Koma ka ga abin da ke ciki

Shin Allah Zai Taimake Ni Idan Na Yi Addu’a?

Shin Allah Zai Taimake Ni Idan Na Yi Addu’a?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

 E, Allah yana taimakon wadanda suke rokon shi da gaske kuma bisa nufinsa. Ko da ba ka taba yin addu’a ba, za ka sami karfafa daga misalai na wadanda suka yi addu’a cewa, “Allah ka taimake ni” da ke Littafi Mai Tsarki. Ga wasu misalai:

  •   “Ka taimake ni, ya Ubangiji Allahna; Ka cece ni bisa ga jinƙanka.”—Zabura 109:26.

  •   “Ni matalauci ne, mai-talauci; Duk da haka Ubangiji ... kai ne taimakona.”—Zabura 40:17.

 Babu shakka, marubucin wadannan kalmomi ya yi imani da Allah sosai. Duk da haka, Allah yana sauraron duk wadanda suka yi addu’a da kyakkyawar aniya, kamar “masu karyayyar zuciya” ko kuma wadanda suke da “ruhu mai-tuba.”—Zabura 34:18.

 Kada ka ji tsoro cewa Allah yana da nisa kuma cewa bai damu da matsalolinka ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ko da shi ke Ubangiji madaukaki ne, ya kan lura da masu tawali’u: Amma masu-girman kai daga nesa ya fishe su.” (Zabura 138:6) Hakika, Yesu ya taba gaya wa almajiransa: “Har da gasussuwan kanku dukansu an kididdige su.” (Matta 10:30) Allah yana ganin abubuwa da yawa game kai da ba ka sani ba. Saboda haka, zai saurare ka sosai idan ka yi masa addu’a ya taimake ka ka jure matsalolinka!—1 Bitrus 5:7.