Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Ku Marabci Bakin da Suka Hallara

Ku Marabci Bakin da Suka Hallara

A ranar 23 ga Maris, muna sa rai cewa mutane wajen miliyan 12 ko kuma fiye da hakan za su halarci taron Tuna da mutuwar Yesu. Babu shakka, za su amfana sosai daga jawabin da za a yi da zai nuna yadda Jehobah ya yi mana tanadin fansa da kuma albarkar da fansar za ta kawo mana a nan gaba! (Ish 11:6-9; 35:5, 6; 65:21-23; Yoh 3:16) Amma, ba mai jawabin ba ne kaɗai zai taimaka wa mahalartan ba. Dukanmu muna da hakkin marabtar baƙin da suka halarci taron. (Ro 15:7) Ga wasu shawarar da za mu iya bi.

  • Maimakon ka zauna a wurin zamanka kana jiran a soma taron, zai dace ka gai da baƙin da suke shigowa, kuma ka yi haka da fara’a

  • Maimakon mai da hankali ga mutanen da ka gayyata kawai, zai dace ka marabci mutanen da suka halarci taron domin an ba su takardar gayyata. Ka ce sababbi su zauna da kai. Ka sa su yi amfani da naka Littafi Mai Tsarki da kuma littafin waƙa

  • Bayan jawabin, ka amsa tambayoyin da suke da shi. Amma idan babu isashen lokaci domin wata ikilisiya tana son ta yi amfani da majami’ar, ku shirya yadda za ku sake haɗuwa bayan ‘yan kwanaki kaɗan don ka amsa tambayoyinsa. Idan ba ka san adireshinsa ko kuma lambar wayarsa ba, za ka iya ce masa: “Zan so mu tattauna abubuwan da ka lura a taron. A ina za mu iya sake haɗuwa?”