Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

5-11 ga Agusta

ZABURA 70-72

5-11 ga Agusta

Waƙa ta 59 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Ku Gaya Wa “Tsara Masu Zuwa” Game da Ikon Allah

(minti 10)

Dauda ya ga yadda Jehobah ya yi ta kāre shi saꞌad da yake matashi (Za 71:5; w99 9/1 24 sakin layi na 17)

Dauda ya ga yadda Jehobah ya taimaka masa saꞌad da ya tsufa (Za 71:9; g04-E 10/8 23 sakin layi na 3)

Dauda ya ƙarfafa matasa ta wajen gaya musu tarihinsa (Za 71:​17, 18; w14 1/15 23 sakin layi na 4-5)

KA TAMBAYI KANKA, ‘Wane ne a ikilisiyarmu da ya daɗe yana bauta wa Jehobah da zan so in tattauna da shi a lokacin ibadarmu ta iyali?’

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Za 72:8—Ta yaya alkawarin da Jehobah ya yi wa Ibrahim a Farawa 15:18 ya cika a lokacin sarautar Sulemanu? (it-1-E 768)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Za 71:​1-24 (th darasi na 5)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 3) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Idan mutumin ya soma gardama, sai ka daina tattaunawa da shi cikin basira. (lmd darasi na 4 batu na 5)

5. Komawa Ziyara

(minti 4) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka ci gaba da tattauna da wani danginka da ka taɓa tattaunawa da shi, amma ya yi jinkirin amincewa da nazarin Littafi Mai Tsarki. (lmd darasi na 8 batu na 4)

6. Ka Bayyana Imaninka

(minti 5) Jawabi. ijwfq-E na 49—Jigo: Me Ya Sa Shaidun Jehobah Suka Canja Wasu Abubuwan da Suka Yi Imani da Su a Dā? (th darasi na 17)

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 76

7. Abin da Za a Iya Yi a Ibada ta Ibada ta Iyali

(minti 15) Tattaunawa.

Lokacin Ibada ta Iyali yana da muhimmanci sosai don yana sa yara su san umurnan Jehobah. (Afi 6:4) Koyon wani abu ba ƙaramin aiki ba ne, amma mutum zai iya jin dadinsa, musamman idan yara suna so su koyi gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. (Yoh 6:27; 1Bi 2:2) Ku duba akwatin nan “ Abin da Za a Iya Yi a Ibada ta Iyali” da zai taimaka wa iyaye su inganta yadda suke ibadarsu ta iyali. Sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Wanne ciki waɗannan shawarwarin za ku so ku gwada?

  • Kun ga wata shawara dabam da za ta taimaka muku?

Ku kalli BIDIYON Ku Ci-gaba da Inganta Ibadarku Ta Iyali. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Ta yaya maigida zai iya sa matarsa ta ji daɗin ibada ta iyali idan su kaɗai ne ba yara?

8. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 123 da Adduꞌa