Ku Ci Gaba da Kaunar Allah

Littafi Mai Tsarki yana dauke da ka’idodi kuma yana koyar da halayen da za su taimaka mana mu ci gaba da kaunar Allah.

Wasika Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu

Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah tana karfafa duk masu kaunar Jehobah su san yadda za su yi rayuwa bisa Kalmarsa Littafi Mai Tsarki.

BABI NA 1

Kaunar da Ke Tsakaninmu da Allah Za Ta Kasance Har Abada

Muna bukatar kokari sosai don abotarmu da Allah ta yi karfi. Ta yaya za mu yi nasara a yin hakan?

BABI NA 2

Mu Bauta wa Allah da Zuciya Mai Tsabta

Allah ya ba kowannenmu zuciya don ta taimaka mana mu yi rayuwa mai kyau.

BABI NA 3

Ka Yi Abokantaka da Masu Kaunar Allah

Abokanmu za su iya sa mu mu yi abu mai kyau ko mara kyau. Ta yaya ka’idodin Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana sa’ad da muke zaban abokai?

BABI NA 4

Me Ya Sa Ya Dace Mu Rika Yin Biyayya?

Akwai dalilai masu kyau da suka sa ya dace mu yi biyayya a cikin iyali da ikilisiya da kuma yankinmu.

BABI NA 5

Yadda Za Mu Ki Saka Hannu A Harkokin Duniya

Yesu ya gaya wa almajiransa cewa, “Ku ba na duniya ba ne.” Me kalmar nan “duniya,” take nufi kuma me ya sa Kiristoci za su ki saka hannu a harkokin duniya?

BABI NA 6

Yadda Za Mu Zabi Nishadin da Ya Dace

Nishadin da mutane suke yi a duniyar nan yana kama da ’ya’yan itace da wani bangarensa yake da kyau, daya kuma ba shi da kyau. Mene ne zai taimaka maka ka zabi nishadin da ya dace?

BABI NA 7

Kana Daraja Rai Yadda Allah Yake Yi Kuwa?

Wane ka’idodin Littafi Mai Tsarki ne suka taimaka mana mu yanke shawara mai kyau game da jini?

BABI NA 8

Jehobah Yana So Bayinsa Su Kasance da Tsabta

Ba jikinmu da tufafinmu da kuma kewayenmu ne kawai Allah yake so mu tsabtace ba. Har da ibadarmu da halinmu da kuma tunaninmu.

BABI NA 9

“Ku Guje Wa Halin Lalata!”

Mutane da yawa ba sa bin dokar Allah game da jima’i. Mece ce lalata kuma ta yaya za mu guje ma wannan halin?

BABI NA 10

Aure Kyauta Ne Daga Allah

Wadanne albarka ne aure yake kawowa? Ta yaya za ka zabi mata ko mijin kirki? Me zai taimaka wa ma’aurata su ci gaba da jin dadin aurensu?

BABI NA 11

Zaman Aure

Kowace iyali tana da nata matsalolin. Duk da haka, ma’aurata da suke da matsaloli masu tsanani ma za su iya karfafa aurensu.

BABI NA 12

Ku Rika Yin Maganganu Masu Dadin Ji

Kalmomi za su iya karfafa mutane ko kuma su yi musu lahani. Jehobah yana koya mana yadda za mu yi magana yadda ya dace.

BABI NA 13

Dukan Bukukuwa Ne Allah Yake So?

Mutane suna jin dadin yin bukukuwa sosai. Me zai taimaka mana mu san ko Allah yana jin dadin bukukuwan?

BABI NA 14

Ku Zama Masu Gaskiya a Kowane Abu

Ka lura da yanayi 4 da za su iya sa yin gaskiya ya yi mana wuya da kuma albarka da za mu samu idan muka yi gaskiya.

BABI NA 15

Ka Ji Dadin Aikin da Kake Yi

Mahaliccinmu yana so mu ji dadin abin da muke yi. To, me zai taimaka mana mu ji dadin aikinmu? Akwai irin aikin da bai kamata Kiristoci su yi ba?

BABI NA 16

Kada Ka Ba Shaidan Dama

Muna rayuwa a duniyar da Shaidan yake iko da ita. Ta yaya za mu kusaci Jehobah kuma mu tsare kanmu daga Shaidan?

BABI NA 17

Ka Ci Gaba da Kaunar Allah

Wani marubucin Littafi Mai Tsarki ya shawarci Kiristoci cewa: “Ku yi ta gina kanku a kan bangaskiyarku nan mafi tsarki.” Ta yaya za ka yi hakan?

Karin Bayani

Ma’anar kalmomi da kuma furuci da ke littafin nan Ku Ci Gaba da Kaunar Allah.