Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Ka Danka ma Mutane Masu-Aminci”

“Ka Danka ma Mutane Masu-Aminci”

“Ka danƙa ma mutane masu-aminci, waɗanda za su iya su koya ma waɗansu kuma.”2 TIM. 2:2.

WAƘOKI: 123, 53

1, 2. Yaya mutane da yawa suke ɗaukan aikin da suke yi?

MUTANE da yawa suna ɗaukan kansu da daraja ko kuma marasa daraja, bisa ga aikin da suke yi. Wasu kuma suna ganin cewa aiki ko kuma matsayi shi yake nuna ko mutum yana da muhimmanci ko a’a. A wasu al’adu idan mutum yana so ya san wani, ɗaya ciki tambayoyi na farko da zai yi shi ne, “Wane irin aiki kake yi?”

2 A wasu lokuta Littafi Mai Tsarki yakan kwatanta mutane da aikin da suke yi. Alal misali, ya kira “Matta mai-karɓan haraji,” ya kira “Siman majemi” kuma ya kira “Luka, ƙaunataccen likitan nan.” (Mat. 10:3; A. M. 10:6; Kol. 4:14) Ƙari ga haka, za a iya kwatanta mu da irin hidimar da muke yi. Littafi Mai Tsarki ya kira Dauda Sarki, ya kira Iliya annabi kuma ya kira Bulus manzo. Waɗannan mutanen sun ɗauki hidimar da Allah ya ba su da muhimmanci sosai. Babu shakka, mu ma za mu iya ɗaukan hidimarmu da muhimmanci.

3. Me ya sa tsofaffi suke bukatar su koyar da matasa? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

3 Babu shakka, dukanmu muna son aikin da muke yi, kuma  idan muka sami dama, za mu so mu ci gaba da yin aikin har abada. Amma abin takaici shi ne, tun daga zamanin Adamu muna tsufa kuma hakan ya sa mu ba ma iya yin abin da muke yi dā. (M. Wa. 1:4) Irin wannan yanayin yana sa bayin Jehobah baƙin ciki sosai. A yau, aikin da mutanen Jehobah suke yi yana daɗa ƙaruwa, don haka, mun soma amfani da na’urorin zamani don yin wa’azi. Wasu tsofaffi a cikinmu ba za su iya yin amfani da irin waɗannan abubuwan ba. (Luk. 5:39) Ban da haka ma, idan mun soma tsufa ƙarfinmu yana raguwa amma matasa sun fi tsofaffi kuzari. (Mis. 20:29) Amma ya dace tsofaffi su mai da hankali ga horar da matasa don su ma su sami ci gaba a hidimarsu ga Jehobah.Karanta Zabura 71:18.

4. Me ya sa yake yi wa wasu wuya su bar wasu su ɗauki matsayinsu? (Ka duba akwatin nan “ Dalilin da Ya Sa Wasu Ba Sa Danƙa ma Mutane Aiki.”)

4 Ba ya wa mutane sauƙi su ɗanka wa matasa matsayi. Wasu suna jin tsoron barin wasu su ɗauki matsayinsu. Wasu kuma suna jin cewa idan ba su ja-goranci aikin da kansu ba, matasa ba za su iya yin aikin kamar yadda za su yi ba. Ƙari ga haka, wasu suna iya yin tunanin cewa ba su da lokacin koyar da wasu. Ban da haka ma, matasa ma suna bukata su kasance da haƙuri idan ba a ba su matsayi ba.

5. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin?

5 Bari mu tattauna tambayoyi uku da suka yi magana game da ba ma wasu aiki. Na farko, ta yaya tsofaffi za su taimaka wa matasa su san yadda za su riƙa yin wasu ayyuka, kuma me ya sa yin hakan yake da muhimmanci? (2 Tim. 2:2) Na biyu, me ya sa yake da muhimmanci matasa su kasance da halin da ya dace sa’ad da ‘yan’uwa da suka ƙware suke koyar da su? Bari mu ga yadda Sarki Dauda ya tallafa wa ɗansa don aiki mai muhimmanci da zai yi.

