DARASI NA 17
Ka Yi Bayani Dalla-Dalla
1 Korintiyawa 14:9
ABIN DA ZA KA YI: Ka taimaka wa masu sauraronka su fahimci saƙon sosai.
YADDA ZA KA YI HAKAN:
Ka bincika batun sosai. Ka fahimci batun da kyau don ka iya bayyana shi ba tare da karatu ba.
Ka yi amfani da gajerun furuci masu sauƙin fahimta. Ko da yake kana iya amfani da furuci mai tsayi, ka yi amfani da gajerun furuci don ka bayyana muhimman darussa.
Ka faɗi ma’anar furucin da ba a sani ba sosai. Kada ka riƙa yawan amfani da furucin da masu sauraronka ba su sani ba. Idan kana son ka ambata kalmar da ba a sani ba, kamar, sunan wani a Littafi Mai Tsarki ko yadda ake awo a zamanin dā ko al’adarsu, ka bayyana ma’anarsu.