Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 RAYUWAR KIRISTA

Mu Yabi Jehobah Ta Wurin Rera Waka da Farin Ciki

Mu Yabi Jehobah Ta Wurin Rera Waka da Farin Ciki

Bulus da Sila sun rera waƙoƙin yabo ga Jehobah sa’ad da suke cikin kurkuku. (A. M 16:25) Babu shakka, hakan ya ƙarfafa su sosai. Mu kuma fa? Waƙoƙin da muke yi a taro da kuma waƙoƙin jw suna ƙarfafa mu da kuma taimaka mana mu jimre matsaloli. Ban da haka ma, suna ɗaukaka Jehobah. (Za 28:7) Ƙungiyarmu tana ƙarfafa mu cewa zai yi kyau mu haddace wasu daga cikin waƙoƙin nan. Ka taɓa yin hakan? Za mu iya yin amfani da lokacin ibada ta iyalinmu don mu koyi da kuma haddace waƙoƙin nan.

KU KALLI BIDIYON NAN YARA NA YABON JEHOBAH DA WAƘOƘI, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Ta yaya za mu amfana daga rera waƙoƙin Mulki?

  • Wane shiri ne sashen Sauti da Bidiyo suke yi kafin su yi rikodin na waƙa?

  • Ta yaya yara da iyayensu suke yin shiri don waƙar da za su rera?

  • A cikin waƙoƙin Mulki, wanne ne ka fi so kuma me ya sa?