Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA ZA KA JI DAƊIN KARANTA LITTAFI MAI TSARKI

Me Zai Sa Ka Ji Dadin Karatun?

Me Zai Sa Ka Ji Dadin Karatun?

Shin kana jin daɗin karanta Littafi Mai Tsarki ne ko a’a? Da akwai abubuwa da yawa da za ka iya yi da za su sa ka ji daɗin karatun. Bari mu yi la’akari da waɗannan abubuwan.

Ka yi amfani da fassara mai sauƙin fahimta. Ba za ka ji daɗin karatun Littafi Mai Tsarki ba idan ka yi amfani da fassarar da aka yi amfani da kalmomin dā ko kuma mai wuyan fahimta. Don haka, ka nemi juyin Littafi Mai Tsarki mai sauƙin fahimta da kuma wanda zai ratsa zuciyarka. Ƙari ga haka, ka nemi Littafi Mai Tsarki da aka fassara da kyau sosai. *

Ka yi amfani da fasaha na zamani. A yau, za a iya samu Littafi Mai Tsarki a intane. Za ka iya karanta Littafi Mai Tsarki a intane ko kuma ka saukar da shi a kwamfutarka ko kuma wayarka. Akwai wasu fasaha da za su iya sa ka duba wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki da suka yi magana a kan batun da kake bincike a kai ko kuma ka gwada da wasu fassara dabam. Idan kuma kana so ka saurari karatun ne kawai, da akwai sautin Littafi Mai Tsarki. Mutane da yawa suna jin daɗin karatun Littafi Mai Tsarki sa’ad da suke tafiya a cikin mota ko suke wanki ko kuma suke wani aikin da zai iya barin su su saurari karatun. Ka yi amfani da wanda ka fi so.

Ka yi amfani da abubuwan da za su inganta nazarin. Yin amfani da abubuwan da za su inganta nazari za su iya taimaka maka ka ji daɗin karatun. Da akwai taswirar ƙasashen da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki. Wannan zai taimaka maka ka  nemi wuraren da aka ambata a karatun da kake yi kuma ka gan kamar abubuwan suna faruwa ne a gabanka. Talifofin da ke cikin wannan mujallar ko kuma a sashen “Koyarwar Littafi Mai Tsarki” a dandalinmu na jw.org/ha, za su taimaka maka ka san ma’anar wasu abubuwa a cikin Littafi Mai Tsarki.

Ka riƙa canja yadda kake karatun. Idan ba ka jin daɗin karanta Littafi Mai Tsarki daga farko zuwa ƙarshe, za ka iya somawa da littafin da ka fi so. Idan kana so ka san game da mutanen da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki, kana iya karanta surorin da suka yi magana game da su. An nuna hanyoyin da za ka iya bi da karatun Littafi Mai Tsarki a cikin akwatin nan “ Ka San Mutanen da Aka Ambata a Cikin Littafi Mai Tsarki.” Kana kuma iya karanta Littafi Mai Tsarki bisa ga batutuwa ko kuma yadda abubuwa suka faru. Ka gwada yin amfani da waɗannan hanyoyin.

^ sakin layi na 4 Mutane da yawa sun ga cewa fassarar New World Translation of the Holy Scriptures daidai ne, kuma yana da sauƙi karantawa da kuma fahimta. Shaidun Jehobah ne suka buga wannan Littafi Mai Tsarki kuma ana samun sa a harsuna fiya da 130. Za ka iya saukar da na Turanci a dandalinmu na jw.org ko kuma ka saukar da manhajar JW Library. Idan kuma kana so, Shaidun Jehobah za su kawo maka shi har gidanka.