Koma ka ga abin da ke ciki

Littafi Mai Tsarki Ya Haramta More Jima’i Ne?

Littafi Mai Tsarki Ya Haramta More Jima’i Ne?

Amsar Littafi Mai Tsarki

Maimakon Littafi Mai Tsarki ya haramta more jima’i, ya nuna cewa baiwa ce daga wajen Allah ga wadanda suka yi aure. Ya halicci mutane “namiji da ta mace” kuma ya duba abin da ya halitta cewa “yana da kyau kwarai.” (Farawa 1:​27, 31) Lokacin da ya hada aure wa mutum da mace na farko, ya ce su “zama nama daya.” (Farawa 2:​24) Wannan gamin ya kunsa more dangantakar jima’i da kuma soyayya.

Littafi Mai Tsarki ya kwatanta dadin da mazaje ke da shi wajen matansu da kalmomin nan: “Ka yi murna da matar kuruciyarka. . . . bari mamanta su ishe ka kowane loto: Ka jarabtu da kaunarta kullayaumi.” (Misalai 5:​18, 19) Haka ma Allah ya so mata su ji more jima’i. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Miji yā ba mata tasa hakkinta na aure, haka kuma matar ga mijinta.”​—1 Korintiyawa 7:3.

Inda aka haramta yin jima’i

Allah ya ce mata da miji ne kawai suke da iznin su yi jima’i yadda yake a Ibraniyawa 13:4: “Aure shi zama abin darajantuwa a wajen dukan mutane, gado kuma shi kasance marar-kazanta: gama da fasikai da mazinata Allah za shi shar’anta.” Dole ne fa aurarru su adana alkawarinsu ga juna. Suna jin dadin kasancewa tare maimakon ban da son kai, suna bin ka’idar Littafi Mai Tsarki da ya ce: “Bayarwa ta fi karba albarka.”​—Ayyukan Manzanni 20:35.