Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Rayuwa Za Ta Koma Yadda Take Kafin Annobar Korona? Yadda Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka

Rayuwa Za Ta Koma Yadda Take Kafin Annobar Korona? Yadda Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka

 Wata shugaban jamiꞌa a jamus mai suna Angela Merkel ta ce: “Dukanmu muna son rayuwa ta koma yadda take a dā.”

 Watakila za ka iya amince da abin da ta fada, domin annobar korona ta ci gaba da shafan mutane a duk fadin duniya. Amma me ake nufi da “yadda rayuwa take a dā”? Mene ne mutane suke sa rai su yi?

  •   Su koma yin rayuwa kamar yadda take kafin annobar. Wasu suna so su yi maꞌamala da mutane, su dinga rugumar mutane da shan hannu da su, su kuma sami damar yin tafiye-tafiye. Wani Likita mai suna Anthony Fauci a ya ce: “Mutane suna ganin yin rayuwa yadda ake yi a dā ya kunshi zuwa gidan abinci da wuraren wasa da dai sauransu.”

  •   Su inganta rayuwarsu. Wasu suna ganin wannan zai ba su damar canja rayuwarsu ta fi yadda take a dā. Suna kuma ganin ya kamata wasu abubuwa su canja, kamar yin aikin da ke cin lokaci da gajiyar da mutum, da wulakancin da mutane suke sha don launin fatarsu ko kuma matsayinsu, da kuma wahala da yawa mutane suke fama da ita don matsalar kwakwalwa. Wani da ya kafa kungiyar World Economic Forum mai suna Klaus Schwab ya ce: “Annobar tana ba mu damar yin tunani game da rayuwarmu da kuma yadda za mu so duniya ta kasance da yin canje-canje a duniya. Amma damar ba za ta kasance har abada ba.”

 Annobar ta jawo ma wasu matsaloli sosai har sun soma tunanin cewa rayuwa ba za ta koma yadda take a dā ba. Alal misali, mutane da yawa sun yi rasa gidajensu da aikinsu, sun yi fama da rashin lafiya kuma wasu nasu sun rasu.

 A gaskiya babu wanda zai iya fada daidai yadda rayuwa za ta kasance bayan an gama annobar korona. (Mai-Waꞌazi 9:11) Amma, Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu kasance da raꞌayin da ya dace da kuma jimre da kowane yanayi da muka fuskanta. Kari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da abin da zai faru a nan gaba da watakila ba ka taba yin tunaninsa ba.

Kasancewa da raꞌayin da ya dace game da annobar korona

 Tun dā Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa za a yi annoba a “karshen zamani.” (Luka 21:11; Matiyu 24:3) Idan muka yi tunani game da ayoyin nan, za mu ga cewa annobar korona tana cikin abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa za su faru, kamar yake-yake da girgizar kasa da kuma yunwa.

 Ta yaya sanin wannan yake taimaka mana: Ko da yake yanayin mutane suke ciki don annobar korona zai iya yin sauki, Littafi Mai Tsarki ya ce muna rayuwa a kwanakin karshe da za a “sha wahala sosai.” (2 Timoti 3:1) Sanin hakan zai taimaka mana mu kasance da raꞌayin da ya dace game da rayuwa a wannan mawuyacin lokaci.

 Littafi Mai Tsarki ya taimaka mana mu san cewa duk da matsaloli da muke gani a duniya yau, nan ba da dadewa ba, za a sami canje-canjen abubuwa, wane canje-canje ke nan?

Za a yi rayuwar da ba mu taba tsammani ba bayan annobar

 Littafi Mai Tsarki ya annabta matsaloli da muke ciki yanzu, ya kuma fada cewa nan ba da dadewa ba, za mu ji dadin rayuwa. Ya kwatanta irin rayuwa da gwamnatocin ꞌyan Adam ba za su iya cim mawa ba, Allah ne kawai zai sa a yi irin wannan rayuwar. “Zai share musu dukan hawaye daga idanunsu. Babu sauran mutuwa, ko bakin ciki, ko kuka, ko azaba.”​—Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4.

 Jehobah b Allah ya yi alkawari cewa: “Ga shi, yanzu zan yi dukan kome sabo!” (Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21:5) Zai magance matsalolin duniyar nan, har da wadanda annobar ta janyo. Zai yi wadannan abubuwa:

  •   Mutane za su sami koshin lafiya har da na kwakwalwa, ba za a kara yin rashin lafiya da mutuwa ba.​—Ishaya 25:8; 33:24.

  •   Mutane za su rika jin dadin aikinsu, ba ayyuka da ke gajiyar da su har rasa karfi.​—Ishaya 65:​22, 23.

  •  Za a kawar da talauci da karancin abinci.​—Zabura 72:​12, 13; 145:16.

  •  Mutane za su daina bakin ciki don abin da ya faru da su a dā, za su kasance da bege cewa za a ta da mutanensu da suka rasu.​—Ishaya 65:17; Ayyukan Manzanni 24:15.

 Ta yaya sanin wannan yake taimaka mana: Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wannan sa zuciyar nan tamu tabbatacciya ce mai tsayar da hankalinmu.” (Ibraniyawa 6:19) Kasancewa da irin begen nan zai karfafa mu. Zai taimaka mana mu jimre da mawuyancin yanayi, mu rage yawan damuwa da kuma sa mu natsu mu rika farin cikin.

 Shin, za ka iya gaskata da alkawuran Littafi Mai Tsarki? Ka karanta talifin nan “Littafi Mai Tsarki Sanannen Littafi Ne Mai Fadin Gaskiya.”

Kaꞌidodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana bayan annobar korona

  •   Ka rika daukan rayuwa da muhimmanci

     Nassi: “Hikima takan kiyaye ran mai ita.”​—Mai-Waꞌazi 7:12.

     Abin da hakan yake nufi a gare ka: Ka tsai da shawarwari masu kyau don kada ka yi rashin lafiya. Ka bincika yadda annobar take a yankinku. Ka bi kaꞌidodin kiwon lafiya da ake bayarwa ka kuma lura da yawan mutane da suke kamuwa da cutar da kuma yawan mutane da suka karbi rigakafi.

  •   Ka yi hattara

     Nassi: “Mai hikima yakan yi hankali ya kauce wa mugunta, amma wawa yakan yi sauri ya aikata abu babu lura.”​—Karin Magana 14:16.

     Abin da hakan yake nufi a gare ka: Ka ci gaba da yin abubuwan da ya kamata yi don ka kāre lafiyar jikinka. Masana suna ganin cewa za mu ci gaba da fama da cutar korona na dogon lokaci.

  •  Ka bi shawara mai kyau

     Nassi: “Mai hikima yakan yi hankali ya kauce wa mugunta, amma wawa yakan yi sauri ya aikata abu babu lura.”​—Karin Magana 14:16.

     Abin da hakan yake nufi a gare ka: Ka mai da hankali ga shawarar da za ka bi. Zabin da za ki yana da muhimmanci, domin idan ka yanke shawara bisa ga labaran karya, hakan zai iya jawo maka rashin lafiya.

  •   Ka kasance da raꞌayin da ya dace

     Nassi: “Kada ka ce, “Me ya sa kwanakin dā sun fi na yanzu?” Gama tambayar nan ba daga hikima ce ta fito ba.”​—Mai-Wa’azi 7:10.

     Abin da hakan yake nufi a gare ka: Ka yi iya kokarinka ka ji dadin rayuwarka ko da wani yanayi ne kake ciki. Ka guji yin tunanin cewa yadda rayuwa take a dā ta fi na yanzu, kuma ka daina yin tunanin a kan abubuwan da annobar ta hana ka yi.

  •   Ka rika daraja mutane

     Nassi: “Ku ba da girma ga kowa.”​—1 Bitrus 2:17.

     Abin da hakan yake nufi a gare ka: Mutane sun fadi raꞌayoyinsu game da annobar da kuma abubuwan da ta jawo. Ka bar su da raꞌayinsu, amma kada ka canja shawarwari masu kyau da ka riga ka yanke. Ka rika daraja wadanda ba su karbi rigakafi ba, da kuma wadanda suke rashin lafiya mai tsanani.

  •   Ka zama mai hakuri

     Nassi: “Kauna tana da hakuri da kirki.”​—1 Korintiyawa 13:4.

     Abin da hakan yake nufi a gare ka: Kada mu kushe wa mutanen da sun nuna cewa suna so su koma yin abubuwan da suke yi kafin annobar. Saꞌad da kake shiri yin wasu ayyuka, ka yi hakuri da kanka yayin da ake saukaka abubuwan da aka hana mutanen yi.

Yadda da Littafi Mai Tsarki yake taimaka mutane su jimre da annobar

 Alkawuran da suke cikin Littafi Mai Tsarki game da nan gaba ne suke karfafa Shaidun Jehobah, yana kuma taimaka musu kada su rika yawan damuwa game da annobar. Suna kuma karfafa wa juna ta wajen yin biyayya ga umurnin Littafi Mai Tsarki na yin taron sujada. (Ibraniyawa 10:​24, 25) Muna marabtar kowa zuwa taron Shaidun Jehobah da ake yi ta manhajar yin taro ta hanyar bidiyo.

 Wasu sun ce yin taro tare da Shaidun Jehobah yana taimaka a mawuyacin lokacin nan. Alal misali, wata da ta kamu da cutar korona ta amince ta halarci taron da aka gayyace ta ta manhajar yin taro ta hanyar bidiyo. Taron sun taimaka mata duk da cewa tana fama da cutura korona. Daga baya ta ce: “Na ji kamar ni ma ina daya daga cikin iyalin nan. Karanta Littafi Mai Tsarki yana sa in kasance da salama da kuma kwanciyar hankali. Yana taimaka mana mini in mai da hankali na a begen da nake da shi game da nan gaba maimakon matsalolina. Ina gode muku don kun taimaka mini in kusaci Allah abin da na dade in nema.”

a Darektar cibiyar National Institute of Allergy and Infectious Diseases a Amirka.

b Bisa ga Littafi Mai Tsarki, Yahweh ko kuma Jehobah ne sunan Allah.​—Zabura 83:18.