Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RAYUWAR KIRISTA

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Taimaka Ma Wadanda Suke So Su Zama Mabiyan Yesu

Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi​—Taimaka Ma Wadanda Suke So Su Zama Mabiyan Yesu

MUHIMMANCINSA: Jehobah yana taimaka ma “waɗanda suke da zuciya ta samun rai na har abada” su zo su bauta masa. (A. M 13:​48, New World Translation; 1Ko 3:7) Muna wannan aikin tare da shi ta wajen mai da hankali ga waɗanda suke aikata abin da suke koya. (1Ko 9:26) Muna bukatar mu taimaka musu su fahimci cewa wajibi ne su yi baftisma idan suna son su sami ceto. (1Bi 3:21) Mu taimaka wa ɗalibanmu su zama mabiyan Yesu ta wajen koya musu yadda za su gyara rayuwarsu da yin wa’azi da kuma keɓe kansu ga Jehobah.​—Mt 28:​19, 20.

YADDA ZA MU CIM MA HAKAN:

  • Ku tuna wa ɗalibanku cewa ainihin dalilin da ya sa kuke nazari da su shi ne don su “san” Jehobah kuma su faranta masa rai.​—Yoh 17:3

  • Ku taimaka musu su daina halayen banza da kuma tarayya da abokan banza

  • Ku riƙa ƙarfafa su sosai kafin su yi baftisma da kuma bayan sun yi hakan.​—A. M 14:22

KU KALLI BIDIYON NAN JEHOBAH ALLAH ZAI TAIMAKE KA, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Mene ne zai iya sa mutum ya ji tsoron yin alkawarin bauta ma Jehobah kuma ya yi baftisma?

  • Ta yaya dattawa za su taimaka wa ɗaliban Littafi Mai Tsarki su sami ci gaba a ibadarsu?

  • Mene ne littafin Ishaya 41:10 ya koya mana game da Jehobah?

  • Waɗanne halaye ne za su taimaka mana mu bauta wa Jehobah da kyau duk da cewa mu ajizai ne?

Ta yaya muke yin aiki tare da Jehobah a wa’azi?