Wane ne Jehovah?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Jehovah shi ne Allah na gaskiya kamar yadda aka bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki, kuma shi ne Mahaliccin dukan abubuwa. (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Annabawa kamar Ibrahim da Musa sun bauta masa, kuma Yesu ma ya yi hakan. (Farawa 24:27; Fitowa 15:1, 2; Yohanna 20:17) Shi ba Allah na al’umma daya ba ne kawai, amma shi Allah ne “bisa dukan duniya.”—Zabura 47:2.
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehovah shi ne sunan Allah. (Fitowa 3:15; Zabura 83:18) An samo sunan daga kalmar Ibrananci da ke nufin “ya kasance” kuma masana da yawa suna ganin ma’anar sunan shi ne “Yana Sa Ya Kasance.” Wannan ma’anar ta yi daidai da matsayin Jehovah na Mahalicci da kuma Mai cika nufinsa. (Ishaya 55:10, 11) Kari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana ainihin halin Jehovah, musamman ma halinsa na ƙauna.—Fitowa 34:5-7; Luka 6:35; 1 Yohanna 4:8.
A Ibrananci, ana rubuta sunan Allah, wato Jehovah, da bakaken nan hudu, wato יהוה ko kuma YHWH. Ba a san ainihi yadda ake kiran sunan da Ibrananci na dā ba, amma an yi amfani da sunan nan Jehovah, a Turanci a cikin juyin The Holy Bible in Hausa da United Bible Societies suka buga a 1932.
Me ya sa ba a san ainihi yadda ake kiran sunan Allah da Ibrananci a dā ba?
A dā, ana rubuta Ibrananci da bakake ne kadai, babu wasula. Duk wanda yake magana a lokacin ya san wasula da ya kamata ya yi amfani da su. Amma bayan da aka gama rubuta Nassosin Ibrananci (wato, “Tsohon Alkawari”), wasu Yahudawa suka fitar da al’adar nan cewa sunan Allah yana da tsarki sosai saboda haka, bai kamata a kira sunan ba. Idan suna karanta wani nassin da ke dauke da sunan Allah, sai su yi amfani da lakabi kamar “Ubangiji” ko “Allah” a maimakon sunan. Da shigewar lokaci, mutane da yawa suka amince da wannan al’adar kuma hakan ya sa ba a sake sanin yadda ake kira sunan ba gaba daya. a
Wasu suna ganin ana kiran sunan “Yahweh” ne, amma wasu suna ganin ba haka ba ne. Wani nadadden littafi da ake kira A Dead Sea Scroll da ke dauke da wasu surorin littafin Levitikus a Helenanci ya nuna cewa ana kira sunan Iao. Marubutan Helenanci na farko sun ce mai yiwuwa ana kira sunan Iae ko I·a·beʹ, ko kuma I·a·ou·eʹ, amma babu wani tabbaci da ya nuna cewa haka aka kira sunan da Ibrananci a dā. b
Wasu ra’ayoyi game da sunan Allah da ba daidai ba
Ra’ayi: Mafassaran wasu juyin Littafi Mai Tsarki da suka yi amfani da sunan nan “Jehovah” sun bi ra’ayinsu ne kawai.
Gaskiyar al’amarin: Bakake hudu na Ibrananci da ake amfani da su a madadin sunan Allah sun fito wajen sau 7000 a cikin Littafi Mai Tsarki. c Yawancin mafassaran Littafi Mai Tsarki sun cire sunan Allah daga cikin fassararsu kamar yadda suka ga dama kuma sun sauya shi da lakabi kamar “Ubangiji.”
Ra’ayi: Allah Mai Iko Duka ba ya bukatar wani suna da zai bambanta shi.
Gaskiyar al’amarin: Allah da kansa ya hure marubutan Littafi Mai Tsarki su yi amfani da sunansa sau dubun dubbai kuma ya ce wadanda suke bauta masa su yi amfani da wannan sunan. (Ishaya 42:8; Joel 2:32; Malakai 3:16; Romawa 10:13) Ya la’anta annabawan karya da suka yi kokari su sa mutanensa mancewa da sunansa.—Irmiya 23:27.
Ra’ayi: Bisa ga al’adar Yahudawa, ya kamata a cire sunan Allah daga Littafi Mai Tsarki.
Gaskiyar al’amarin: Gaskiya ne cewa wasu marubutan Yahudawa sun ki su kira sunan Allah. Amma ba su cire sunan daga cikin Littafi Mai Tsarki da suka kwafa ba. Gaskiyar ita ce, Allah ba ya so mu bi al’adun ’yan Adam da suka saba wa dokokinsa.—Matta 15:1-3.
Ra’ayi: Bai kamata a rubuta sunan Allah a cikin Littafi Mai Tsarki ba domin ba a san ainihi yadda ake furta shi da Ibrananci ba.
Gaskiyar al’amarin: Wadanda suke da ra’ayin nan suna ganin kamar Allah yana so duka mutanen da suke yare dabam-dabam su kira sunansa a ta hanya daya. Amma Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa masu bauta wa Allah a zamanin dā sun kira sunaye dabam-dabam bisa ga harshensu.
Alal misali, ku yi la’akari da wannan alkali Ba’isra’ile mai suna Joshua. Kiristoci na farko da suke Ibrananci sun kira sunansa Yehoh·shuʹaʽ, amma Kiristocin da suke Helenanci sun kira shi I·e·sousʹ. Littafi Mai Tsarki yana dauke da fassarar sunan Joshua daga Ibrananci zuwa Helenanci, kuma hakan ya nuna cewa Kiristoci sun yi amfani da sunaye bisa ga yadda aka furta su a yarensu.—Ayyukan Manzanni 7:45; Ibraniyawa 4:8.
Haka ma yake da sunan Allah. Abin da ya fi muhimmanci shi ne yin amfani da sunan Allah a wurin da ya kamata a cikin Littafi Mai Tsarki, ba kira sunan ainihi yadda aka kira shi a dā ba.
a New Catholic Encyclopedia, Second Edition, Kundi na 14, shafuffuka na 883-884, ya ce: “Bayan Yahudawa suka yi shekaru da dawowa daga Bauta a Babila, sai suka soma ganin kamar bai kamata a kira sunan Yahweh ba domin yana da tsarki sosai. Hakan ya sa suka soma amfani da ADONAI ko ELOHIM, a maimakon su kira Yahweh.”
b Don karin bayani, ka duba jigon nan “Sunan Allah a Cikin Nassosin Ibrananci,” a cikin kasidar nan Taimako don Nazarin Kalmar Allah.
c Ka duba the Theological Lexicon of the Old Testament, Volume 2, shafuffuka na 523-524.