DAUDA YA HORAR DA SULEMANU KUMA YA TALLAFA MASA

6. Mene ne Sarki Dauda ya so ya yi, kuma me Jehobah ya gaya masa?

6 Bayan ya yi shekaru yana gudun hijira, Dauda ya zama sarki kuma ya soma rayuwa mai kyau. Ya yi baƙin ciki cewa  Jehobah bai da “gida” ko kuma haikalin da mutane za su riƙa zuwa don su masa bauta, don haka, ya so ya gina masa. Ya gaya wa annabi Nathan cewa: “Ga shi, ni ina zaune cikin gida na [katakan] cedar, amma sanduƙin alkawarin Ubangiji yana ƙarƙashin zannuwa.” Nathan ya ce masa: Ka “yi dukan abin da ke cikin zuciyarka; gama Allah yana tare da kai.” Amma Jehobah ya ba da wani umurni dabam. Ya gaya wa Nathan ya faɗa wa Dauda cewa: “Ba za ka gina mini gida in zauna a ciki ba.” Duk da haka, Jehobah ya yi wa Dauda alkawarin cewa zai ci gaba da yi masa albarka kuma ya ƙara gaya masa cewa ɗansa Sulemanu ne zai gina haikalin. Yaya Dauda ya ji game da hakan?1 Laba. 17:1-4, 8, 11, 12; 29:1.

7. Yaya Dauda ya ji sa’ad da aka gaya masa cewa ba shi ne zai gina haikalin Jehobah ba?

7 Babu shakka, Dauda ya so ya gina wa Jehobah haikali, wataƙila ya yi baƙin ciki sa’ad da aka gaya masa cewa ba shi ne zai yi hakan ba. Duk da haka, ya tallafa wa ɗansa Sulemanu. Dauda ya taimaka wajen shirya ma’aikata da za su riƙa tattara jan ƙarfe da azurfa da zinariya da kuma itace. Kuma ya ƙarfafa Sulemanu ya ce: “Yanzu fa, ɗana, Ubangiji shi zauna tare da kai; ka yi albarka, ka gina gidan Ubangiji Allahnka, kamar yadda ya ambata a kanka.”1 Laba. 22:11, 14-16.

8. Me ya sa wataƙila Dauda ya ga cewa Sulemanu ba zai iya yin aikin ba, kuma mene ne ya yi?

8 Karanta 1 Labarbaru 22:5. Wataƙila Dauda ya ga cewa wannan aikin ya fi ƙarfin Sulemanu. Me ya sa? Saboda haikalin “mai-daraja ƙwarai da gaske” ne, kuma a lokacin Sulemanu “ƙarami ne, yana kuwa da ƙuruciya.” Amma Dauda ya san cewa Jehobah zai taimaka wa Sulemanu ya idar da aikin da ya ba shi. Don haka, Dauda ya mai da hankali ga abin da zai iya yi don ya taimaka, sai ya soma tattara kayan da za a yi aikin da su.

KA YI FARIN CIKI SA’AD DA KAKE HORAR DA WASU

Muna farin cikin ganin yadda matasa suke hidimar Jehobah da ƙwazo (Ka duba sakin layi na 9)

9. Ta yaya tsofaffi za su ji daɗin ba wa matasa ayyukan da suke yi? Ka ba da misali.

9 Kada ‘yan’uwa tsofaffi su yi baƙin ciki idan ya zama musu dole su danƙa wa matasa matsayinsu. Dukanmu mun fahimci cewa aikin da ya fi muhimmanci shi ne hidimar Jehobah. Dattawa suna bukatar su yi farin ciki sa’ad da suka ga matasa da suka horar suna shirye su yi aiki. Ga wani misali, a ce wani mahaifi ya soma koya wa yaronsa yadda zai tuƙa mota, a lokacin da yaron yake ɗan ƙarami ya mai da hankali ga yadda mahaifinsa yake tuƙa motar. Da ya girma, sai mahaifin ya bayyana masa abin da yake yi, da yaron ya kai lokacin da zai soma yin tuƙi, sai ya soma tuƙa motar kuma mahaifinsa yana faɗa masa abin da zai yi. A wasu lokuta idan ɗan ya tuƙa motar kaɗan zai ba wa mahaifin ma ya tuƙa amma da yake mahaifin ya tsufa ɗan ne zai yi riƙa  yin tuƙin. Babu shakka, mahaifin zai ji daɗin barin ɗansa ya yi wannan aikin. Hakazalika, dattawa ma suna farin cikin ganin yadda matasa da suka horar suke ƙwazo a hidimar Jehobah.

