Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYUBA 11-15

Ayuba Ya Yi Imani da Tashin Matattu

Ayuba Ya Yi Imani da Tashin Matattu

Ayuba ya yi imani cewa Allah zai ta da shi daga matattu

14:7-9, 13-15

  • Ayuba ya yi amfani da bishiya, wataƙila bishiyar zaitun wajen nuna tabbaci da yake da shi cewa Allah zai ta da shi daga matattu

  • Bishiyar zaitun tana da jijiyoyi masu shiga ƙasa sosai kuma hakan yakan sa ta sake tsiro bayan an datse bishiyar. Muddin jijiyoyin ba su mutu ba, za su sake tsirowa

  • Idan aka yi ruwan sama bayan fāri mai tsawo, kututturen bishiyar zaitun zai iya sake tsirowa kuma “ya yi rassa”