Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Za Ka Iya Zama Mai Tawali’u Sa’ad da Kake Fuskantar Jaraba

Za Ka Iya Zama Mai Tawali’u Sa’ad da Kake Fuskantar Jaraba

“Ka yi tafiya da tawali’u tare da Allahnka?”MI. 6:8.

WAƘOƘI: 48, 95

1-3. Mene ne wani annabi daga Yahuda ya yi, kuma mene ne ya same shi don hakan? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

A LOKACIN da Sarki Jeroboam yake sarauta, Jehobah ya tura wani annabi daga Yahuda ya je wurin sarkin Isra’ila da ya daina bauta masa ya ba sarkin saƙon hukunci. Annabi mai tawali’u ya idar da saƙon Allah, kuma Jehobah ya kāre shi daga hannun mugun sarkin nan Jeroboam.1 Sar. 13:1-10.

2 Amma sa’ad da yake komawa gida, sai ya haɗu da wani tsoho daga Bethel. Mutumin ya ce shi annabin Jehobah ne. Sai ya sa annabin ya ƙi bin umurnin da Jehobah ya ba shi cewa kada ya ‘ci gurasa, ko ya sha ruwa a can’ Isra’ila kuma kada ya ‘juya ko ya koma ta hanyar da ya zo ba.’ Jehobah bai yi farin ciki ba da abin da ya yi. Sa’ad da annabin yake komawa gida, sai zaki ya tare shi a hanya kuma ya kashe shi.1 Sar. 13:11-24.

3 Me ya sa annabi mai tawali’u a dā ya yarda wannan tsohon ya ruɗe shi? Littafi Mai Tsarki bai faɗi dalilin ba. Wataƙila ya manta gabaki ɗaya cewa ya kamata ya yi ‘tafiya da tawali’u tare da Allah.’ (Karanta Mikah 6:8.) A cikin Littafi Mai Tsarki yin tafiya da Jehobah yana nufin dogara a gare shi da goyon bayan sarautarsa da kuma bin ja-gorarsa. Mutum mai tawali’u ya san cewa ya kamata ya ci gaba da yin addu’a ga Jehobah. Ya  kamata wannan annabin ya tambayi Jehobah don ya bayyana masa, amma Littafi Mai Tsarki ba ce ya yi hakan ba. A wasu lokatai, mu ma muna tsai da shawarwari, kuma ba ma sanin abin da ya kamata mu yi. Amma neman taimakon Jehobah zai taimaka mana mu guji yin kura-kurai masu tsanani.

4. Mene ne za mu koya a wannan talifin?

4 A talifin da ya gabata, mun koyi dalilin da ya sa har ila yana da muhimmanci Kiristoci su kasance da tawali’u da kuma abin da nuna wannan halin ya ƙunsa. Amma wane yanayi ne zai sa kasancewa da wannan halin ya yi mana wuya? Ta yaya za mu koyi wannan hali mai kyau don mu kasance da tawali’u ko sa’ad da muke fuskantar jaraba? Don a amsa waɗannan tambayoyin, za mu tattauna yanayi uku da zai hana mu kasancewa da tawali’u, kuma za mu ga matakin da ya kamata mu ɗauka a kowane yanayi.Mis. 11:2.

IDAN YANAYINMU YA CANJA

5, 6. Ta yaya Barzillai ya nuna cewa shi mai tawali’u ne?

5 Yadda muke yin abubuwa sa’ad da yanayinmu ya canja ko kuma aka canja mana aiki zai iya nuna ko muna da tawali’u da gaske. Babu shakka, Barzillai mai shekara 80 ya yi murna sosai a lokacin da Dauda ya gaya masa ya zo ya riƙa zama a fadarsa. Da a ce ya amince da abin da Dauda ya gaya masa, da ya ji daɗin zama da sarkin sosai. Duk da haka, Barzillai ya ƙi. Me ya sa? Ya tsufa don haka, ya gaya wa Dauda cewa ba ya so ya zama masa kaya. Saboda haka, Barzillai ya ce wani mai suna Chimham da wataƙila ɗansa ne ya je fadar yana zama a madadinsa.2 Sam. 19:31-37.

6 Tawali’u ne ya taimaka wa Barzillai ya iya tsai da wannan shawara mai kyau. Bai ƙi zuwa fadar kamar yadda Dauda ya gaya masa don yana ganin ba zai iya yin aikin ba ko kuma don ba ya son zama a wurin da ake yawan hayaniya ba. A maimakon haka, ya fahimci yanayinsa sosai kuma ba ya so ya saka kansa a aikin da ya fi ƙarfinsa ba. (Karanta Galatiyawa 6:4, 5.) Hakazalika, idan muka mai da hankali ga sunan da muke da shi ko matsayi, za mu zama masu girman kai da gāsa kuma ba za mu yi nasara ba. (Gal. 5:26) Amma tawali’u zai taimaka wa ‘yan’uwa su mai da hankali ga baiwa da dukansu suke da shi da kuma ƙwazon da suke yi don su girmama Allah kuma su taimaka ma wasu.1 Kor. 10:31.

7, 8. Ta yaya tawali’u zai taimaka mana mu daina dogara ga iyawarmu?

7 Zai iya yi mana wuya mu kasance da tawali’u idan muka sami iko ko kuma aka ba mu matsayi. A lokacin da Nehemiya ya ji cewa mutanen Urushalima suna shan wahala, ya yi addu’a sosai ga Jehobah. (Neh. 1:4, 11) Mutanen sun sami albarka sa’ad da Sarki Artaxerxes ya naɗa Nehemiya ya zama gwamna a yankin. Duk da haka, ko da yake yana da matsayi da iko da arziki, Nehemiya bai taɓa dogara ga kansa ko baiwar da yake da shi ba. A maimakon haka, ya yi tafiya tare da Allah. A kullum, yana neman taimakon Jehobah ta wurin bincika Kalmar Allah. (Neh. 8:1, 8, 9) Nehemiya bai yi amfani da ikonsa don ya cuci mutane ba, amma ya ba da kansa don ya taimaka musu.Neh. 5:14-19.

8 Misalin Nehemiya ya nuna yadda tawali’u zai taimaka mana mu daina dogara ga iyawarmu sa’ad da aka canja mana aiki ko kuma muka sami ƙarin aiki. Dattijon da ya dogara ga kansa zai iya soma yin ayyukan ikilisiya ba tare da yin addu’a ga  Jehobah da farko ba. Wasu suna iya yanke shawara kafin su yi addu’a ga Jehobah don ya albarkaci shawara da suka tsai da. Amma hakan ya nuna cewa suna da tawali’u ne? Mutum mai tawali’u ba ya dogara ga kansa ko sa’ad da yake yin aikin da ya taɓa yi a dā. Ya san cewa ba zai iya gwada kansa da Allah ba. Idan muna fuskantar matsaloli, ya kamata mu mai da hankali don kada mu dogara ga kanmu. (Karanta Misalai 3:5, 6.) Da yake mu bayin Jehobah ne, bai kamata mu riƙa ganin cewa kasancewa da matsayi ko iko zai iya sa mu fi wasu a iyalinmu ko kuma a ikilisiya ba. A maimakon haka, muna so mu riƙa yin aiki da juna da haɗin kai.1 Tim. 3:15.

SA’AD DA AKE MANA BA’A KO KUMA AKA YABE MU

9, 10. Ta yaya zama masu tawali’u zai taimaka mana mu jimre sa’ad da ake mana ba’a?

9 Zai iya yi mana wuya mu kame kanmu sa’ad da ake mana ba’a. Hannatu ta yi kuka sosai don kishiyarta Peninnah takan tsokane ta kullum. Ko da yake maigidan Hannatu yana son ta, amma ba ta haihu ba. Bayan haka, sa’ad da take addu’a a mazauni, Babban Firist Eli ya ɗauka cewa ta sha giya ta bugu. Duk da haka, Hannatu ta kame kanta kuma ta amsa Eli da ladabi don ita mai tawali’u ce. An saka addu’a mai ban ƙarfafa da ta yi a cikin Littafi Mai Tsarki. Addu’ar ta nuna cewa tana da bangaskiya sosai ga Jehobah kuma tana ƙaunarsa.1 Sam. 1:5-7, 12-16; 2:1-10.

10 Kasancewa da tawali’u zai taimaka mana mu ci gaba da ‘rinjayar mugunta da nagarta.’ (Rom. 12:21) Rayuwa a wannan zamanin ba shi da sauƙi, saboda haka bai kamata mu yi mamaki ba sa’ad da aka yi mana rashin adalci. Ko da yake hakan zai sa mu fushi, ya kamata mu kame kanmu. (Zab. 37:1) Ƙari ga haka, mukan yi baƙin ciki sosai idan muna da matsala da ‘yan’uwanmu, amma mutum mai tawali’u zai yi koyi da Yesu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sa’anda aka zage shi, ba ya mayar da zagi ba; . . . , amma ya danƙa maganarsa  ga wanda ke yin shari’a mai-adalci.” (1 Bit. 2:23) Yesu ya san cewa Jehobah ne mai yin ramako. (Rom. 12:19) Hakazalika, an gargaɗi Kiristoci su zama masu tawali’u kuma kada su riƙa “rama mugunta da mugunta ba.”1 Bit. 3:8, 9.

11, 12. (a) Mene ne zama masu tawali’u zai sa mu yi sa’ad da aka yabe mu ko kuma yi mana daɗin baki? (b) Ta yaya kasancewa masu tawali’u zai shafi irin tufafin da muke sakawa da yadda muke ado da kuma halinmu?

11 Idan ana yawan yabonmu ko kuma yi mana daɗin baki, hakan zai iya sa mu zama masu girman kai. Alal misali, an yabi Esther sosai don tana cikin mata masu gwanin kyau a ƙasar Fasiya kuma an yi mata ado da kayan ƙwalliya na musamman na shekara guda. Ƙari ga haka, kullum tana cuɗanya da ‘yammata da yawa daga dukan Daular Fasiya da suke son sarkin ya aure su. Duk da haka, Esther ta ci gaba da nuna ladabi da natsuwa, kuma ba ta canja halinta ba sa’ad da sarkin ya zaɓe ta ta zama sarauniya.Esther 2:9, 12, 15, 17.

Shin adonka yana nuna cewa kana daraja Jehobah da kuma bayinsa, ko kuma yana nuna cewa ba ka da tawali’u? (Ka duba sakin layi na 12)

12 Idan mu masu tawali’u ne, za mu riƙa saka tufafi da suka dace kuma mu yi ado a hanyar da za ta nuna cewa muna mutunta mutane. Maimakon mu riƙa yin fahariya ko neman burge mutane, za mu yi ƙoƙari mu zama masu “ladabi” da tawali’u. (Karanta 1 Bitrus 3:3, 4; Irm. 9:23, 24) Za mu nuna abin da ke cikin zuciyarmu ta furucinmu da kuma ayyukanmu. Alal misali, muna iya sa mutane su soma ganin mu fitattu ne don abubuwan da muke yi ko iyawarmu ko kuma don ‘yan’uwa sanannu da muke abokantaka da su. Ƙari ga haka, muna iya bayyana abubuwa a hanyar da za ta sa a riƙa yabonmu mu kaɗai don abubuwan da muka cim ma ko da yake mutane ne suka taimaka mana. Amma Yesu ya kafa mana misali mai kyau. Maimakon ya burge mutane da hikimarsa, sau da yawa ya yi ƙaulin Nassosin Ibrananci sa’ad da yake koyarwa. Ya yi hakan don ba ya son mutane su yabe shi amma su yabi Jehobah.Yoh. 8:28.

SA’AD DA MUKE SO MU YANKE SHAWARA

13, 14. Ta yaya zama masu tawali’u zai taimaka mana mu tsai da shawarwari masu kyau?

13 Muna bukatar mu zama masu tawali’u sa’ad da muke tsai da shawarwari. A lokacin da manzo Bulus yake zama a Kaisariya, annabi Agabus ya gaya masa cewa za a kama shi idan ya tafi Urushalima. Ana iya kashe shi ma a wurin, don haka sai ‘yan’uwa suka roƙi Bulus kada ya je. Amma ya ƙi, ba don ya dogara ga kansa ba ko kuma don yana tsoro ba. Bulus ya dogara ga Jehobah kuma yana shirye ya yi hidimarsa ko da mene ne zai faru da shi. Da ‘yan’uwa suka ga ya nace, sai suka bar shi ya tafi Urushalima.A. M. 21:10-14.

14 Zama masu tawali’u zai taimaka mana mu tsai da shawarwari masu kyau ko ma ba mu san abin da zai faru a nan gaba ba. Alal misali, mukan yi tunani cewa, mene ne zai faru idan muka soma rashin lafiya sa’ad da muke hidima ta cikakken lokaci? Idan iyayenmu tsofaffi suna bukatar taimako kuma fa? Ta yaya za mu kula da kanmu sa’ad da muka tsufa? Ba za mu iya sanin amsoshin waɗannan tambayoyin ba ko da mun yi addu’a ko kuma tunani a kansu. (M. Wa. 8:16, 17) Amma, idan mun dogara ga Jehobah za mu san cewa muna da kasawa. Bayan mun yi bincike da neman taimakon wasu da kuma yin addu’a a kan wani batu, muna bukatar mu bi ja-gorar ruhu mai tsarki. (Karanta Mai Wa’azi 11:4-6.) Idan muka yi hakan, Jehobah  zai albarkace mu ko kuma ya taimaka mana mu yanke shawarar da ta dace.Mis. 16:3, 9.

YADDA ZA MU KASANCE MASU TAWALI’U

15. Ta yaya yin tunani game da yadda Jehobah yake taimakonmu zai sa mu zama masu tawali’u?

15 Tun da yake zama masu tawali’u zai amfane ne mu sosai, ta yaya za mu ci gaba da zama masu tawali’u? Bari mu tattauna hanyoyi huɗu da za mu yi hakan. Na farko, muna bukatar mu riƙa yin bimbini game da Jehobah, mu riƙa yin tunani sosai game da halayensa. Kuma sa’ad da muka gwada kanmu da Jehobah, za mu ga cewa ya fi mu sanin abubuwa sosai. (Isha. 8:13) Ya kamata mu tuna cewa muna sha’ani da Maɗaukaki ne ba mala’ika ko kuma ɗan Adam ba. Sanin hakan zai sa mu ‘ƙasƙantar da kanmu a ƙarƙashin hannu mai-iko na Allah.’1 Bit. 5:6.

16. Ta yaya yin bimbini a kan ƙaunar da Allah yake mana zai sa mu kasance masu tawali’u?

16 Na biyu, yin bimbini a kan yadda Jehobah yake ƙaunarmu zai taimaka mana mu zama masu tawali’u. Manzo Bulus ya kwatanta ikilisiyar Kirista da jikin mutum, ya ce Jehobah ya halicci dukan gaɓoɓin jikin mutum da “daraja” sosai. (1 Kor. 12:23, 24) Ƙari ga haka, Jehobah yana kula da mu sosai ko da yake mu ajizai ne. Ba ya kwatanta aikin da muke yi da na wasu ko kuma ya ƙi nuna mana ƙauna saboda kura-kuranmu. Da yake Jehobah yana ƙaunarmu muna samun kwanciyar hankali a duk inda muke hidima.

17. Ta yaya za mu amfana idan muka mai hankali ga halaye masu kyau na ‘yan’uwanmu?

17 Hanya ta uku ita ce, nuna godiya don hidima da muke yi a ƙungiyar Jehobah da kuma mai da hankali ga halaye masu kyau na ‘yan’uwanmu. Maimakon mu riƙa son zama a kan gaba ko muna son gaya wa mutane abubuwan da za su yi, zai dace mu nemi shawara daga wurinsu kuma mu yi abin da suka faɗa. (Mis. 13:10) Ƙari ga haka, za mu yi musu murna sa’ad da suka sami wani gata a cikin ikilisiya. Ban da haka ma, za mu yabe Jehobah don yadda yake yi wa ‘ ’yan’uwanmu da ke cikin duniya’ albarka.1 Bit. 5:9.

18. Ta yaya yin nazari Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu zama masu tawali’u?

18 Hanya ta huɗu ita ce bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a rayuwarmu. Idan muna yin hakan, za mu kasance da ra’ayin da ya dace kuma za mu fahimci ra’ayin Jehobah a kan batutuwa dabam-dabam. Yin nazarin Littafi Mai Tsarki da addu’a da kuma yin amfani da abubuwan da muka koya zai taimaka mana mu kasance da halin kirki. (1 Tim. 1:5) Ban da haka ma, za mu koya saka bukatun wasu a gaba da namu. Idan muna yin hakan, Jehobah ya yi alkawarin cewa zai “kammala” koyar da mu kuma zai taimaka mana mu zama masu tawali’u kuma mu kasance da wasu halaye masu kyau.1 Bit. 5:10.

19. Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da kasance wa masu tawali’u har abada?

19 Girman kan annabin da ya fito daga Yahudiya da muka ambata ɗazu ya sa ya rasa ransa kuma ya ɓata dangantakarsa da Jehobah. Babu shakka, za mu iya zama masu tawali’u ko da muna fuskantar jaraba. Bayin Allah a dā da kuma a yanzu sun nuna cewa hakan yana iya yiwuwa. Koya game da Jehobah zai taimaka mana mu ci gaba da zama masu tawali’u. (Mis. 8:13) Ko da wane irin yanayi ne muke ciki yanzu sanin Jehobah gata ne babba. Muna bukata mu ɗauki wannan gatan da muhimmanci sosai, kuma mu ci gaba da bauta wa Jehobah da tawali’u har abada.