Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 7

Kana Daraja Rai Yadda Allah Yake Yi Kuwa?

Kana Daraja Rai Yadda Allah Yake Yi Kuwa?

“Allah wanda yake ba da rai ga dukan kome.”​—1 TIMOTI 6:13.

1, 2. Wane kyauta mai daraja ne Jehobah ya ba mu?

JEHOBAH ya ba wa kowannenmu wani kyauta. Kyautan shi ne rai. (Farawa 1:27) Yana so mu ji daɗin rayuwa sosai. Don haka, ya yi mana tanadin wasu ƙa’idodin da za su taimaka mana mu yanke shawarwarin da suka dace. Ya kamata mu yi amfani da ƙa’idodin don su taimaka mana mu “iya bambanta” tsakanin “nagarta da mugunta.” (Ibraniyawa 5:14) Idan muka yi hakan, muna barin Jehobah ya nuna mana yadda ya kamata mu riƙa yin abubuwa. Idan muna bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma muna ganin yadda suke taimaka mana, hakan zai sa mu daraja su sosai.

2 Sha’anin rayuwa yana da wuyar fahimta. Muna iya fuskantar wani yanayin da babu wata takamammen doka game da hakan a Littafi Mai Tsarki. Alal misali, a wasu lokuta muna bukatar mu yanke shawara game da magunguna ko jinyar da ta ƙunshi jini. Ta yaya za mu yanke shawarar da za ta faranta wa Jehobah rai? Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da ƙa’idodi da yawa da suke nuna mana yadda Jehobah yake ɗaukan rai da kuma jini. Idan muka fahimci waɗannan ƙa’idodin, za mu yanke shawara mai kyau kuma mu kasance da kwanciyar rai. (Karin Magana 2:​6-11) Bari mu tattauna wasu daga cikin ƙa’idodin nan.

YADDA ALLAH YAKE ƊAUKAN RAI DA KUMA JINI

3, 4. (a) Ta yaya Jehobah ya bayyana mana yadda yake ɗaukan jini? (b) Mene ne jini yake wakilta?

3 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa jini yana da tsarki sosai domin rai yana cikin jini. Jehobah yana ɗaukan rai da daraja sosai. Bayan Kayinu ya kashe ɗan’uwansa, Jehobah ya gaya masa cewa: “Muryar jinin ɗan’uwanka tana yi mini kuka daga ƙasa!” (Farawa 4:10) Jinin Habila na wakiltar ransa, kuma da Kayinu ya kashe shi, ya ɗauki ransa.

4 Bayan Ambaliyar Ruwan da aka yi a zamanin Nuhu, Allah ya gaya wa ’yan Adam cewa za su iya cin nama. Amma ya gaya musu cewa: “Kada ku ci nama tare da jinin.” (Farawa 9:4) Wannan dokar ba don ’ya’yan Nuhu kawai ba ne amma har da mu ma. Hakika a gun Jehobah, jini na wakiltar rai. Muna bukatar mu kasance da irin wannan ra’ayin.​—Zabura 36:9.

5, 6. Ta yaya Dokar da aka bayar ta hannun Musa ta nuna yadda Jehobah yake ɗaukan rai da jini?

5 A Dokar da Jehobah ya ba wa Musa, Jehobah ya ce: “Duk . . . wanda ya ci jini, ni Yahweh zan ɗaura fuskata wurin yin gāba da mutumin har sai na kawar da shi daga jama’a. Gama rai na kowace halitta yana cikin jininta ne.”​—Littafin Firistoci 17:​10, 11.

6 Dokar da aka bayar ta hannun Musa ta ce duk mutumin da ya yanka dabba, ya zubar da jininta a ƙasa. Yin hakan zai nuna cewa an mai da ran dabbar ga Mahaliccinta wato Jehobah. (Maimaitawar Shari’a 12:16; Ezekiyel 18:4) Jehobah bai bukaci Isra’ilawan su wanke jinin har sai sun tabbata cewa babu jini ko kaɗan a naman ba. Amma idan suka yi iya ƙoƙarinsu don su fitar da jinin, za su iya cin naman ba tare da zuciyarsu ta dame su ba. Idan suka daraja jinin dabbar, suna nuna cewa sun daraja Jehobah Mahaliccin rai. Ƙari ga haka, Dokar ta bukaci Isra’ilawa su miƙa hadayar dabba don zunubansu.​—Ka duba Ƙarin Bayani na 19 da 20.

