Ta Hannun Yohanna 13:1-38
13 Ana nan tun kafin Bikin Ƙetarewa ya yi, Yesu ya riga ya sani cewa lokacinsa ya yi da zai bar wannan duniyar kuma ya koma wurin Uban, Yesu ya ƙaunaci mutanensa da suke a duniya, ya kuma nuna musu ƙaunarsa har ƙarshe.
2 Yesu da almajiransa suna cin abincin yamma, kuma Ibilis ya riga ya saka a zuciyar Yahuda Iskariyoti, ɗan Siman, ya ci amanar Yesu.
3 Da yake Yesu ya san cewa Uban ya sa dukan abubuwa a hannunsa, ya kuma san cewa ya fito ne daga wurin Allah kuma zai koma wurin Allah,
4 sai ya tashi, ya cire mayafinsa ya ajiye a gefe kuma ya ɗauki tawul ya ɗaura a kwankwasonsa.
5 Bayan haka, ya zuba ruwa a ƙaramin daro, sai ya soma wanke ƙafafun almajiransa kuma yana share ƙafafunsu da tawul da ya ɗaura a kwankwasonsa.
6 Da ya zo kan Siman Bitrus, sai Bitrus ya ce masa: “Ubangiji, kana so ka wanke mini ƙafafu?”
7 Sai Yesu ya amsa masa ya ce: “Ba ka fahimci abin da nake yi yanzu ba, amma bayan da na yi abubuwan nan, za ka fahimta.”
8 Bitrus ya ce masa: “Ba za ka taɓa wanke ƙafafuna ba.” Sai Yesu ya amsa masa ya ce: “Idan ban wanke ƙafafunka ba, babu abin da zai haɗa ni da kai.”
9 Sai Siman Bitrus ya ce masa: “Ya Ubangiji, ba ma ƙafafuna kaɗai za ka wanke ba, amma ka wanke har da hannayena da kaina ma.”
10 Yesu ya ce masa: “Duk wanda ya yi wanka, ƙafafunsa kawai ne yake bukatar ya wanke domin ya riga ya tsabtace jikinsa. Kuma kuna da tsabta, amma ba dukanku ba ne.”
11 Domin ya san mutumin da zai ci amanarsa. Shi ya sa ya ce: “Ba dukanku ba ne kuke da tsabta.”
12 Bayan da ya gama wanke ƙafafunsu kuma ya saka mayafinsa, ya koma ya zauna a teburi, sai ya tambaye su, ya ce: “Kun fahimci abin da na yi muku?
13 Kuna kira na ‘Malam’ da kuma ‘Ubangiji,’ kuma gaskiyarku ne, domin ni Malam ne da kuma Ubangiji.
14 Saboda haka, idan ni, duk da cewa Ubangiji ne da kuma Malam, na wanke ƙafafunku, dole ne ku ma ku wanke ƙafafun juna.
15 Na nuna muku misali, domin ku ma ku yi yadda na yi muku.
16 A gaskiya ina gaya muku, bawa bai fi maigidansa ba, kuma wanda aka aiko bai fi wanda ya aiko shi ba.
17 Yanzu da kuka san waɗannan abubuwan, za ku yi farin ciki idan kuka yi su.
18 Ba na magana game da dukanku; na san waɗanda na zaɓa. Amma hakan zai faru ne domin a cika abin da ke cikin nassi da ya ce: ‘Wanda yake cin abincina a dā ya juya mini baya.’
19 Daga yanzu, ina gaya muku wannan kafin ya faru, domin a lokacin da ya faru, za ku ba da gaskiya cewa ni ne shi.
20 A gaskiya ina gaya muku, duk wanda ya karɓi wanda na aika, ya karɓe ni ma, kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi Wanda ya aiko ni ma.”
21 Bayan da Yesu ya faɗi abubuwan nan, sai ya damu sosai, kuma ya faɗa a fili cewa: “A gaskiya ina gaya muku, ɗaya daga cikinku zai ci amanata.”
22 Sai almajiransa suka soma kallon juna, don ba su san almajirin da Yesu yake magana a kansa ba.
23 Ɗaya cikin almajiransa, wanda Yesu yake ƙauna, yana zaune kusa da* Yesu.
24 Sai Siman Bitrus ya yi ma almajirin alama da hannu cewa: “Ka gaya mana wanda yake magana game da shi.”
25 Sai almajirin ya matso kusa da Yesu kuma ya tambaye shi cewa: “Ubangiji, wane ne shi?”
26 Yesu ya amsa ya ce: “Wanda zan ba ma gutsuren burodin da na tsoma a cikin kwano, shi ne mutumin.” Bayan da ya tsoma burodin a cikin kwano, sai ya ɗauka, ya ba Yahuda, ɗan Siman Iskariyoti.
27 Da Yahuda ya karɓi gutsuren burodin, sai Shaiɗan ya shiga cikin zuciyarsa. Yesu ya ce masa: “Abin nan da kake yi, ka yi shi da sauri.”
28 Amma, babu wani a cikin waɗanda suke cin abinci tare da shi a teburin da ya san dalilin da ya sa ya gaya masa hakan.
29 Hakika, wasu suna tunani cewa, tun da Yahuda ne yake riƙe jakar kuɗi, Yesu yana gaya masa ne cewa, “Ka sayo abubuwan da muke bukata don bikin,” ko kuma ya ba wa talakawa wani abu.
30 Saboda haka, bayan da ya karɓi gutsuren burodin, sai ya fita nan da nan. Kuma a lokacin dare ya yi.
31 Da Yahuda ya fita, sai Yesu ya ce: “Yanzu an ɗaukaka Ɗan mutum, kuma an ɗaukaka Allah ta wurinsa.
32 Allah da kansa zai ɗaukaka shi, kuma zai yi hakan nan da nan.
33 Yara ƙanana, ina tare da ku na ɗan lokaci. Za ku neme ni; amma kamar yadda na gaya wa Yahudawa, ‘Wurin da zan je, ba za ku iya zuwa ba,’ yanzu ina gaya muku ku ma.
34 Ina ba ku sabuwar doka, wato, ku ƙaunaci juna, kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku riƙa ƙaunar juna.
35 Ta haka, kowa zai san cewa ku almajiraina ne, idan kuna ƙaunar juna.”
36 Siman Bitrus ya ce masa: “Ubangiji, ina za ka je?” Yesu ya amsa masa ya ce: “Wurin da zan je, ba za ka iya bi na yanzu ba, amma za ka bi ni daga baya.”
37 Bitrus ya ce masa: “Ubangiji, me ya sa ba zan iya bin ka a yanzu ba? Zan ba da raina a madadinka.”
38 Yesu ya amsa ya ce: “Za ka ba da ranka a madadina? A gaskiya ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara za ka yi mūsun sani na sau uku.”
Hasiya
^ A yaren Girka, “a ƙirjin.”