Koma ka ga abin da ke ciki

Me Littafi Mai Tsarki Ya Fada Game da Annoba?

Me Littafi Mai Tsarki Ya Fada Game da Annoba?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa za a yi annoba (cututtuka da suke yaduwa sosai) a kwanakin karshe. (Luka 21:​11, Littafi Mai Tsarki) Irin wadannan cututtukan ba horo ba ne daga Allah. Gaskiyar ita ce, nan ba da dadewa ba, Allah zai yi amfani da Mulkinsa wajen kawar da dukan ire-iren rashin lafiya, har da annoba.

 Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa za a yi annoba?

 Littafi Mai Tsarki bai ambaci irin annoba da za a yi ba, kamar annobar koronabairas, wato COVID-19, ko cutar sida, wato AIDS, ko annobar da ake kira Spanish flu. Amma ya annabta cewa za a yi “annoba.” (Luka 21:11; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 6:​8, Littafi Mai Tsarki) Hakan alama ce cewa muna “kwanakin karshe” ko kuma “karshen zamani.”​—2 Timoti 3:1; Matiyu 24:3.

 Allah ya taba hukunta mutane da cututtuka?

 A cikin Littafi Mai Tsarki akwai labaran wasu mutane da Allah ya hukunta su ta wajen sa su yi rashin lafiya. Alal misali ya sa wasu mutane sun zama kutare. (Littafin Kidaya 12:​1-16; 2 Sarakuna 5:​20-27; 2 Tarihi 26:​16-21) Amma a wadannan lokuta, Allah bai sa kowa da kowa har da mutanen kirki su yi rashin lafiya ba. A maimakon haka, Allah ya zabi wadanda suka yi masa rashin biyayya ne kuma ya hukunta su.

 Annoba da muke gani a yau hukunci ne daga Allah?

 A’a. Wasu suna da’awar cewa Allah yana amfani da annoba da kuma wasu cututtuka don ya yi wa mutane horo a yau. Amma Littafi Mai Tsarki bai goyi bayan wannan ra’ayin ba. Ta ya muka san haka?

 Dalili daya shi, wasu bayin Allah a dā da kuma a zamaninmu sun yi fama da rashin lafiya. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da ‘yawan rashin lafiyar’ da Timoti ya yi, duk da cewa shi mutum mai aminci ne. (1 Timoti 5:23) Littafi Mai Tsarki bai ce hakan horo ne daga wurin Allah ba. Haka ma a yau, wasu bayin Allah suna yin rashin lafiya. A yawancin lokuta, tsautsayi ne yake sa su kamu da wadannan cututtuka.​—Mai-Wa’azi 9:11.

 Kari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya ce lokacin da Allah zai hukunta mutane bai kai ba. A maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya kira wannan lokacin da muke rayuwa “ranar ceto,” ma’ana, wannan lokaci ne da Allah yake ba wa dukan ’yan Adam dama su zama aminansa don su sami ceto. (2 Korintiyawa 6:2) Wata hanyar da Allah yake amfani da ita don ya ba mutane damar samun ceto ita ce, wa’azin “labari mai dadi na Mulkin” Allah da ake yi a duk duniya.​—Matiyu 24:14.

 Akwai lokacin da za a daina yin annoba kuwa?

 E. Littafi Mai Tsarki ya yi annabci cewa lokaci yana zuwa da ba wanda zai yi rashin lafiya, kuma lokacin nan ya yi kusa. Allah zai yi amfani da Mulkinsa ya kawo karshen rashin lafiya. (Ishaya 33:24; 35:​5, 6) Zai cire wahala da azaba da mutuwa daga duniyar nan. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4) Kuma zai ta da wadanda suka mutu don su ma su ji dadin rayuwa a aljanna ba tare da rashin lafiya ba.​—Zabura 37:29; Ayyukan Manzanni 24:15.

 Nassosin da suka yi magana a kan cututtuka

 Matiyu 4:23: “Yesu ya yi ta zazzaga dukan kasar Galili, yana koyarwa a majami’unsu, yana wa’azin labari mai dadi na Mulkin Allah. Yana kuma warkar da kowane irin ciwo da rashin lafiya na mutane.”

 Ma’ana: Ayyukan ban al’ajabi da Yesu ya yi sun nuna soma tabin abin da za a yi wa ’yan Adam a Mulkin Allah nan ba da dadewa ba.

 Luka 21:​11, Littafi Mai Tsarki: “Za a yi . . . annoba.”

 Ma’ana: Cututtukan da muke gani a yau sun nuna cewa muna kwanakin karshe.

 Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 6:8: “Da na duba, sai ga wani doki wanda kalarsa ta kode. Sunan mai hawansa kuwa Mutuwa ce, Wurin Zaman Matattu kuma yana biye da shi. Aka ba su iko . . . su kashe su ta wurin . . . bala’i,” wato annoba.

 Ma’ana: Annabcin da aka yi game da mahayan dawaki hudu ya nuna cewa za a yi annoba a zamaninmu.