Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 76

Yin Wa’azi Yana Sa Mu Murna?

Ka Zabi Sauti
Yin Wa’azi Yana Sa Mu Murna?
DUBA

(Ibraniyawa 13:15)

 1. 1. Yaya kuke ji ne

  in kun je yin wa’azi

  Kuma da ƙwazo kuka

  yi shelar Mulkinsa?

  Ku yi ƙoƙarinku,

  Allah zai taimake ku

  Don shi ya san mutanen

  da suke ƙaunar sa.

  (AMSHI)

  Idan muka yi wa’azi

  yana sa mu murna sosai.

  Bari mu riƙa yabon sa

  kullum har abada.

 2. 2. Yaya kuke ji ne

  in waɗanda suke jin

  Tsoron Allah suna jin

  daɗin wa’azinku?

  Wasu za su ƙi ji,

  wasu za su bijire.

  Duk da haka ba za mu

  daina wa’azi ba.

  (AMSHI)

  Idan muka yi wa’azi

  yana sa mu murna sosai.

  Bari mu riƙa yabon sa

  kullum har abada.

 3.  3. Yaya kuke ji ne

  idan kun tuna cewa

  Allah na tare da ku

  don ku yi aikinsa?

  In muna wa’azi

  mu ƙoƙarta mu ratsa

  Zuciyar mutanen da

  muke wa wa’azi.

  (AMSHI)

  Idan muka yi wa’azi

  yana sa mu murna sosai.

  Bari mu riƙa yabon sa

  kullum har abada.

(Ka kuma duba A. M. 13:48; 1 Tas. 2:4; 1 Tim. 1:11.)