10. Ta yaya Musa ya ɗauki matsayinsa da kuma ikon da yake da shi?

10 Idan mu tsofaffi ne, muna bukatar mu mai da hankali don kada mu soma ƙishi. Ku yi la’akari da abin da Musa ya yi sa’ad da wasu daga cikin Isra’ilawa suka soma yin abu kamar annabawa. (Karanta Littafin Lissafi 11:24-29.) Joshua mataimakin Musa ya so ya hana su. A ganinsa, suna so su kwace wa Musa matsayinsa ne. Amma Musa ya ce masa: ‘Kana jin kishi domina? Da ma dukan jama’ar Ubangiji annabawa ne, Ubangiji kuwa ya sa ruhunsa a bisansu!’ Musa ya san cewa Jehobah yana sane da abin da yake faruwa. Maimakon ya kāre matsayinsa, Musa ya so dukan mutane su sami irin dangantakar da yake da shi da Jehobah. Kamar Musa mu ma muna farin ciki idan wasu suka samu ƙarin aiki a hidimar Jehobah, ko ba haka ba?

11. Mene ne wani ɗan’ uwa ya ce game da danƙa ma wani aikinsa?

11 A yau, muna da misalan ‘yan’uwa da yawa da suka yi shekaru suna yi hidima kuma suka horar da matasa da yawa don su ma su yi hidimarsu da ƙwazo. Alal misali, wani ɗan’uwa mai suna Peter ya yi shekaru 74 yana hidima ta cikkaken lokaci, amma ya yi amfani da shekaru 35 daga cikinsu don hidima a ofishin Shaidun Jehobah da ke Turai. Ya yi shekaru da yawa yana hidima a matsayin mai kula da Sashen Hidima. Amma yanzu Paul wani matashi da ya yi aiki shekaru da yawa tare da Peter ne yake kula da Sashen Hidimar. Da aka tambayi Peter yadda ya ji game da hakan, ya ce “Ina farin cikin sanin cewa akwai ‘yan’uwa da aka horar kuma suna a shirye su karɓi dukan aikin da aka ba su kuma suna ɗaukan wannan aikin da muhimmanci sosai.”

KU RIƘA DARAJA TSOFAFFI

12. Wane darasi ne za mu koya daga misalin Rehoboam?

12 Bayan da Sulemanu ya mutu, ɗansa Rehoboam ne ya zama sarki. A lokacin da Rehoboam ya soma sarauta ya nemi shawara daga dattawa a kan yadda zai yi aikinsa. Amma bai bi shawararsu ba. A maimakon haka, ya bi shawarar matasan da suka girma tare da shi waɗanda suke yi masa hidima a fada. Hakan ya sa bai yi nasara ba. (2 Laba. 10:6-11, 19) Wane darasi ne muka koya? Idan muka karɓi shawarar tsofaffi da suka ƙware za mu kasance da hikima. Bai kamata matasa su ga kamar ana takura musu ne don ana gaya musu su riƙa yin abu yadda aka saba yi dā. Suna bukatar su karɓi shawarar tsofaffi kuma kada su yi tunanin cewa shawarar ba za ta amfane su ba.

13. Ta yaya matasa za su yi aiki tare da tsofaffi da haɗin kai?

13 A wasu lokuta za a iya danƙa wa matasa aikin da tsofaffi suka yi a dā. Don haka, matasan suna bukatar su riƙa neman shawara daga tsofaffin da suka taɓa yin aiki a wurin idan suna so su yi nasara. Paul wanda muka ambata ɗazu, da aka danƙa masa aikin da Peter yake yi a dā, ya ce, “Nakan nemi shawara daga wurin Peter kuma ina gaya ma wasu da muke aiki tare su riƙa yin hakan.”

