Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 BABI NA 17

Ka Ci Gaba da Kaunar Allah

Ka Ci Gaba da Kaunar Allah

“Ku yi ta gina kanku a kan bangaskiyarkun nan mafi tsarki . . . Ku kiyaye kanku cikin ƙaunar Allah.”​—YAHUDA 20, 21.

1, 2. Mene ne za mu yi don mu ci gaba da ƙaunar Allah?

DUKANMU muna so mu kasance da ƙarfi da kuma ƙoshin lafiya. Shi ya sa mukan ci abinci mai gina jiki kuma muna motsa jiki da kula da jikinmu. Ko da yake yin hakan bai da sauƙi, ba ma dainawa. Amma akwai wata hanya kuma da muke bukatar mu kasance da ƙarfi da kuma ƙoshin lafiya.

2 Matakin da muka ɗauka na yin nazarin Littafi Mai Tsarki yana da kyau sosai, amma muna bukatar mu ci gaba da ƙarfafa dangantakarmu da Allah. Yahuda ya ba wa Kiristoci shawara cewa: “Ku kiyaye kanku cikin ƙaunar Allah.” Ya gaya musu yadda za su yi hakan. Ya ce: “Ku yi ta gina kanku a kan bangaskiyarkun nan mafi tsarki.” (Yahuda 20, 21) To, ta yaya za mu sa bangaskiyarmu ta yi ƙarfi?

KA CI GABA DA ƘARFAFA BANGASKIYARKA

3-5. (a) Wane ra’ayi ne Shaiɗan yake so ka kasance da shi game da irin halayen da Jehobah yake so? (b) Yaya kake ji game da dokoki da kuma ƙa’idodin Jehobah?

3 Yana da muhimmanci ka gaskata cewa ƙa’idodin Jehobah ne suka fi amfani. Shaiɗan yana so ka gaskata cewa zai yi maka wuya ka yi irin rayuwar da Jehobah  yake so ka yi, kuma za ka fi farin ciki idan kana yin abin da ka ga dama. Tun daga zamanin Adamu da Hauwa’u ne Shaiɗan yake ƙoƙarin sa mutane su gaskata da hakan. (Farawa 3:​1-6) Kuma har yanzu bai daina ba.

4 Shin abin da Shaiɗan ya faɗa gaskiya ne? Yana da wuya mu kasance da halayen da Jehobah yake so? A’a. Alal misali, a ce kana zagayawa a wani wurin shakatawa mai kyau. Sai ka ga an kewaye wani ɓangaren wurin da katanga. Za ka iya cewa, ‘Me ya sa aka kewaye ɓangaren nan da katanga?’ Ba da daɗewa ba sai ka ji kukar zaki a bayan katangar. Za ka yi murna cewa an saka katangar, ko ba haka ba? In ba don katangar ba, da zakin ya cinye ka. Ƙa’idodin Jehobah suna kama da wannan katangar, Shaiɗan kuma yana kama da zakin. Shi ya sa Kalmar Allah ta gargaɗe mu cewa: “Ku kame kanku, ku zauna da shiri. Ga shi abokin gābanku Shaiɗan yana yawo yana ruri kamar zaki mai jin yunwa, yana neman wanda zai cinye.”​—1 Bitrus 5:8.

5 Jehobah yana so mu ji daɗin rayuwa sosai. Ba ya so mu bar Shaiɗan ya yaudare mu. Shi ya sa ya ba mu dokoki da kuma ƙa’idodi don su kāre mu kuma su sa mu farin ciki. (Afisawa 6:11) Manzo Yaƙub ya ce: “Mutumin da ya mai da hankalinsa wajen bincike cikakkiyar koyarwar nan . . . za a sa masa albarka cikin dukan abin da yake yi.”​—Yaƙub 1:25.

