Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

19-25 ga Agusta

ZABURA 75-77

19-25 ga Agusta

Waƙa ta 120 da Adduꞌa | Gabatarwar Taro (minti 1)

DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH

1. Me Ya Sa Bai Kamata Mu Zama Masu Fahariya Ba?

(minti 10)

Waɗanda suke fahariya suna ɓata wa Allah rai (Za 75:4; 1Ti 3:6; w18.01 28 sakin layi na 4-5)

Duk wani aiki da muka samu a ƙungiyarmu, kyauta ce daga wurin Jehobah ba don iyawarmu ba ne (Za 75:​5-7; w06 8/1 29 sakin layi na 2)

Jehobah zai ƙasƙantar da mutanen da suke da girman kai, kamar masu mulkin duniyar nan (Za 76:12)

2. Abubuwa Masu Daraja Daga Kalmar Allah

(minti 10)

  • Za 76:10—Ta yaya “fushin” mutum yake ɗaukaka Jehobah? (w06 8/1 29 sakin layi na 3)

  • A karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon, waɗanne abubuwa masu daraja ne ka samu?

3. Karatun Littafi Mai Tsarki

(minti 4) Za 75:1–76:12 (th darasi na 11)

KA YI WAꞌAZI DA ƘWAZO

4. Fara Magana da Mutane

(minti 3) SAꞌAD DA KAKE AYYUKA NA YAU DA KULLUM. Ka nuna wani bidiyo daga jw.org a yaren da maigidan ya fi so. (lmd darasi na 1 batu na 4)

5. Fara Magana da Mutane

(minti 4) WAꞌAZI GIDA-GIDA. Ka canja abin da kake so ka faɗa saꞌad da mutumin ya gaya maka cewa bai yi imani da Allah ba. (lmd darasi na 2 batu na 5)

6. Almajirtarwa

RAYUWAR KIRISTA

Waƙa ta 127

7. Ku Riƙe Aminci Idan Aka Yabe Ku

(minti 7) Tattaunawa.

Ku kalli BIDIYON Ku Rike Aminci Kamar Yesu—Sa’ad da Aka Yabe Ku. Sai ka tambayi masu sauraro:

  • Wane darasi ne ka koya daga yadda Sergei ya amsa cikin sauƙin kai bayan da aka yabe shi?

8. Waꞌazi na Musamman da Za A Soma Nazari da Mutane a Satumba da Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!

(minti 8) Jawabin da mai kula da hidima zai yi. Ka ƙarfafa ꞌyanꞌuwa su yi marmarin wannan waꞌazi na musamman, kuma ka ambata shirin da aka yi don hakan.

9. Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya

Kammalawa (minti 3) | Waƙa ta 95 da Adduꞌa