Hausa
Mece ce Ranar Shari’a?
https://cms-imgp.jw-cdn.org/img/p/2015328/univ/art/2015328_univ_sqr_xl.jpg

Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Mece ce Ranar Shari’a?

Ma Ya Sa Ranar Shari’a Za Ta Zama Ranar Farin Ciki?

A zamanin dā, Allah ya yi amfani da alƙalai don ya cece mutanensa daga masu zalunci. (Alƙalawa 2:18) Littafi Mai Tsarki ya ce Ranar Shari’a za ta zama lokacin farin ciki domin Jehobah wanda shi ne alƙalin dukan duniya zai ceci ’yan Adam daga masu zalunci.—Karanta Zabura 96:12, 13; Ishaya 26:9.

Allah ya naɗa Yesu don ya shari’anta masu rai da kuma matattu. (Ayyukan Manzanni 10:42; 17:31) Mutane da yawa sun mutu ba tare da sanin Allah ba. Saboda haka, a Ranar Shari’a, Yesu zai ta da waɗannan mutanen domin a koya musu game da Allah na gaskiya kuma su ƙaunace shi.—Karanta Ayyukan Manzanni 24:15.

Me ya sa Ranar Shari’a za ta ɗauki tsawon shekaru dubu?

Za a ta da matattu a lokacin sarautar Yesu ta shekaru dubu. (Ru’ya ta Yohanna 20:4, 12) Za su bukaci lokaci don su koya game da Jehobah kuma su yi masa biyayya. Akasin ra’ayoyin mutane, Littafi Mai Tsarki ya ce za a shari’anta mutane bisa ga abubuwan da suka yi bayan da aka ta da su daga mutuwa.—Karanta Romawa 6:7.

Littafi Mai Tsarki ya ce ranar shari’a za ta zo farat ɗaya, kafin shekaru dubun su soma. An kuma kira wannan ranar ƙarshe, kamar yadda aka tattauna a talifofi na farko na wannan mujallar. A wannan ranar, Allah zai halaka dukan miyagun mutane. (2 Bitrus 3:7) Saboda haka, ya kamata mu nuna cewa muna ƙaunar Allah.—Karanta 2 Bitrus 3:9, 13.