6. Me zai sa mu kasance da tabbaci cewa umurnan Jehobah ne suka fi amfani?

6 Idan muka bi umurnin Jehobah, za mu amfana kuma dangantakarmu da shi za ta ƙara ƙarfi. Alal misali, muna amfana sosai sa’ad da muka yi addu’a kamar yadda ya ce mu riƙa yi. (Matiyu 6:​5-8; 1 Tasalonikawa 5:17)  Muna farin ciki sosai in muka bi umurnin da ya ba mu cewa mu riƙa halarta taro da ƙarfafa juna da kuma yin wa’azi. (Matiyu 28:​19, 20; Galatiyawa 6:2; Ibraniyawa 10:​24, 25) Idan muna tunani a kan yadda abubuwan nan suke sa bangaskiyarmu ta yi ƙarfi, za mu kasance da tabbaci cewa umurnan Jehobah suna da amfani sosai.

7, 8. Me zai taimaka mana mu daina damuwa game da jarraba da za mu iya fuskanta a nan gaba?

7 Muna iya damuwa cewa a nan gaba za mu fuskanci jarraba da za ta yi mana wuya mu jimre. Idan ka taɓa tunanin hakan, ka tuna da abin da Jehobah ya ce: “Ni ne Yahweh Allahnku, wanda ya koya muku domin amfanin kanku, wanda ya nuna muku hanyar da za ku bi. Ayya! Da a ce kun yi biyayya da umarnaina, da salamarku za ta kasance kamar ruwan rafi, . . . adalcinku kuma za ta yi ta ɓullowa kamar raƙuman ruwan teku.”​—Ishaya 48:​17, 18.

8 Idan muka yi wa Jehobah biyayya, salamarmu za ta zama kamar ruwan rafi da ke gudu ba tsayawa. Kuma  kamar yadda raƙuman teku ke wanke bakin teku ba fasawa, haka adalcinmu za ta kasance. Za mu iya riƙe amincinmu ko da me ya faru da mu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Danƙa wa Yahweh damuwarka, shi kuwa zai lura da kai, ko kaɗan ba zai bar masu adalci su jijjigu ba.”​—Zabura 55:22.

‘KU ZAMA MASU CIKAKKEN GANEWA’

9, 10. Mene ne zama mai cikakken ganewa yake nufi?

9 Idan ka ci gaba da ƙarfafa dangantakarka da Jehobah, za ka ‘zama mai cikakken ganewa.’ (Ibraniyawa 6:1) Mene ne ake nufi da zama mai cikakken ganewa?

10 Ba yawan shekaru ne yake sa mutum ya kasance da cikakken ganewa ba. Maimakon haka, sai ya kusaci Jehobah sosai kuma ya kasance da ra’ayinsa. (Yohanna 4:23) Manzo Bulus ya ce: “Masu rayuwar halin mutuntaka sukan mai da hankalinsu ga sha’anin jiki ne, amma masu rayuwar Ruhu sukan mai da hankalinsu ga abin da Ruhu yake so ne.” (Romawa 8:5) Wanda yake da cikakken ganewa ba ya mai da hankali ga sha’awar jiki ko kuma abin duniya. Amma yana mai da hankali ga bauta wa Jehobah da kuma yanke shawarwarin da suka dace. (Karin Magana 27:11; karanta Yaƙub 1:​2, 3.) Ba ya barin abubuwa marasa kyau su rinjaye shi. Wanda yake da cikakken ganewa ya san abin da yake da kyau kuma yana ƙoƙarin aikata shi.

11, 12. (a) Mene ne Bulus ya ce game da ‘hankalinmu’? (b) Ta yaya zama mai cikakken ganewa yake kama da ɗan kwallon da ya ƙware?

11 Muna bukatar mu saka ƙwazo sosai kafin mu zama masu cikakken ganewa ko kuma Kiristocin da suka manyanta. Manzo Bulus ya ce: “Abinci mai tauri, ai, na  manya ne, wato waɗanda hankalinsu ya horu yau da kullum, su rarrabe nagarta da mugunta.” (Ibraniyawa 5:​14, Littafi Mai Tsarki) Kalmar nan “horu” za ta sa mu tuna da yadda ake horar da ’yan wasan kwallo.

