Ana taron Tuna da Mutuwar Yesu a ƙasar Jamus

LITTAFIN TARO DON RAYUWA TA KIRISTA DA HIDIMARMU Maris 2016

Gabatarwa

Shawara a kan yadda za ku iya ba da Hasumiyar Tsaro da kuma takardar gayyata na taron tuna da mutuwar Yesu na shekara ta 2016. Ka yi amfani da misalan nan don ka rubuta taka gabatarwar.

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Esther Ta Yi Sadaukarwa don Jehobah da Kuma Bayinsa

Da gaba gadi, ta sa ranta cikin hadari kuma ta taimaka wa Mordekai don ya samar da dokar da za ta kare Yahudawa daga hallaka. (Esther 6-10)

KA YI WA’AZI DA KWAZO

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Ka Rubuta Taka Gabatarwa

Ka yi amfani da shawarwarin nan don ka rubuta taka gabatarwa ta Hasumiyar Tsaro da kuma Awake!

RAYUWAR KIRISTA

Ku Marabci Bakin da Suka Hallara

Ta yaya za mu iya marabtar baki da kuma wadanda suka yi sanyin gwiwa a ibadarsu da suka halarci taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ayuba Ya Yi Aminci Sa’ad da Ya Fuskanci Gwaji

Ya nuna cewa Jehobah ne ya fi muhimmanci a rayuwarsa. (Ayuba 1-5)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ayuba Mutum Mai Aminci Ya Nuna Takaicinsa

Ayuba ya damu kuma ya karaya, hakan ya shafi tunaninsa amma bai daina kaunar Jehobah ba. (Ayuba 6-10)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

Ayuba Ya Yi Imani da Tashin Matattu

Ya san cewa Jehobah zai ta da shi daga mutuwa kamar yadda kututturen bishiya yake tsirowa daga saiwarsa. (Ayuba 11-15)

RAYUWAR KIRISTA

Fansar Yesu Ta Sa Ya Yiwu a Ta da Matattu

Fansar da Jehobah ya tanadar ta sa muna da begen tashin matattu. Maimakon bakin cikin domin an yi mana rasuwa, za mu marabce su sa’ad da suka tashi da matattu.