Koma ka ga abin da ke ciki

Littafi Mai Tsarki Ya Yi Magana Game da Auren Jinsi Iri Ɗaya?

Littafi Mai Tsarki Ya Yi Magana Game da Auren Jinsi Iri Ɗaya?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Da daɗewa Mahaliccinmu ya kafa dokokin da ke sarrafa aure kafin gwamnatoci su fara sarrafa aure. Littafi na farko cikin Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa: “Mutum za ya rabu da ubansa da uwatasa, ya manne wa matatasa: za su zama nama ɗaya kuma.” (Farawa 2:24) Bisa ga abin da Vine’s Expository Dictionary of Biblical Words, Kalmar Ibranancin nan “mata” tana nufin “halitta ta mace.” Yesu ya tabbatar da cewa waɗanda aka gama su tare a aure ya kamata su “namiji da tamata” ne.—Matta 19:4.

Saboda haka, shirin Allah ne cewa aure ya zama na dindindin, gami na ƙwarai tsakanin namiji da tamace. An shirya namiji da tamace su gami juna don su iya ƙosar da sha’awar juna a jiye-jiye da ta jima’i da kuma haihuwar yara.