Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

A Dā Ina Tsoron Mutuwa!

A Dā Ina Tsoron Mutuwa!
  • SHEKARAR HAIHUWA: 1964

  • ƘASAR HAIHUWA: INGILA

  • TARIHI: NI ‘YAR ISKA CE SA’AD DA NAKE MATASHIYA

RAYUWATA A DĀ

An haife ni a yankin Paddington da ke birnin Landan, a ƙasar Ingila. Ina zama da mahaifiyata da kuma yayyena uku. Mahaifinmu ba ya yawan zama a gida domin shi mashayi ne.

Sa’ad da nake ƙarama, mahaifiyata ta koya mini yin addu’a kowane dare. Ina da wani ƙaramin Littafi Mai Tsarki da ke ɗauke da littafin Zabura kaɗai, kuma na kirkiro sauti don in riƙa rera ta. Na tuna wani furuci da na taɓa karantawa a wani littafi da ba zan taɓa mantawa ba. Ya ce: “Wata rana, ba za mu wanzu ba.” Furucin ya hana ni yin barci daddare domin ina tunanin yadda rayuwata za ta kasance a nan gaba. Na ce wa kaina, ‘Babu shakka, rayuwa tana da ma’ana. Me ya sa nake wanzuwa?’ Ba na so in mutu!

Sai na soma sha’awar maitanci. Na yi ƙoƙarin yin magana da mutanen da suka mutu, ina yawan zuwa makabarta tare da abokan makarantarmu, kuma muna kallon fina-finai masu ban tsoro. Muna jin daɗin kallon fina-finan duk da cewa muna jin tsoro.

Na soma rayuwar banza sa’ad da nake ‘yar shekara goma. Na soma shan taba sigari, kuma na shaƙu da shi sosai. Bayan haka, sai na soma shan wi-wi. Da na kai shekara 11, sai na soma shan giya. Ko da yake ba na jin daɗinsa, amma yana ƙayatar da ni idan na bugu. Ina son waƙa da kuma rawa sosai. Ina zuwa duk inda ake yin fati da daddare. Ina sulale in fita daddare kuma in dawo kafin gari ya waye. Washegari, sai in fasa makaranta don na gaji sosai. Amma a ranar da na je makaranta, ina yawan shan giya.

Na faɗi jarrabawar sauke karatu. Hakan ya sa mahaifiyata fushi sosai don ba ta san irin rayuwar da nake yi ba. Mun yi gardama da ita, sai na bar gida. Na koma zama da saurayina mai suna Tony na ɗan lokaci. Yana sata da saurin fushi kuma yana sayar da ƙwayoyi. Ba da daɗewa ba, sai na yi ciki kuma na haifi ɗanmu na fari sa’ad da nake ‘yar shekara 16.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA

Na fara haɗuwa da Shaidun Jehobah sa’ad da nake zama a masaukin mata masu jego marasa aure. Hukuma ta ba ni ɗaki a masaukin. Shaidu biyu mata suna yawan kawo ziyara wurin matan da ke masaukin. Wata rana sai na tattauna da su. Na so in nuna musu cewa ba sa faɗin gaskiya. Duk da haka, sun yi amfani da Littafi Mai Tsarki wajen amsa dukan tambayoyin da na yi musu a hanya mai sauƙi. Matan suna da sauƙin kai da kirki kuma hakan ya sosa zuciyata sosai. Sai na yarda su soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni.

Ba da jimawa ba, sai na koyi wani abu a Littafi Mai Tsarki da ya canja rayuwata. Tun ina ƙarama, ba na so in mutu. Yanzu na gane koyarwar Yesu game da tashin matattu. (Yohanna 5:28, 29) Na sake koya cewa Allah yana kula da ni sosai. (1 Bitrus 5:7) Kalmomin da ke Irmiya 29:11 sun ƙarfafa ni. Ayar ta ce: “Gama na san irin tunanin da ni ke tunaninku da su, in ji Ubangiji, tunani na lafiya, ba na masifa ba, domin im ba ku bege mai-kyau a ƙarshe.” Sai na soma yin imani cewa zan iya rayuwa har abada a Aljanna a duniyar nan.Zabura 37:29.

Shaidun Jehobah sun nuna mini ƙauna sosai. Da farko da na halarci taronsu, na lura cewa suna da fara’a sosai kuma sun marabce ni da hannu bibbiyu. (Yohanna 13:34, 35) Hakan ya bambanta sosai da yadda aka marabce ni a wani coci. Shaidun sun marabce ni duk da yanayina. Sun kula da ni kuma sun taimaka mini sosai. Sai na ga cewa suna ƙaunar juna sosai.

Na koya a nazarin da nake yi cewa zan bukaci yin canje-canje da dama don rayuwata ta jitu da ƙa’idodin Allah. Bai kasance mini da sauƙi in daina shan taba sigari ba. Har ila, na gane cewa wasu waƙoƙi suna tayar mini da sha’awar shan wi-wi. Saboda haka, sai na canja irin waƙoƙin da nake ji. Na daina zuwa fati da hotal don kada in riƙa buguwa da giya. Sai na soma tarayya da abokan kirki waɗanda halinsu zai taimaka mini.Misalai 13:20.

Tony ma yana nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah a lokacin. Da Shaidu suka yi amfani da Littafi Mai Tsarki wajen amsa tambayoyinsa, sai shi ma ya yi imani da abin da yake koya. Ya yi canje-canje sosai. Ya daina sata da shan wi-wi kuma ya daina tarayya da abokansa masu faɗa. Don mu faranta wa Jehobah rai, mun ga cewa ya dace mu daina rayuwar banza don mu taimaka wa ɗanmu. Mun yi aure a shekara ta 1982.

“Na daina farkawa daddare don tsoron mutuwa da kuma abin da zai faru a nan gaba”

Na tuna lokacin da nake neman labaran mutanen da suka yi nasara wajen canja rayuwarsu a mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! * Labaran da na karanta sun ƙarfafa ni! Sun sa in ga cewa bai kamata in gudu ko in ja-da-baya ba. Na ci gaba da yin addu’a ga Jehobah cewa kada ya yatsar da ni. Ni da maigidana Tony mun yi baftisma a matsayin Shaidun Jehobah a watan Yuli na shekara ta 1982.

YADDA NA AMFANA

Kasancewa da dangantaka da Jehobah ya cece ni. Ni da maigidana mun shaida taimakon Jehobah a mawuyacin lokaci. Mun ga ya dace mu dogara ga Allah a mawuyacin lokaci, kuma mun ga cewa yana taimaka wa iyalinmu.Zabura 55:22.

Ina jin daɗin taimaka wa ɗanmu da ‘yarmu su san Jehobah. Yanzu ina farin cikin ganin cewa yaransu ma suna bauta wa Allah.

A yau, na daina farkawa daddare don tsoron mutuwa da kuma abin da zai faru a nan gaba. Ni da maigidana muna ziyarar ikilisiyoyin Shaidun Jehobah dabam-dabam kowane mako don mu ƙarfafa su. Muna zuwa wa’azi tare da ‘yan’uwan don mu koya wa mutane cewa idan sun yi imani da Yesu, za su sami rai na har abada.

^ sakin layi na 17 Shaidun Jehobah ne suka wallafa su.