Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYUBA 1-5

Ayuba Ya Yi Aminci Sa’ad da Ya Fuskanci Gwaji

Ayuba Ya Yi Aminci Sa’ad da Ya Fuskanci Gwaji

Ayuba yana zama a ƙasar Uz a lokacin da Isra’ilawa suke bauta a Masar. Ko da yake Ayuba ba Ba’isra’ile ba ne, amma ya bauta wa Allah da aminci. Mutanen gidansa suna da yawa, yana da arziki kuma yana da suna a yankinsa. Shi mashawarci da kuma alƙali ne mai adalci. Karimi ne ga talakawa. Babu shakka, Ayuba mutumi ne mai aminci.

Ayuba ya nuna sarai cewa Jehobah ne ya fi muhimmanci a rayuwarsa

1:8-11, 22; 2:2-5

  • Shaiɗan ya lura cewa Ayuba yana da aminci. Bai musanta cewa Ayuba yana da aminci ba, amma ya ce ba da zuciya ɗaya yake hakan ba

  • Shaiɗan ya ce Ayuba yana bauta wa Jehobah saboda alherin da yake masa

  • Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya gwada Ayuba domin ya san cewa da’awarsa ƙarya ce. Shaiɗan ya sa Ayuba ya fuskanci matsanancin yanayi

  • Sa’ad da Ayuba ya ci gaba da yin aminci, sai Shaiɗan ya ƙalubalanci dukan mutane

  • Ayuba bai yi zunubi ba kuma bai ɗaura wa Allah laifi ba