Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 WAƘA TA 123

Mu Rika Bin Ja-gorancin Jehobah

Ka Zabi Sauti
Mu Rika Bin Ja-gorancin Jehobah
DUBA

(1 Korintiyawa 14:33)

 1. 1. Mu bayin Jehobah muna wa’azi,

  Wa’azi game da Mulkin Allahnmu.

  Ja-gorancin Allah za mu riƙa bi,

  Mu riƙe aminci, mu yi haɗin kai.

  (AMSHI)

  Allah Jehobah ne ya kamata

  Mu riƙa bauta wa.

  Yana ƙaunar mu, yana da iko,

  Za mu riƙe aminci.

 2. 2. Allahnmu Jehobah ya yi tanadi,

  Tanadin ruhunsa da wakilinsa.

  Za mu yi biyayya da gaba gaɗi,

  Mu riƙa wa’azin Mulkin Allahnmu!

  (AMSHI)

  Allah Jehobah ne ya kamata

  Mu riƙa bauta wa.

  Yana ƙaunar mu, yana da iko,

  Za mu riƙe aminci.

(Ka kuma duba Luk. 12:42; Ibran. 13:​7, 17.)