12 Idan muka ga wanda ya iya wasan kwallo, mun san cewa ya yi amfani da lokaci sosai wajen horar da kansa kafin ya iya buga kwallon. Ba haifar sa aka yi haka ba. Domin idan aka haifi yaro, bai san yadda zai yi amfani da hannayensa da kuma ƙafafunsa ba. Amma da shigewar lokaci, zai koyi yadda zai riƙe abubuwa da kuma yin tafiya. Idan ya ci gaba da horar da kansa, zai zama ɗan kwallo da ya ƙware sosai. Haka ma, muna bukatar mu horar da kanmu kafin mu zama Kiristoci masu cikakken ganewa.

13. Mene ne zai taimaka mana mu ɗauki abubuwa yadda Jehobah yake ɗaukan su?

13 Wannan littafin ya koya mana yadda za mu riƙa ɗaukan abubuwa yadda Jehobah yake ɗaukansu. Mun koyi yadda za mu ƙaunaci ƙa’idodin Jehobah. Idan muna so mu yanke wata shawara, mu tambayi kanmu: ‘Wace doka ce aka ba da game da hakan ko kuma wace ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ce ta dace da yanayin? Ta yaya zan bi dokar ko ƙa’idar? Mene ne Jehobah yake so na yi?’​—Karanta Karin Magana 3:​5, 6; Yaƙub 1:5.

14. Mene ne za mu yi don mu ƙarfafa bangaskiyarmu?

14 Kada mu daina ƙarfafa bangaskiyarmu. Kamar yadda cin abinci mai kyau yake taimaka mana mu kasance da ƙoshin lafiya, haka ma koyan abubuwa game da Jehobah yake taimaka mana mu ƙarfafa bangaskiyarmu. A lokacin da muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki, mun koyi wasu abubuwa masu muhimmanci  game da Jehobah da kuma umurnansa. Amma da shigewar lokaci, muna bukatar mu ci gaba da ƙara koyan abubuwa game da Jehobah. Shi ya sa manzo Bulus ya ce: “Abinci mai kauri shi ne na waɗanda suka yi girma.” Idan muna amfani da abubuwan da muke koya, za mu kasance da hikima. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Muhimmin abu shi ne samun hikima.”​—Karin Magana 4:​5-7; 1 Bitrus 2:2.

15. Me ya sa yake da muhimmanci mu ƙaunaci Jehobah da kuma ’yan’uwanmu sosai?

15 Wanda yake da ƙoshin lafiya ya san cewa yana bukatar ya kula da kansa don ya ci gaba da kasancewa da ƙoshin lafiya. Haka ma, wanda yake ƙaunar Jehobah ya san cewa yana bukatar ya ci gaba da ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah. Bulus ya gaya mana cewa: “Ku gwada kanku domin ku sani ko kuna bin Yesu Almasihu cikin aminci. Ku dinga auna kanku.” (2 Korintiyawa 13:5) Amma ba ƙarfafa bangaskiyarmu kawai muke bukatar mu riƙa yi ba. Dole ne ƙaunarmu ga Jehobah da kuma ’yan’uwanmu ta ci gaba da ƙarfi. Bulus ya ce: “Ko da ina . . . da dukan ilimi, ko da kuma ina da bangaskiya sosai, har yadda zan iya kawar da duwatsu, amma in dai ba ni da ƙauna, to, ni ba kome ba ne.”​—1 Korintiyawa 13:​1-3.

KA RIƘA TUNAWA DA BEGENKA

16. Yaya Shaiɗan yake so mu riƙa ji?

16 Shaiɗan yana so mu gaskata cewa ba za mu iya faranta wa Jehobah rai ba. Yana so mu yi sanyin gwiwa cewa babu abin da zai iya magance matsalar da muke fuskanta. Ba ya so mu amince da ’yan’uwanmu Kiristoci kuma ba ya so mu yi farin ciki. (Afisawa 2:2) Shaiɗan ya san cewa tunani mara kyau zai iya mana lahani  kuma zai ɓata dangantakarmu da Allah. Amma Jehobah ya ba mu wani abu da zai iya taimaka mana mu guji yin tunani mara kyau, wato bege.

