Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA ZA KA JI DAƊIN KARANTA LITTAFI MAI TSARKI

Ta Yaya Zan Soma Karatun?

Ta Yaya Zan Soma Karatun?

Mene ne za ka yi da zai sa ka ji daɗin karanta Littafi Mai Tsarki kuma ka amfana daga karatun? Ga abubuwa biyar da suka taimaki mutane da yawa.

Ka nemi wuri mai kyau. Ka nemi inda ba a surutu. Ka kawar da abubuwan da za su iya raba hankalinka. Ka nemi wurin da akwai haske da kuma iska mai daɗi, hakan zai sa ka amfana sosai daga karatun.

Ka kasance da ra’ayin da ya dace. Tun da Littafi Mai Tsarki daga wurin Ubanmu na sama ne, za ka amfana sosai idan ka kasance da hali irin na yaron da yake so ya koyi abubuwa daga wurin iyayensa. Ka kawar da duk wani ra’ayi marar kyau da kake da shi game da Littafi Mai Tsarki don Allah ya koyar da kai.Zabura 25:4.

Ka riƙa yin addu’a kafin ka soma karatun. Ba abin mamaki ba ne cewa muna bukatar taimakon Allah don mu fahimci Littafi Mai Tsarki, domin Kalmarsa ce. Allah ya yi alkawarin cewa zai ba da “ruhu mai-tsarki ga waɗanda suke roƙonsa.” (Luka 11:13) Ruhu mai tsarki zai taimaka maka ka fahimci Kalmar Allah. Da shigewar lokaci, zai sa ka iya fahimtar “zurfafan al’amuran Allah.”1 Korintiyawa 2:10, Littafi Mai Tsarki.

Ka karanta yadda za ka fahimta. Kada ka riƙa karantu kawai. Amma ka riƙa yin tunani a kan abin da kake karantawa. Ka tambayi kanka: ‘Waɗanne halaye ne mutumin da nake karantu a kansa yake da su? Ta yaya zan yi koyi da shi?’

Ka kafa maƙasudai. Idan kana so ka amfana daga karatun Littafi Mai Tsarki, kana bukatar ka koyi abin da zai iya kyautata rayuwarka. Za ka iya kafa maƙasudai kamar su: ‘Ina so in san Allah sosai.’ ‘Ina so in zama mutumin kirki ko miji ko kuma matar kirki.’ Bayan haka, sai ka nemi nassosin da za su taimaka maka ka cim ma su. *

Waɗannan shawarwari guda biyar za su iya taimaka maka ka soma karatun Littafi Mai Tsarki. Amma mene ne zai sa ka ji daɗin karatun sosai? Talifi na gaba zai ba ka wasu shawarwari.

^ sakin layi na 8 Idan ba ka san ayoyin Littafi Mai Tsarki da za su iya taimaka maka ba, Shaidun Jehobah za su yi farin cikin taimaka maka.