14. Mene ne za mu iya koya daga haɗin kan Bulus da Timotawus?

14 Matashin nan Timotawus ya yi aiki tare da manzo Bulus na shekaru da yawa. (Karanta Filibiyawa 2:20-22.) Bulus ya rubutu wa Korintiyawa cewa: Zan “aike  muku Timotawus, wanda yake ɗana cikin Ubangiji, ƙaunatace, mai-aminci kuwa, domin shi tuna muku da al’amurana da ke cikin Kristi, kamar yadda nake koyarwa koina a cikin kowace ikilisiya.” (1 Kor. 4:17) Wannan furucin ya nuna cewa Bulus da Timotawus suna da haɗin kai. Bulus ya koyar da Timotawus ‘al’amuransa da ke cikin Kristi’ sosai. Kuma Timotawus ya fahimci abubuwan da Bulus ya koya masa, don haka Bulus ya ƙaunace shi kuma ya tabbata cewa Timotawus zai lura da ikilisiyar Kirista da ke Koranti. Babu shakka, wannan misali ne mai kyau da dattawa za su iya yin koyi da shi sa’ad da suke koyar da matasa da sa’ad da suke yin ja-goranci a cikin ikilisiya.

DUKANMU MUNA DA AIKI MAI MUHIMMANCI

15. Ta yaya umurnin da Bulus ya yi wa Kiristocin da ke Roma zai taimaka mana idan canje-canje da ake yi sun shafe mu?

15 Muna rayuwa ne a lokacin da ake yawan canje-canje. Kuma sashen ƙungiyar Jehobah da ke nan duniya yana samun ci gaba. Kuma irin waɗannan canje-canjen za su iya shafanmu, don haka, muna bukatar mu kasance da tawali’u kuma mu sa hidimar Jehobah a kan gaba, saboda yin hakan zai sa mu kasance da haɗin kai. Bulus ya rubuta wa Kiristocin da ke Roma cewa: “Nake fāɗa wa kowane mutum wanda ke cikinku, kada shi aza kansa gaba da inda ya kamata; amma ya tuna yadda za shi aza da hankali, gwargwadon yadda Allah ya ɗiba wa kowane mutum rabon bangaskiya. Gama kamar yadda muna da gaɓaɓuwa da yawa cikin jiki ɗaya, dukan gaɓaɓuwa kuma aikinsu ba ɗaya ba ne: haka nan mu, da muke da yawa, jiki ɗaya ne cikin Kristi.”Rom. 12:3-5.

16. Mene ne tsofaffi da matasa da kuma mata suke bukata su yi don ƙungiyar Jehobah ta kasance da haɗin kai da salama?

16 Ko da a wane irin yanayi ne muka sami kanmu, muna bukatar mu ci gaba da goyon bayan Mulkin Jehobah. Tsofaffi kuna bukata ku koyar da matasa don su ma su yi ƙwazo a irin hidimar da kuke yi. Matasa kuma kuna bukata ku nuna cewa kuna a shirye ku yi aikin da aka ba ku, kuma ku kasance da tawali’u kuna girmama tsofaffi. Ku kuma mata, kuna bukatar ku yi koyi da misalin Biriskilla matar Akila da ta tallafa wa mijinta a lokacin da yanayinsu ya canja.A. M. 18:2.

17. Wane tabbaci ne Yesu ya kasance da shi, kuma mene ne ya koyar da mabiyansa su yi?

17 Yesu ma ya kafa mana misali mai kyau a batun koyar da wasu don su yi ƙwazo a hidimar Jehobah. Ya san cewa ya kusan gama hidimarsa a duniya kuma wasu ne za su ci gaba da yin wannan aikin da ya soma. Ko da yake ya san cewa mabiyansa ajizai ne, ya tabbata cewa za su iya yin aikin fiye da wanda ya yi. (Yoh. 14:12) Ya koyar da su sosai kuma sun yaɗa bisharar Mulkin Allah a zamaninsu.Kol. 1:23.

18. Wane bege ne muke da shi, kuma me muke bukatar mu yi yanzu?

18 Bayan mutuwar Yesu, Jehobah ya ta da shi zuwa sama kuma ya ba shi ƙarin aiki da kuma iko da ya fi na “dukan sarauta, da hukunci, da iko, da mulki.” (Afis. 1:19-21) Idan muka mutu da aminci kafin Armageddon, Jehobah zai ta da mu zuwa sabuwar duniya inda za mu yi aiki mai ma’ana kuma mu ji daɗinsa. Amma yanzu da akwai aikin da muke bukatar mu ɗauka da muhimmanci wato yin wa’azin Mulkin Allah. Bari dukanmu tsofaffi da matasa mu “yawaita cikin aikin Ubangiji.”1 Kor. 15:58.