17. Me ya sa bege yake da muhimmanci?

17 A 1 Tasalonikawa 5:​8, Littafi Mai Tsarki ya kwatanta begenmu da hular kwano da soja yake sakawa don ya kāre kansa lokacin yaƙi. Littafi Mai Tsarki ya kira wannan hular kwanon “sa zuciya ga samun ceto.” Idan muka yi bege ko sa zuciya ga alkawuran da Jehobah ya yi, hakan zai kāre mu daga yin tunani mara kyau.

18, 19. Ta yaya begen da Yesu yake da shi ya ƙarfafa shi?

18 Begen da Yesu yake da shi ya ƙarfafa shi sosai. A dare na ƙarshe kafin a kashe Yesu, ya fuskanci matsaloli. Ɗaya daga cikin aminansa ya ci amanarsa. Wani kuma ya yi mūsun saninsa. Sauran kuma sun gudu sun bar shi. Mutanen ƙasarsa sun kama shi kuma suka ce a kashe shi. Me ya taimaka wa Yesu ya jimre abubuwan nan?  “Saboda farin cikin da aka sa a gabansa, ya jimre wa [“gungumen azaba,” NW ] ya mai da abin kunya ba kome ba, a yanzu kuma yana zaune a hannun daman kujerar mulkin Allah.”​—Ibraniyawa 12:2.

19 Yesu ya san cewa idan ya riƙe amincinsa, hakan zai ɗaukaka Ubansa kuma zai nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. Begen da yake da shi ya sa shi farin ciki sosai. Ƙari ga haka, ya san cewa nan ba da daɗewa ba, zai koma sama kuma ya sake kasancewa tare da Ubansa. Wannan begen ya taimaka masa ya jimre. Kamar Yesu, mu ma ya kamata mu riƙa tunani a kan begen da muke da shi. Yin hakan zai taimaka mana mu jimre duk wata matsalar da za mu fuskanta.

20. Me zai taimaka maka ka mai da hankali ga abin da ya dace?

20 Jehobah yana ganin bangaskiyarka da kuma ƙoƙarin da kake yi. (Ishaya 30:18; karanta Malakai 3:10.) Ya yi alkawari cewa zai “biya bukatar zuciyarka.” (Zabura  37:4) Don haka, ka riƙa tunani a kan abubuwan da kake sa rai a kai. Shaiɗan yana so ka daina kasancewa da bege kuma ka ɗauka cewa Jehobah ba zai cika alkawuransa ba. Amma kada ka bar tunani mara kyau ya rinjaye ka! Idan ka lura cewa ba ka gaskatawa da alkawuran Allah kamar dā, ka roƙi Jehobah ya taimaka maka. Ka tuna da abin da ke littafin Filibiyawa 4:​6, 7: “Kada ku damu da kome, sai dai a cikin kome ku faɗa wa Allah bukatunku ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. Ta haka kuwa Allah zai ba ku salama iri wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam, za ta kuma tsare zukatanku da tunaninku cikin Almasihu Yesu.”

21, 22. (a) Wane alkawari ne Jehobah ya yi wa mutane game da nan gaba? (b) Me ka kuɗiri aniyar yi?

21 Ka riƙa neman lokaci don ka yi tunani a kan abubuwa masu kyau da za su faru a nan gaba. Nan ba da daɗewa ba, dukan mutane za su bauta wa Jehobah. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:​9, 14) Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance a sabuwar duniya. Rayuwar za ta yi daɗi sosai! Za a halaka Shaiɗan da kuma aljanunsa. Ba za ka yi rashin lafiya ko kuma ka mutu ba. Maimakon haka, a kowace rana za ka tashi da ƙoshin lafiya kuma ka yi farin ciki. Mutane a lokacin za su yi aiki tare don su mai da duniya aljanna. Za a kasance da abinci mai kyau da kuma wuraren kwana masu kyau. Babu mugayen mutane sai dai mutanen kirki. Da shigewar lokaci, dukan mutane a duniya za su more “ ’yancin nan na ɗaukakar da za a yi wa ’ya’yan Allah.”​—Romawa 8:21.

22 Jehobah yana so ka zama amininsa. Don haka, ka yi ƙoƙari don ka riƙa yi wa Jehobah biyayya kuma ka kusace shi kowace rana. Bari dukanmu mu ci gaba da ƙaunar Allah har abada abadin!​—Yahuda 21.