Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Mene ne Mulkin Allah Zai Yi?

Mene ne Mulkin Allah Zai Yi?

Yesu ya ce almajiransa su yi addu’a Mulkin Allah ya zo. Ya san cewa munanan abubuwan da ke faruwa a yau ba nufin Allah ba ne, kuma Mulkin Allah ne kaɗai gwamnatin da za ta iya magance matsalolinmu. Mene ne Mulkin Allah zai yi?

ABIN DA MULKIN ALLAH YA RIGA YA YI

A talifi na baya, mun tattauna alamar da Yesu ya bayar. Alamar ta nuna cewa an riga an kafa Mulkin Allah a sama kuma Yesu ne aka naɗa Sarkin Mulkin.

Littafi Mai Tsarki ya ce da zarar Yesu ya zama sarki, zai kori Shaiɗan da aljanunsa daga sama. A yanzu haka, a duniyar nan ne suke da iko. Wannan yana cikin dalilan da suka sa abubuwa sun ƙara muni tun shekara ta 1914.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:​7, 9.

Duk da cewa abubuwa sai daɗa lalacewa suke a duniya, Yesu, Sarkin Mulkin Allah, ya yi abubuwa da dama don ya taimaki mutane a faɗin duniya. Yesu ya annabta cewa za a yaɗa bishara a ko’ina, kuma hakan ya sa mutane da yawa sun koyi ƙa’idodin Allah kuma sun soma bin su. (Ishaya 2:​2-4) Miliyoyin mutane sun koyi yadda za su ji daɗin zaman iyalinsu ba tare da barin aikinsu ko kayan duniya su zama abu mafi muhimmanci a rayuwarsu ba. Mutanen nan suna koyan yadda za su inganta rayuwarsu a yau, kuma suna koyan halayen da za su sa su shiga Mulkin Allah.

 MENE NE MULKIN ALLAH ZAI YI A NAN GABA?

Ko da yake Yesu ya riga ya soma sarauta a sama, mutane ne suke mulki a duniya. Amma Allah ya riga ya gaya wa Yesu cewa: “Ka ci sarauta a tsakiyar maƙiyanka.” (Zabura 110:​2, Littafi Mai Tsarki Cikin Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Nan ba da daɗewa ba, Yesu zai hallaka duka abokan gābansa kuma ya sa waɗanda suke yin nufin Allah su ji daɗin rayuwa.

A lokacin, Mulkin Allah zai:

  • Hallaka addinan ƙarya. Littafi Mai Tsarki ya kira addinan ƙarya karuwa kuma ya ce za a murƙushe ta nan ba da daɗewa ba. Za a hallaka dukan addinan da suke koyar da abin da ba daidai ba game da Allah kuma suna takura wa mutane. Mutane da yawa za su yi mamaki sa’ad da aka hallaka addinan ƙarya.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 17:​15, 16.

  • Kawar da gwamnatocin ’yan Adam. Mulkin Allah zai hallaka dukan mulkokin ’yan Adam.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 19:​15, 17, 18.

  • Hallaka mugayen mutane. Me zai faru da waɗanda suka duƙufa aikata mugunta kuma suka ƙi goyon bayan Mulkin Allah? “Za a kawar da mugaye daga ƙasar.”​—Karin Magana 2:22.

  • Hallaka Shaiɗan da aljanunsa. Ba za a bar Shaiɗan da aljanunsa su “ƙara ruɗin al’ummai” ba.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 20:​3, 10.

Ta yaya hakan zai amfani waɗanda suka goyi bayan Mulkin Allah?

 ABIN DA MULKIN ALLAH ZAI YI MA TALAKAWANSA

Da yake Yesu zai yi sarauta daga sama ne, zai yi abin da babu wani shugaba ɗan Adam ya taɓa yi. Allah ya zaɓi mutane 144,000 daga duniya don su yi sarauta tare da Yesu. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 5:​9, 10; 14:​1, 3) Yesu zai tabbata cewa an yi abin da Allah yake so a nan duniya. Mene ne Mulkin Allah zai yi wa talakawansa a duniya?

  • Zai kawar da ciwo da mutuwa. “Ba mazaunin ƙasar da zai ce, ‘Ina ciwo,’ ” kuma “babu sauran mutuwa.”​—Ishaya 33:24; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4.

  • Zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali. “Dukan ’ya’yanki . . . za su kuwa yalwata cikin salama,” kuma “kowane mutum zai zauna cikin salama a ƙarƙashin itacen inabinsa da na ɓaurensa. Ba wanda zai tsoratar da shi.”​—Ishaya 54:13; Mika 4:4.

  • Kowa zai sami aiki mai kyau. “Mutanena da na zaɓa za su daɗe suna jin daɗin aikin hannuwansu. Ba za su yi aiki a banza ba.”​—Ishaya 65:​22, 23.

  • Zai gyara duniya. ‘Daji da busasshiyar ƙasa za su yi murna, hamada za ta yi farin ciki, ta fitar da fulawa, ta ba da amfani.’​—Ishaya 35:1.

  • Zai koya wa mutane abin da za su yi don su rayu har abada. “Rai na har abada kuwa shi ne, mutane su san ka, kai da kake Allah makaɗaici na gaskiya, su kuma san Yesu Almasihu wanda ka aiko.”​—Yohanna 17:3.

Allah yana so ka more albarkun nan. (Ishaya 48:18) A talifi na gaba, za a bayyana abin da za ka yi yanzu don kai ma ka more abubuwan nan.