7. Ta yaya Dauda ya daraja jini?

7 Abin da Dauda ya yi sa’ad da yake yaƙi da Filistiyawa ya nuna mana yadda jini yake da daraja. Sojojin Dauda sun lura cewa yana jin ƙishin ruwa. Sai suka sadaukar da rayukansu, suka je inda maƙiyansu suke don su ɗebo masa ruwa. Da suka kawo ruwan, Dauda ya ƙi sha kuma ya “juye shi a ƙasa kamar hadaya ga Yahweh.” Dauda ya ce: “Yahweh ya sawwaƙe mini in sha daga wannan ruwan! Ai zai zama mini kamar jinin waɗanda suka sadaukar da rayukansu ta wurin ɗiban ruwan” ne. Dauda ya san cewa rai da kuma jini suna da daraja sosai a gun Allah.​—2 Sama’ila 23:​15-17.

8, 9. Yaya Kiristoci a yau ya kamata su riƙa ɗaukan jini?

8 Bayan mutuwar Yesu, bayin Allah ba sa bukatar su miƙa hadayun dabbobi. Duk da haka, suna bukatar su riƙa daraja rai. Ɗaya daga cikin Dokar da Jehobah ya ba wa Kiristoci ita ce su ‘kiyaye kansu daga . . . jini.’ Kiyaye wannan dokar tana da muhimmanci kamar kiyaye dokar da aka bayar na guje wa lalata da kuma bautar gumaka.​—Ayyukan Manzanni 15:​28, 29.

Ta yaya zan bayyana shawarar da na yanke game da ƙananan sassan jini?

9 A yau ma, mu Kiristoci mun san cewa Jehobah shi ne Mahaliccin rai kuma dukan halittu nasa ne. Mun kuma san cewa jini yana da tsarki kuma yana wakiltar rai. Don haka, muna bukatar mu bincika ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kafin mu yanke wata shawara game da jinyar da ta ƙunshi ƙarin jini.

JINYAR DA TA ƘUNSHI ƘARIN JINI

10, 11. (a) Mene ne ra’ayin Shaidun Jehobah game da ƙarin jini ko kuma wasu ɓangarori huɗu na jini? (b) Wace shawara ce kowane Kirista zai yanke da kansa?

10 Shaidun Jehobah sun fahimci cewa ƙin shan jini ba shi ne kaɗai abin ake nufi da mu ‘kiyaye kanmu daga . . . jini’ ba. Ayar tana nufin kada mu sa jini a jikinmu a kowace hanya. Hakan ya ƙunshi ƙarin jini da kuma ajiye jininmu don a sake amfani da shi. Ƙari ga haka, ya ƙunshi ƙin amincewa da jajaye ko fararen ƙwayoyin halitta na jini da kamewar jini da kuma ruwan jini (red cells, white cells, platelets, and plasma).

11 A wasu lokuta, ana rarraba waɗannan ɓangarori huɗu na jini zuwa wasu ƙananan sashe na jini. Kowane Kirista ne yake da hakkin yanke shawarar ko zai karɓi waɗannan sassa na jini ko a’a. Ban da haka, kowane Kirista ne zai zaɓi yadda za a yi amfani da jininsa sa’ad da ake masa tiyata ko sa’ad da ake masa gwaje-gwaje ko sa’ad da ake masa wata jinya.​—Ka duba Ƙarin Bayani na 21.

12. (a) Me ya sa shawarwarin da muka yanke bisa ga tunanin zuciyarmu yake da muhimmanci a gun Jehobah? (b) Ta yaya za mu yanke shawarwari masu kyau game da wata jinya?

12 Shin Jehobah ya damu da shawarar da muka yanke da taimakon zuciyarmu? Ƙwarai kuwa. Jehobah ya damu da abin da muke tunaninsa da kuma abin da ke zuciyarmu. (Karanta Karin Magana 17:3; 24:12.) Don haka, idan muna so mu yanke shawara game da wata jinya, mu yi addu’a ga Jehobah kuma mu yi bincike game da jinyar. Bayan haka, sai mu yi amfani da tunanin zuciyarmu da muka horar wajen yanke shawarar. Kada mu tambayi mutane abin da za su yi idan suna cikin yanayinmu kuma kada mu bar mutane su gaya mana abin da za mu yi. Ya kamata kowane Kirista “ya ɗauki kayan kansa.”​—Galatiyawa 6:5; Romawa 14:12.

DOKOKIN JEHOBAH SUNA NUNA CEWA YANA ƘAUNAR MU

13. Mene ne dokokin Jehobah a kan jini suka koya mana game da shi?

13 Duk abin da Jehobah ya gaya mana mu yi zai amfane mu kuma yana nuna cewa yana ƙaunar mu. (Zabura 19:​7-11) Amma, muna masa biyayya ba don amfanin da muke samu kawai ba ne. Muna yin hakan don muna ƙaunarsa. Ƙaunarmu ga Jehobah ce take motsa mu mu ƙi amincewa da ƙarin jini. (Ayyukan Manzanni 15:20) Ban da haka, ƙin karɓan jini yana kāre mu daga wasu cututtuka. Mutane da yawa a yau sun san cewa ƙarin jini yana da haɗari sosai kuma likitoci da yawa sun gaskata cewa mara lafiyan zai fi amfana idan aka yi masa tiyata ba tare da ƙarin jini ba. Babu shakka, dokokin Jehobah sun nuna hikimarsa da kuma ƙaunar da yake mana.​—Karanta Ishaya 55:9; Yohanna 14:​21, 23.

14, 15. (a) Waɗanne dokoki ne Jehobah ya ba wa mutanensa don ya kāre su? (b) Ta yaya za mu bi ƙa’idodin waɗannan dokokin?

14 Tun daga farko, dokokin Jehobah suna amfanar mutanensa. Jehobah ya ba wa mutanensa Isra’ilawa dokoki don su kāre su daga jin raunuka masu tsanani. Alal misali, wata doka ta bukaci maigida ya gina ƙaramar katanga a gidan samansa don kada mutum ya faɗi. (Maimaitawar Shari’a 22:8) Ya kuma ba da wata doka game da dabbobi. Idan wani yana da bijimi mai taurin kai, hakkinsa ne ya riƙa kula da shi don kada ya ji ma wani rauni. (Fitowa 21:​28, 29) Duk Ba-isra’ilen da bai bi wannan dokar ba, za a kama shi da laifi idan wani abu ya faru.

15 Waɗannan dokokin suna nuna mana cewa Jehobah yana ɗaukan rai da daraja sosai. Me hakan ya koya mana? Ya kamata mu nuna cewa muna daraja rai ta yadda muke kula da gidajenmu da motocinmu da yadda muke tuƙi da kuma yadda muke wasannin motsa jiki. Wasu mutane musamman ma matasa suna ganin ba abin da zai faru da su. Don haka, suna yin abubuwan da suke da haɗari sosai. Amma ba haka Jehobah yake so mu riƙa yi ba. Yana so mu ɗauki ranmu da kuma na mutane da daraja sosai.​—Mai-Wa’azi 11:​9, 10.

16. Yaya Jehobah yake ji game da zubar da ciki?

16 Dukan ran ’yan Adam suna da daraja a gun Jehobah har da na jaririn da ba a haifa ba. A Dokar da aka ba da ta hannun Musa, idan mutum ya ji wa mata mai ciki rauni ba da gangan ba kuma matar ta mutu ko cikin ya zube, za a kama shi da laifin kisa. Ko da ya yi hakan ba da sanin sa ba, wajibi ne a biya rai a maimakon rai. (Karanta Fitowa 21:​22, 23.) A gun Allah, jaririn da ke ciki ma mutum ne. Don haka, yaya kake gani yake ji game da cikin da ake zubarwa? Yaya kake ganin yake ji sa’ad da ya ga miliyoyin jariran da ake kashewa kowace shekara?

17. Me zai taimaka wa macen da ta zubar da ciki a dā ta daina baƙin ciki?

17 Idan mace ta zubar da ciki kafin ta fara bauta ma Jehobah fa? Jehobah zai gafarta mata saboda fansar Yesu. (Luka 5:32; Afisawa 1:7) Bai kamata macen da ta yi irin wannan kuskuren a dā kuma ta tuba ta riƙa baƙin ciki ba. “Ubangiji mai jinƙai ne, mai ƙauna ne kuma, . . . Kamar yadda gabas take nesa da yamma, haka . . . ya nisantar da zunubanmu daga gare mu.”​—Zabura 103:​8-14, Littafi Mai Tsarki.

KA GUJI MUGUN TUNANI

18. Me ya sa bai kamata mu tsani mutane ba?

18 Daga zuciyarmu ne za mu soma daraja kyautar rai da Allah ya ba mu. Kuma hakan zai shafi yadda muke ɗaukan mutane. Manzo Yohanna ya ce, “Duk wanda yake ƙin ɗan’uwansa, shi mai kisan kai ne.” (1 Yohanna 3:15) Idan muka soma ƙin wani, kafin mu ankara, za mu tsani mutumin sosai. Idan muka tsani mutum, ba za mu daraja shi ba amma za mu riƙa masa sharri ko kuma mu so ya mutu. Jehobah ya san yadda muke ji game da mutane. (Littafin Firistoci 19:16; Maimaitawar Shari’a 19:​18-21; Matiyu 5:22) Idan muka lura cewa mun tsani wani, zai dace mu yi iya ƙoƙarinmu don mu daina wannan mugun tunanin.​—Yaƙub 1:​14, 15; 4:​1-3.

19. Me ra’ayin Jehobah game da faɗa zai taimaka mana mu yi?

19 Wata hanya kuma da za mu nuna cewa muna daraja rai ita ce wadda aka rubuta a littafin Zabura 11:5. A wurin, mun koyi cewa Jehobah “yakan ƙi mai son tā da hankali.” Idan muna kallon fina-finan da ake faɗa, hakan zai nuna cewa mu ma masu son faɗa ne. Don haka, maimakon mu riƙa tunanin abubuwan da za su jawo tashin hankali, ya kamata mu riƙa tunanin abubuwan da za su sa mu zauna lafiya da mutane.​—Karanta Filibiyawa 4:​8, 9.

KADA KA BI MUTANEN DA BA SA DARAJA RAI

20-22. (a) Ta yaya Jehobah yake ɗaukan mutane a duniyar Shaiɗan? (b) Ta yaya mutanen Allah za su nuna cewa su “ba na duniya ba ne”?

20 Mutane a duniyar Shaiɗan ba sa daraja rai kuma Jehobah yana ganin hakan a matsayin kisan kai. Shekaru da yawa yanzu, hukumomin siyasa sun sa mutane da yawa har ma da bayin Jehobah sun rasa rayukansu. A Littafi Mai Tsarki, an kwatanta hukumomi ko gwamnatocin da muguwar dabba. (Daniyel 8:​3, 4, 20-22; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 13:​1, 2, 7, 8) A yau, mutane suna samun kuɗi sosai ta wajen sayar da makamai. Hakika, “duniya duka tana a hannun mugun nan.”​—1 Yohanna 5:19.

21 Amma Kiristocin gaskiya a yau “ba na duniya ba ne.” Mutanen Jehobah ba sa saka hannu a siyasa ko kuma yaƙi. Ba sa kashe mutane. Don haka, ba sa haɗa kai da mutanen da suke kisa. (Yohanna 15:19; 17:16) Idan aka tsananta wa Kiristoci na gaskiya, ba sa ramawa. Yesu ya gaya mana cewa mu ƙaunaci maƙiyanmu.​—Matiyu 5:44; Romawa 12:​17-21.

22 Addini ma yana cikin abubuwan da suka jawo mutuwar miliyoyin mutane. Da Littafi Mai Tsarki yake magana game Babila Babba, wato ƙungiyar addinan ƙarya, ya ce: “A cikin Babila aka sami jinin annabawa da na tsarkaka, i, jinin dukan waɗanda aka kashe a duniya.” Shin ka fahimci dalilin da ya sa Jehobah ya ce mana: “Ku fito, ya mutanena, daga cikinta”? Mutanen Jehobah ba sa bin addinan ƙarya.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 17:6; 18:​2, 4, 24.

23. Mene ne ‘fita’ daga Babila Babba ya ƙunsa?

23 Don ‘mu fita’ daga Babila Babba, wajibi ne mu ware kanmu daga duk wani abu da yake da alaƙa da addinin ƙarya. Alal misali, wajibi ne mu gaya musu cewa su cire sunanmu daga sunayen mambobinsu. Ban da haka, muna bukatar mu ƙi duk abubuwa marasa kyau da addinan ƙarya suke yi. Addinan ƙarya suna ɗaukaka yin lalata da siyasa da kuma haɗama. (Karanta Zabura 97:10; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 18:​7, 9, 11-17) Kuma hakan ya sa miliyoyin mutane sun rasa rayukansu a ’yan shekarun nan.

24, 25. Ta yaya sanin Jehobah zai sa mu kasance da kwanciyar hankali da zuciya mai kyau?

24 Kafin mu soma bauta ma Jehobah, wataƙila mun yi waɗannan mugayen abubuwa da mutanen duniya suke yi. Amma yanzu mun canja. Mun gaskata da fansar Yesu kuma mun yi alkawarin bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu. Hakan ya sa ‘Ubangiji ya sabunta zuciyarmu.’ Yanzu muna da kwanciyar hankali da zuciya mai tsabta domin mun san cewa muna faranta wa Allah rai.​—Ayyukan Manzanni 3:19; Ishaya 1:18.

25 Ko da a dā muna cikin ƙungiyoyin da ba sa daraja rai, Jehobah zai gafarta mana domin fansar Yesu. Muna yi wa Jehobah matuƙar godiya don rai da ya ba mu kyauta. Kuma za mu iya nuna hakan ta wajen taimaka wa mutane su san Jehobah, su ware kansu daga duniyar Shaiɗan kuma su kasance da dangantaka mai kyau da Allah.​—2 Korintiyawa 6:​1, 2.

KA GAYA WA MUTANE GAME DA MULKIN ALLAH

26-28. (a) Wane aiki mai muhimmanci ne Jehobah ya ba wa Ezekiyel? (b) Wane aiki ne Jehobah ya ba mu a yau?

26 A zamanin dā, Jehobah ya gaya wa annabi Ezekiyel ya gargaɗi mutanensa cewa za a halaka Urushalima kuma ya gaya musu yadda za su iya tsira. Idan Ezekiyel bai gargaɗi mutanen ba, alhakinsu zai zama a kansa. (Ezekiyel 33:​7-9) Ezekiyel ya nuna cewa yana daraja rai ta wajen gaya wa mutane wannan saƙo mai muhimmanci.

27 Jehobah ya ba mu aikin gargaɗar da mutane cewa za a halaka duniyar nan ba da daɗewa ba, kuma ya ce mu taimaka musu su bauta masa don su tsira. (Ishaya 61:2; Matiyu 24:14) Muna so mu yi iya ƙoƙarinmu wajen gaya wa mutane wannan saƙon. Muna so mu zama kamar Bulus da ya ce: “Ba alhakin jini ko na ɗayanku a kaina, domin na sanar muku da nufin Allah duka.”​—Ayyukan Manzanni 20:​26, 27.

28 Akwai wasu abubuwan da muke bukatar mu yi don mu kasance da tsabta. Bari mu bincika hakan a babi na gaba.