Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

 LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

Na Koyi Cewa Jehobah Mai Jinkai Ne da Kuma Gafartawa

Na Koyi Cewa Jehobah Mai Jinkai Ne da Kuma Gafartawa
  • SHEKARAR HAIHUWA: 1954

  • ƘASAR HAIHUWA: KANADA

  • TARIHI: MAZAMBACI DA ƊAN CĀCA

RAYUWATA A DĀ:

An haife ni a wata karkara a birnin Montreal. Mahaifina ya rasu sa’ad da nake wata shida, kuma hakan ya sa mahaifiyata ta ɗauki nawayar iyalin. Iyayena suna da yara takwas kuma ni ne ɗan auta cikinsu.

Sa’ad da nake girma, shan miyagun ƙwayoyi da yin cāca da yin faɗa da kuma yin cuɗanya da ɓarayi ya zama min jiki. Na zama masinjan karuwai da masu ba da rance a hanyar da ta saɓa wa doka, sa’ad da nake ɗan shekara goma. Ina jin daɗin yin ƙarya da zamba kamar yadda nake jin daɗin shan ƙwayoyi.

Sa’ad da na kai shekara 14, na ƙware sosai a yin zamba. Alal misali, ina sayan agogo da warwaro da su zobe masu ruwan gwal, sai in sayar da su a kan titi da kuma garejoji a matsayin gwal masu tsada. Ina farin ciki domin ina samun kuɗi a banza. Na taɓa samun dala dubu goma a yini guda!

Na rasa wurin kwana bayan da aka kore ni a makarantar gyara halin matasa masu taurin kai sa’ad da nake ɗan shekara 15. Na soma kwana a titi da gareji da kuma a gidajen abokaina.

’Yan sanda suna yawan tuhuma na saboda halina. Ba su iya kai ni gidan yari ba domin ba na sayar da kayan sata. Amma, suna ci mini tara sosai saboda zambar da nake yi da kuma yin kasuwanci ba tare da lasisi ba. Da yake ba na tsoron kowa, ina taya masu ba da rancen kuɗi karɓan kuɗin da suke bin mutane. Yin hakan na da haɗari sosai, a wasu lokuta, ina yin yawo da bindiga. A wasu kuma, ina yin aiki tare da ƙungiyoyin ɓarayi.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA:

Lokaci na farko da na san Littafi Mai Tsarki shi ne sa’ad da nake ɗan shekara 17. A lokacin, ina zama da budurwata, sai ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Amma da yake ban amince da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da ɗabi’a ba, na ƙaura daga gidanta zuwa wurin wata budurwata.

 Na soma canja ra’ayina sa’ad da ita ma ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah! Ta canje halayenta kamar su rashin haƙuri da kuma zafin rai, kuma hakan ya burge ni sosai. An gayyace ni zuwa taro a majami’ar Shaidun Jehobah. Mutane masu tsabta da kuma kirki sun marabce ni a majami’ar. Hakan ya yi dabam da abubuwan da ke faruwa a duniya! Iyalina sun ƙi ni kuma babu wanda ke ƙaunata tun ina yaro. Amma ƙaunar da Shaidun Jehobah suka nuna min ita ce ainihin abin da nake bukata. Sa’ad da Shaidun Jehobah suka ce suna so su yi nazari da ni, na amince da haka.

Abin da nake koya daga Littafi Mai Tsarki ya ceci raina. Ni da abokaina biyu mun so mu je fashi domin in sami kuɗin biyan bashin cācar dala 50,000 da na yi. Amma ina farin ciki domin na janye daga shirin. Abokaina biyun sun je fashin, an kama ɗaya cikinsu, ɗayan kuma an kashe shi.

Yayin da na ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki, na fahimci cewa ina bukatar yin canje-canje sosai. Alal misali, na koyi abin da Littafi Mai Tsarki ya ce a 1 Korintiyawa 6:10: “Ɓarayi, da masu-ƙyashi, da masu-maye, da masu-alfasha, da masu-ƙwace, ba za su gāji mulkin Allah ba.” Sa’ad da na karanta wannan ayar, irin mugun zunubin da nake yi ya sa na zub da hawaye. Na fahimci cewa ina bukatar in canja salon rayuwata gabaki ɗaya. (Romawa 12:2) Ina yawan yin faɗa da ƙarya kuma ina da zafin rai sosai.

Amma, na koya daga Littafi Mai Tsarki cewa Jehobah mai jinƙai ne kuma yana gafartawa. (Ishaya 1:18) Na roƙi Jehobah sosai ya taimaka mini in daina irin waɗannan halayen. Da taimakonsa, na yi gyara a salon rayuwata. Hanya ta musamman da na yi hakan ita ce ta wajen yin ragistan aurenmu.

A lokacin ni ɗan shekara 24 ne kuma ina da yara uku. Yanzu ina bukatar in nemi aiki mai kyau, amma matsalar ita ce, ban yi makaranta sosai ba. Na sake yin addu’a sosai ga Jehobah, bayan haka, sai na fita neman aiki. Na gaya wa mutanen da na je intabiyu wurinsu cewa ina so in canja salon rayuwata kuma in riƙa yin gaskiya. A wasu lokuta, ina gaya musu cewa ina nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ina so in zama mutumin kirki. Mutane da yawa sun ƙi su ɗauke ni aiki. Amma a ƙarshe, bayan da na gaya wa wani mutumin da ke yi mini intabiyu abubuwan da na yi a dā, sai ya ce: “Zuciyata tana ce mini in ɗauke ka aiki, amma a gaskiya ban san abin da ya sa ba.” Na san cewa Jehobah ne ya amsa addu’ata. Daga baya, ni da matata mun yi baftisma kuma mun zama Shaidun Jehobah.

YADDA NA AMFANA:

Ina da rai yau domin ina bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma ina yin abubuwa masu kyau. Ina da iyali. Zuciyata ba ta damu na yanzu domin ina da tabbaci cewa Jehobah ya gafarta min.

Na yi shekara 14 yanzu ina hidima ta cikakken lokaci, ina taimaka wa mutane su san abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki, kuma a kwana kwanan nan, matata ma ta soma wannan hidimar. A cikin sama da shekaru 30 yanzu, na taimaka wa abokan aikina guda 22 su soma bauta wa Jehobah kuma hakan na sa ni farin ciki sosai. Har yanzu ina zuwa wuraren kasuwanci, amma ba domin in zambaci mutane ba kamar yadda nake yi a dā. A yanzu, ina zuwa ne domin in gaya musu abin da na yi imani da shi. Wannan abu ne mai tamani, wato begen yin rayuwa har abada a nan gaba a duniya inda masu zamba ba za su kasance ba.—Zabura 37:10, 11.

Ina da rai a yau domin ina bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki