Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ESTHER 6-10

Esther Ta Yi Sadaukarwa don Jehobah da Kuma Bayinsa

Esther Ta Yi Sadaukarwa don Jehobah da Kuma Bayinsa

Esther ta yi sadaukarwa kuma ta nuna gaba gaɗi wajen kāre bayin Jehobah

8:3-5, 9

  • Esther da Mordekai sun sami kāriya. Amma, an kusan idar da saƙon hukunci da Haman ya zartar a kan Yahudawan da ke daular baki ɗaya

  • Esther ta sake saka ranta cikin haɗari ta wajen zuwa wurin sarkin ba tare da ya gayyace ta ba. Ta yi kuka don mutanenta kuma ta ce sarkin ya soke dokar da aka kafa da sunan sarkin

  • A lokacin, ba a iya soke dokar da aka kafa da sunan sarki. Saboda haka, sarkin ya ƙarfafa Esther da Mordekai su kafa wata sabuwar doka

Jehobah ya sa bayinsa sun yi nasara

8:10-14, 17

  • An kafa wata doka da ta ba Yahudawa izinin kāre kansu

  • Mahaya sun hanzarta zuwa wurare dabam-dabam don su sanar da wannan saƙon, kuma Yahudawa sun yi shirin yaƙi

  • Mutane da yawa sun ga alamar cewa Allah yana goyon bayansu kuma sun soma bin addinin Yahudawa