Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Wasika Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu

Wasika Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu

Saƙo ga masu ƙaunar Jehobah da Kalmarsa:

Yesu ya ce: “Za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ba ku ’yanci.” (Yohanna 8:32) Ka yi tunanin irin farin cikin da ka yi sa’ad da ka fara sanin gaskiyar Littafi Mai Tsarki! Ka ji daɗin sanin cewa ko da yake ana yawan ƙarya a duniya, zai yiwu mu san gaskiyar Kalmar Allah.​​—⁠2 Timoti 3:⁠1.

Jehobah yana so mu san gaskiya. Kuma da yake muna ƙaunar mutane, muna so mu gaya musu gaskiyar Kalmar Allah. Amma bautar Allah ta wuci hakan. Don haka, dole ne mu yi iya ƙoƙarinmu mu riƙa rayuwa irin ta Kirista domin muna daraja ƙa’idodin Jehobah. Yesu ya gaya mana hanya mai muhimmanci da za mu nuna cewa muna ƙaunar Allah. Ya ce: “Na bi umarnan Ubana, na kuma zauna a cikin ƙaunarsa. Haka ku kuma, in kun bi umarnaina za ku zauna a cikin ƙaunata.”​​—⁠Yohanna 15:⁠10.

Yesu yana ƙaunar Ubansa sosai kuma ya yi duk wani abin da Ubansa ya gaya masa ya yi. Idan muka yi rayuwa irin ta Yesu, Jehobah zai ƙaunace mu kuma za mu kasance da kwanciyar hankali. Kamar yadda Yesu ya ce, “yanzu da kun san waɗannan abubuwa za ku zama masu albarka idan kun yi su.”​​—⁠Yohanna 13:⁠17.

Mun tabbata cewa littafin nan zai taimaka maka ka bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don ka zama aminin Allah. Fatanmu shi ne, za ka ƙaunaci Allah kuma ka ci gaba da ‘ƙaunarsa’ don ka sami “rai na har abada.”​​—⁠Yahuda 21.

Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah