Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Sun Daina Bin Addinin Karya

Sun Daina Bin Addinin Karya

“Ku fito daga cikinta, ya al’ummata.”​—R. YOH. 18:4.

WAƘOƘI: 10193

1. Ta yaya muka san cewa mutanen Allah za su daina zaman bauta a Babila Babba, kuma waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

A TALIFIN da ya shige, mun koyi yadda Kiristoci suka yi zaman bauta a Babila Babba. Abin farin ciki shi ne, ba za su ci gaba da yin haka har abada ba. Mun san da hakan domin a cikin Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya umurci bayinsa cewa, “Ku fito daga cikinta, ya al’ummata,” wato daga cikin Babila Babba. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 18:⁠4.) Muna mamarin sanin lokacin da mutanen Allah suka daina bin addinin ƙarya gabaki ɗaya! Amma kafin wannan, muna bukatar mu san amsoshin waɗannan tambayoyin: Wane mataki ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka ɗauka game da Babila Babba kafin shekara ta 1914? Shin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun kasance da ƙwazo a wa’azi a lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya? Sa’ad da suke bukatar su yi wasu canje-canje, shin hakan yana nufin cewa a lokacin suna bin addinin ƙarya ne?

FAƊUWAR BABILA

2. Wane mataki ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka ɗauka kafin Yaƙin Duniya na Ɗaya?

2 Shekaru da yawa kafin Yaƙin Duniya na Ɗaya, Charles  Taze Russell da kuma wasu abokansa sun gano cewa ‘yan Kiristandem ba sa koyar da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Don haka, sai suka ɗauki matakin ƙin yin tarayya da su. A watan Nuwamba, a shekara ta 1879, Zion’s Watch Tower (Hasumiyar Tsaro) ta ambata cewa: “Muna ɗaukan duk cocin da suke da’awa cewa suna bin Kristi amma kuma suna goyan bayan gwamnati a matsayin Babila Babba, wadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta da karuwa.”​—⁠Karanta Ru’ya ta Yohanna 17:​1, 2.

3. Mene ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka yi don su nuna cewa ba sa so su ci gaba da yin tarayya da addinin ƙarya? (Ka duba hoton da ke shafi na 26.)

3 Mutanen Allah masu aminci sun san cewa idan suna so Allah ya albarkace su wajibi ne su daina tarayya da addinin ƙarya. Don haka, yawancinsu sun rubuta wasiƙa zuwa ga cocinsu cewa ba za su ci gaba da zama membansu kuma ba. A wasu wurare, suna karanta wasiƙar da suka rubuta sa’ad da ake wani taro a cocin. A inda ba a amince da hakan ba, ‘yan’uwan sukan tura wasiƙa ga kowane memban cocin cewa ba sa son su yi tarayya da addinin ƙarya ko kaɗan! Akwai lokacin da yin hakan zai iya sa a kashe su. Amma daga shekara ta 1870, sai gwamnatoci a ƙasashe da yawa suka daina goyan bayan coci kamar yadda suke yi a dā. Hakan ya sa mutane za su iya tattauna Kalmar Allah kuma su ƙi gaskata da wasu koyarwar coci ba tare da jin tsoro ba.

4. A lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya, yaya mutanen Allah suke ɗaukan Babila Babba?

4 Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun fahimci cewa suna bukatar su gaya wa duniya gabaki ɗaya game da matakin da suka ɗauka ba kawai su gaya wa ‘yan’uwansu ko abokansu ko kuma membobin cocinsu ba. Suna son duniya ta san cewa Babila Babba karuwa ce! Shi ya sa daga watan Disamba ta shekara ta 1917 har zuwa farkon shekara ta 1918, Ɗaliban sun yi aiki tuƙuru don su rarraba wata warƙa mai jigo “The Fall of Babylon” wato Faɗuwar Babila guda miliyan goma. Wannan warƙar ta bayyana kome game da Kiristendam. Hakan ya sa limaman coci fushi sosai amma Ɗaliban ba su daina ba. Sun riga sun ƙudura niyya cewa wajibi ne su yi “wa Allah biyayya fiye da mutum.” (A. M. 5:​29, Littafi Mai Tsarki) Mene ne hakan ya nuna mana? Ya nuna cewa waɗannan Kiristocin ba su ci gaba da bin addinin ƙarya ba amma sun janye kansu daga ita kuma suna taimaka wa wasu ma su yi hakan.

SUN YI WA’AZI DA ƘWAZO A LOKACIN YAƘIN DUNIYA NA ƊAYA

5. Mene ne ya nuna cewa ‘yan’uwa sun yi wa’azi da ƙwazo a lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya?

5 Shekarun da suka shige, mun ɗauka cewa Jehobah ya yi fushi da mutanensa don ba su yi wa’azi da ƙwazo a lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya ba. Wannan dalilin ne ya sa muka ce Jehobah ya ƙyale su su yi zaman bauta a Babila Babba na ɗan karamin lokaci. Amma mutanen Allah da suka yi rayuwa a tsakanin shekara ta 1914 da kuma 1918 sun bayyana cewa dukansu sun yi iya ƙoƙarinsu don su ci gaba da yin wa’azi. Muna da ƙwaƙƙwaran dalilin da ya sa muka gaskata da hakan. Fahimtar ainihin abin da ya faru da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki a lokacin ya taimaka mana mu fahimci wasu abubuwan da suka faru da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki.

6, 7. (a) Wane ƙalubale ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka fuskanta a lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya? (b) Ka ba da misalan da suka nuna cewa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun kasance da ƙwazo a lokacin.

 6 Gaskiyar ita ce, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da suka yi rayuwa a lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya, wato daga shekara ta 1914 zuwa 1918 sun yi wa’azi da ƙwazo sosai. Amma don wasu dalilai, yin hakan bai yi musu sauƙi ba. Bari mu yi la’akari da dalilai guda biyu. Na farko, ainihin aikin da suka yi a lokacin shi ne rarraba littattafai. Sa’ad da gwamnati ta hana rarraba littafin nan The Finished Mystery a shekara ta 1918, hakan ya sa ya yi wa ‘yan’uwa wuya su yi wa’azi. Ba su iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki kaɗai don yin wa’azi ba sai dai da littafin nan The Finished Mystery. Na biyu shi ne sa’ad da cutar da ake kiran Spanish Flu ta ɓarke a shekara ta 1918. Wannan cuta ce da take yaɗuwa sosai kuma hakan ya hana ‘yan’uwa yin tafiye-tafiye da kuma yin wa’azi. Amma duk da haka, waɗannan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi iya ƙoƙarinsu don su yi wa’azi.

Waɗannan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun kasance da ƙwazo! (Ka duba sakin layi na 6, 7)

7 A shekara ta 1914, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun nuna wa mutane fiye da miliyan tara bidiyon nan “Photo-Drama of Creation.” Wannan fim ɗin majigi ne mai ɗauke da hotuna da kuma sauti da ya nuna tarihin ‘yan Adam tun daga lokacin halitta har zuwa ƙarshen sarauta Yesu na shekara dubu. Wannan fim ɗin gagarumin abu ne da aka cim ma a lokacin. Alal misali, mutanen da suka kalli wannan fim ɗin a shekara ta 1914 sun fi dukan Shaidun Jehobah da ke duniya a yau yawa! Wasu rahotanni sun kara nuna cewa a shekara ta 1916, mutane guda 809,393 ne suka halarci taro a Amirka, kuma a shekara ta 1918, lambar ta ƙaru zuwa 949,444. Hakika, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun sa ƙwazo sosai a yin wa’azi!

8. Ta yaya aka taimaka wa ‘yan’uwa su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah a lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya?

8 A lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya, ‘yan’uwan da suke yin ja-gora sun yi iya ƙoƙarinsu don su yi wa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da suke wurare dabam-dabam tanadin abin da zai riƙa ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah. Wannan tanadin ya ƙarfafa ‘yan’uwan kuma ya ba su ƙarfin gwiwa don su ci gaba da  yin wa’azi. Ɗan’uwa Richard H. Barber, wanda ya yi wa’azi da ƙwazo a lokacin ya ce: “Mun yi nasaran tura wasu masu kula masu ziyara zuwa ikilisiyoyi kuma muna tabbatawa cewa an rarraba Hasumiyar Tsaro da kuma tura mujallar zuwa Kanada inda aka hana mu rarraba ta. Na samu gatar tura wa wasu abokaina ƙaramin littafin nan The Finished Mystery don an ƙwace nasu. Ɗan’uwa Rutherford ya ce mana mu shirya babban taro a birane da yawa da suke yammacin Amirka kuma mu tura ‘yan’uwan da za su ba da jawaban da za su ƙarfafa ‘yan’uwa sosai.”

ANA BUKATAR A YI WASU CANJE-CANJE

9. (a) Me ya sa mutanen Allah suke bukatar a yi musu gyara a shekara ta 1914 zuwa 1919? (b) Duk da hakan wane tunani ne bai kamata mu yi ba?

9 Ba dukan abubuwan da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka yi a shekara ta 1914 zuwa 1919 ne suka jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba. Ko da yake su masu tawali’u ne, ‘yan’uwan ba su fahimci abin da Jehobah yake nufi sa’ad da ya gaya musu cewa su riƙa yin biyayya ga masu mulki ba. (Rom. 13:⁠1) Shi ya sa suka saka hannu a yaƙin da aka yi da kuma siyasa a lokacin. Alal misali, sa’ad da shugaban ƙasar Amirka ya ce a yi addu’ar zaman lafiya a ranar 30 ga watan Mayu na shekara ta 1918, Hasumiyar Tsaro ta ƙarfafa ‘yan’uwa cewa su ma su yi hakan. Wasu ‘yan’uwa ma sun ba da gudummawa don su tallafa wa yaƙin, wasu kuma suka sayi bindigogi da takubba don su je yaƙin. Duk da haka, ba zai dace mu yi tunanin cewa wannan dalilin ne ya sa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka ci gaba da zaman bauta a Babila Babba ba. Maimakon haka, sun fahimci cewa suna bukatar su daina yin tarayya da addinin ƙarya kuma suna gab da yin hakan a lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya.​—⁠Karanta Luka 12:​47, 48.

10. Ta yaya Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka nuna cewa suna daraja rai?

10 Ko da yake waɗannan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki ba su fahimci aihinin abin da ake nufi cewa kada Kiristoci su saka hannu a yaƙi kamar yadda muka fahimce shi a yau ba, sun san cewa Littafi Mai Tsarki ya ce kada a kashe mutum. Don haka, ‘yan’uwan da suka ɗauki makamai kuma suka je yaƙi a lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya, sun ƙi yin amfani da su don su yi kisa. An tura waɗanda suka yi haka bakin dāga don a kashe su a yaƙi.

11. Mene ne hukumomi suka yi sa’ad da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka ƙi yin amfani da takobi a yaƙi?

11 Shaiɗan ya yi fushi sosai don ‘yan’uwan sun riƙe amincinsu a lokacin yaƙin. Don haka, sai ya soma amfani da dokokin gwamnati don ya tsanata musu. (Zab. 94:20) Wani sojan Amirka manjo janar mai suna James Franklin Bell ya gaya wa J. F. Rutherford da W. E. Van Amburgh cewa gwamnati ta yi ƙoƙarin ƙiƙiro wata sabuwar doka da za ta sa a yi wa duk wanda ya ƙi saka hannu a yaƙi hukuncin kisa. Wannan mutumin yana magana ne musamman game da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki. Cikin fushi, Janar Bell ya gaya wa Rutherford cewa: “Ba a kafa dokar ba don shugaban ƙasar Amirka mai suna Wilson bai amince da dokar ba. Duk da haka, mun san yadda za mu kama ku, kuma za mu yi hakan!”

12, 13. (a) Me ya sa aka tura ‘yan’uwa guda takwas kurkuku? (b) Shin hakan ya sa ‘yan’uwan su ƙi kasancewa da aminci ne? Ka bayyana.

12 Daga ƙarshe, hukumomin sun sami  hanyar da za su iya tsananta wa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki. An kama ɗan’uwa Rutherford da Van Amburgh da kuma wasu ‘yan’uwa guda shida. Sa’ad da alƙalin yake yin hukuncinsa, ya ce: “Addinin da waɗannan mutanen suke bi ya fi sojojin Jamus haɗari sosai . . . Ɗaliban sun ƙi yin biyayya ga gwamnati da hukumomi da kuma dukan limaman coci, don haka dole ne a azabtar da su.” (Ka duba littafin nan Faith on the March da A. H. Macmillan ya rubuta, shafi na 99) An yi wa waɗannan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki hukuncin yin shekaru da yawa a kurkuku a birnin Atlanta da ke jihar Georgia. Amma an sāke su sa’ad da aka daina yin yaƙin kuma aka yi watsi da dukan abin da ake tuhumarsu a kai.

13 Waɗannan maza guda takwas sun ƙudura niyyar bin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce duk da cewa suna kurkuku. Sun rubuta wasiƙa ga shugaban ƙasar Amirka sa’ad da suke kurkuku cewa: “A cikin Littafi Mai Tsarki, Allah ya ce ‘Kada a yi kisa,’ saboda haka, Allah zai yi fushi da duk Ɗalibin Littafi Mai Tsarki da ya ƙi yin biyayya ga wannan umurnin, kuma zai halaka shi. Shi ya sa ba za mu kashe kowa ba.” Hakika, waɗannan ‘yan’uwan sun kasance da gaba gaɗi kuma sun nuna cewa za su ci gaba da kasancewa da aminci!

SUN SAMI ‘YANCI DAGA BAYA!

14. Bisa ga abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki, ka bayyana abin da ya faru a shekara ta 1914 zuwa 1919.

14 Littafin Malakai 3:​1-3 sun bayyana abin da ya faru da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki daga shekara ta 1914 zuwa farkon shekara ta 1919. (Karanta.) A wannan lokacin, Jehobah ya shigo cikin haikalinsa tare da Yesu, wato “mala’ikan alkawari” don su duba abin da “ ’ya’yan Levi,” wato shafaffu suke yi. Bayan Jehobah ya yi musu gyara kuma ya tsarkake su, sai ya ba su wani sabon aiki. A shekara ta 1919, Yesu ya naɗa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” don ya riƙa yi wa dukan bayin Allah ja-gora. (Mat. 24:45) Hakan ya sa mutanen Allah suka daina tarayya da Babila Babba gabaki ɗaya. Tun daga lokacin, sun ci gaba da koyan abubuwa game da Jehobah kuma sun ƙara ƙaunarsa sosai. Ya kamata mu riƙa godiya don wannan babban gatan! [1]

15. Ta yaya ‘yancin da muka samu daga Babila Babba ya kamata ya shafe mu?

15 Muna godiya sosai da muka sami ‘yanci daga Babila Babba! Shaiɗan ya yi iya ƙoƙarinsa don ya ga cewa babu wanɗanda suke bauta wa Allah a duniya amma bai yi nasara ba. Ya kamata mu riƙa tunawa da dalilin da ya sa Jehobah ya ‘yantar da mu daga addinin ƙarya. Dalilin shi ne yana so dukan mutane su tsira. (2 Kor. 6:⁠1) Har yanzu akwai mutane da yawa da suke bin addinin ƙarya. Waɗannan mutane suna bukatar a koya musu gaskiya. Bari mu yi iya ƙoƙarinmu don mu bi misalin waɗannan ‘yan’uwan masu aminci kuma mu taimaka wa mutane sun fito daga addinin ƙarya!

^ [1] (sakin layi na 14) Akwai abubuwan da suka faru sa’ad da Yahudawa suka yi zaman bauta a Babila na shekara 70 da suka yi daidai da abin da ya faru da Kiristoci sa’ad da ‘yan ridda suka soma yin koyarwar ƙarya. Amma zaman bautar da Yahudawa suka yi ba ya wakiltar abin da ya faru da Kiristoci, domin tsawon shekarun da suka yi zaman bautar ba ɗaya ba ne. Saboda haka, bai kamata mu soma ganin kamar duk abin da ya faru da Yahudawan sa’ad da suke zaman bauta yana wakiltar abin da ya faru da Kiristoci shaffafu shekaru da yawa kafin shekara ta 1919 ba.