimaka wa iyayena, kuma ganin yadda Jehobah yake kula da iyalinmu ya sa na kasance da tabbaci cewa zai kula da ni idan na je wata ƙasa. Abin da ya taimaka mini in ɗauki mataki ke nan!” Maureen ta soma hidima a Yammacin Afirka a shekara ta 1979 kuma ta yi hakan na tsawon shekaru 30. Bayan haka, Maureen ta koma ƙasar Kanada tana jinyar mahaifiyarta, amma har ila tana hidimar majagaba na musamman. Bayan ta yi tunanin hidimar da ta yi a ƙasar waje, ta ce: “Jehobah ya tanadar mini da abin da nake bukata kuma ya yi hakan a daidai lokacin da nake bukatar su.”

Wendy

Wendy, wata ‘yar’uwa mai shekaru 65 ta soma hidimar majagaba a Ostareliya sa’ad da take shekara goma sha huɗu. Ta ce: “Ni mai jin kunya ce sosai a lokacin kuma ina jin tsoron magana da baƙi. Amma yin hidimar majagaba ya taimaka mini in yi magana da mutane daga wurare dabam-dabam, kuma hakan ya taimaka mini na kasance da gaba gaɗi. Da sannu a hankali, sai na daina jin tsoro. Yin hidimar majagaba ya koya mini yadda zan dogara ga Jehobah kuma na soma tunanin tafiyar ƙasar waje don yin wa’azi. Ƙari ga haka, wata ‘yar’uwa marar aure da ta yi hidima a Jafan har tsawon shekaru 30 ta gayyace ni in zo in yi wa’azi tare da ita a Jafan na tsawon watanni uku. Yin wa’azi tare da ita ya sa na ƙara sha’awar yin wa’azi a ƙasar waje.” A shekara ta 1986, Wendy ta ƙaura zuwa Vanuatu, wani tsibirin da ke da nisan kilomita 1,770 daga gabashin Ostareliya, don yin wa’azi.

Har ila Wendy tana hidima a Vanuatu amma yanzu tana wani ofishinmu na fassara. Ta ce: “Ina farin ciki sosai idan na ga yadda ake kafa sababbin ikilisiyoyi da kuma rukunonin Shaidun Jehobah. Taimakawa da aikin Jehobah a waɗannan tsibiran yana sa ni murna sosai.”

Kumiko (a tsakiya)

Kumiko, wata ‘yar’uwa mai shekaru 65 tana hidimar majagaba a ƙasar Jafan sa’ad da wadda suke wa’azi tare ta ce su je su yi hidima a ƙasar Nepal. Kumiko ta ce: “Ta gaya mini cewa mu ƙaura sau da sau amma na ƙi domin ina ganin ba zan iya koyan sabon yare ba kuma zai yi min wuya in saba da yanayin wurin. Wata matsalar kuma ita ce, ba ni da isashen kuɗi. Kafin in yanke shawara a kan wannan batun, sai na yi hatsari da babur kuma aka kwantar da ni a asibiti. Sa’ad da nake asibiti sai na soma tunani, ‘Wa ya san abin da zai faru da ni bayan wannan? Zan iya kamuwa da wata muguwar cuta kuma in kasa zuwa wa’azi a ƙasar waje. Ba gwamma na je na gwada yin wa’azi na tsawon shekara guda a wurin ba?’ Na yi addu’a ga Jehobah ya taimaka min in ɗauki wannan matakin.” Bayan Kumiko ta bar asibiti, sai ta ziyarci ƙasar Nepal kuma daga baya ita da abokiyarta suka ƙaura zuwa wurin.

 Bayan da Kumiko ta yi tunani a kan hidimar da ta yi kusan shekaru goma a ƙasar Nepal, ta ce: “Abubuwa da nake jin tsoronsu ba su faru ba. Ina farin ciki cewa na je hidima a inda ake bukatar masu shelar bishara sosai. Sau da yawa idan ina yin wa’azi a wani iyali, sai maƙwabtan wajen mutane biyar ko shida, su zo don su saurara. Har ƙananan yara ma suna roƙona in ba su wata warƙa. Ina farin cikin yin wa’azi a wannan wurin da mutane suke son jin bishara.”

YADDA SUKA MAGANCE MATSALOLINSU

’Yan’uwa mata da muka gana da su sun fuskanci matsaloli dabam-dabam. Ta yaya suka magance waɗannan matsalolin?

Diane

Diane, wata ‘yar’uwa da ta fito daga Kanada ta ce: “Da farko, ya mini wuya in yi nesa da ‘yan gidanmu.” Yanzu shekarunta 62 ne kuma ta yi shekaru 20 tana wa’azi a ƙasar Kwaddebuwa. Ta ce: “Na roƙi Jehobah ya taimake ni don in ƙaunaci mutanen da nake musu wa’azi. Wani ɗan’uwa mai suna Jack Redford, da ya koyar da mu a makarantar Gilead ya gaya mana cewa da farko, za mu iya mamakin irin abubuwan da ke faruwa a yankinmu, musamman idan muka ga yadda mutane suke fama da matsanancin talauci. Amma kuma ya ce: ‘Kada ku damu da talaucin. Ku mai da hankalinku ga mutanen da kansu kuma ku lura da yadda suke ji bayan sun fahimci gaskiyar Littafi Mai Tsarki.’ Abin da na yi ke nan kuma hakan ya taimaka min sosai! Idan ina yi wa mutane wa’azi game da Mulkin, sai in ga yadda suke farin ciki sosai don na ƙarfafa su.” Ban da wannan, me ya taimaka wa Diane ta saba da yin wa’azi a ƙasar waje? Ta ce: “Na zama abokan waɗanda nake nazarin Littafi Mai Tsarki da su kuma ganin yadda suka zama bayin Jehobah ya sa ni farin ciki sosai. Inda nake hidima ya zama kamar ƙasata. A wurin na sami iyaye da ‘yan’uwa a cikin ƙungiyar Jehobah, kamar yadda Yesu ya faɗa.”—Mar. 10:29, 30.

Anne wata ‘yar’uwa mai shekaru 46 tana hidima a wata ƙasa a Asiya, inda aka saka takunkumi a aikin Shaidun Jehobah. Ta ce: “Shekaru da yawa da na yi hidima a wurare dabam-dabam a ƙasar waje, na yi zama da ‘yan’uwa mata da suka fito daga wurare dabam-dabam kuma halayensu sun bambanta da nawa. A wasu lokuta, hakan na kawo saɓani tsakaninmu. Idan hakan ya faru, nakan ƙoƙarta in kusace su domin in ƙara fahimtar al’adarsu. Ƙari ga haka, na koyi yadda zan daɗa nuna musu ƙauna da sanin yakamata. Ina farin ciki cewa wannan ƙoƙarin ya cim ma sakamako mai kyau kuma yanzu sun zama abokaina na kud-da-kud. Sun taimaka mini sosai in ci gaba da yin hidimata.”

Ute

 A shekara ta 1993, an tura Ute, wata ‘yar’uwa daga Jamus zuwa ƙasar Madagascar don ta yi hidima. Yanzu tana da shekaru 53 kuma ta ce: “Da farko, na yi fama sosai da koyan yare da yanayin wurin da zazzaɓin cizon sauro da kuma tsutsotsi masu sa mutane rashin lafiya. Amma ‘yan’uwa mata da ke wurin da yaransu, har ma da ɗalibaina sun taimaka min in koyi yarensu. ‘Yar’uwa da muke wa’azi tare a ƙasar ta taimaka min a duk lokacin da nake rashin lafiya. Amma mafi muhimmanci, Jehobah ya taimaka min sosai. Ina masa addu’a kuma in gaya masa duk abin da ke damuna. Sai in jira Jehobah ya amsa addu’ata. Wani lokaci, yakan ɗauki kwanaki ko kuma watanni kafin Jehobah ya amsa addu’ar, amma yana magance mini dukan matsalolina.” Ute ta yi shekara 23 yanzu tana hidima a ƙasar Madagascar.

AN ALBARKACE SU SOSAI

’Yan’uwa mata da ba su yi aure da suka je hidima a wasu ƙasashe sun sami albarka sosai kamar yadda wasu ma suka shaida hakan. Waɗanne albarka suka samu?

Heidi

Heidi wata ‘yar Jamus da take da shekaru 73 ta soma hidima a ƙasar Kwaddebuwa tun shekara ta 1968. Ta ce: “Ina farin cikin ganin waɗanda na yi nazari da su suna bauta wa Jehobah. Wasu daga cikinsu sun zama majagaba, wasu kuma dattawa ne a cikin ikilisiya. Da yawa a cikinsu suna kira na Mama ko Kaka. Ɗaya daga cikin dattawan da iyalinsa suna ganina kamar wadda take cikin iyalinsu. Saboda haka, zan iya cewa Jehobah ya ba ni ɗa da suruka da kuma jikoki uku.”3 Yoh. 4.

Karen (a tsakiya)

Karen, wata ‘yar’uwa daga ƙasar Kanada wadda take da shekaru 72 ta yi hidima a Yammacin Afirka har tsawon shekaru 20. Ta ce: “Yin wa’azi a ƙasar waje ya taimaka min in zama mai haƙuri da sadaukar da kai kuma na riƙa ƙaunar mutane. Yin hidima tare da ‘yan’uwa da suka fito daga ƙasashe dabam-dabam ya sa na ƙara fahimtar yadda mutane daga wurare dabam-dabam suke tunani. Na koyi cewa akwai hanyoyi dabam-dabam da za a iya yin wasu abubuwa. Yanzu ina da abokai daga ƙasashe da yawa! Ko da yake abubuwa da muke yi yanzu sun bambanta kuma muna hidima dabam-dabam, abokantakarmu tana nan daram.”

Margaret, wata ‘yar’uwa daga ƙasar Ingila wadda take da shekaru 79 ta yi hidima a jamhuriyar Laos. Ta ce: “Yin hidima a ƙasar waje ya taimaka mini in ga yadda Jehobah yake jawo kowane irin mutum daga kowace ƙasa zuwa ƙungiyarsa. Hakan ya ƙarfafa bangaskiyata. Yanzu ina da tabbaci cewa Jehobah ne yake ja-gorar ƙungiyarsa kuma zai cika duk wani alkawarin da ya yi.”

Hakika, ‘yan’uwa mata marasa aure da yawa da suke hidima a ƙasashen waje suna aiki na musamman a yaɗa bishara kuma sun cancanci mu yaba musu. (Alƙa. 11:40) Ƙari ga haka, adadinsu yana ƙaruwa sosai. (Zab. 68:11) Shin za ku iya daidaita ayyukan da kuke yi don ku bi sawun waɗannan ‘yan’uwa mata masu ƙwazo da aka ambata a cikin wannan talifin? Idan kuka yi hakan, za ku ga cewa “Ubangiji nagari ne.”Zab. 34:8.