Ayyukan Manzanni 24:1-27
24 Bayan kwanaki biyar, sai Hananiya shugaban firistoci ya zo tare da wasu dattawa, da wani lauya mai suna Tartulus, kuma suka kai ƙarar da suke da shi a kan Bulus a gaban gwamna.
2 Da aka ba wa Tartulus izinin yin magana, sai ya soma zargin Bulus yana cewa:
“Mun ga cewa muna more zaman lafiya sosai ta wurinka, kuma muna more canje-canje a wannan ƙasar, da yake kana tunani da kyau kafin ka yi wani abu.
3 A kowane lokaci, kuma a koꞌina, mutanenmu suna ganin hakan kuma suna gode maka sosai, Ya Mai Girma Felis.
4 Amma domin kada in ƙara ɓata maka lokaci, ina roƙon ka ka yi haƙuri kuma ka saurari ɗan gajeren bayanin da za mu yi maka.
5 Gama muna da tabbacin cewa wannan mutumin mai ta da rikici* ne, yana sa Yahudawa da ke zama a dukan duniya su yi wa gwamnati tawaye, kuma shi ne shugaban ƙungiyar nan da ake kira Nazarawa.
6 Ya kuma yi ƙoƙari ya ƙazantar da haikali, shi ya sa muka kama shi.
7 * ——
8 Idan ka yi masa tambayoyi da kanka, za ka gane daga wurinsa dukan waɗannan zargi da muka kawo a kansa.”
9 Da jin hakan, sai Yahudawa ma suka goyi bayan zargin, suna cewa abubuwan nan gaskiya ne.
10 Da gwamnan ya yi wa Bulus alama da kai cewa ya yi magana, sai Bulus ya amsa ya ce:
“A shirye nake in kāre kaina, tun da na san cewa ka yi shekaru da yawa kana shariꞌa a ƙasar nan.
11 Kamar yadda kai da kanka za ka iya tabbatarwa, bai wuci kwana goma sha biyu da suka shige ba da na tafi Urushalima domin in yi bauta;
12 kuma ba su same ni ina gardama da kowa a haikali ba, ko ina zuga mutane su ta da hankalin jamaꞌa a majamiꞌu, ko kuma a dukan birnin ba.
13 Kuma ba za su iya ba ka tabbaci a yanzu da zai nuna cewa abubuwan da suke zargi na a kai gaskiya ne ba.
14 Amma na yarda cewa ina bauta wa Allah na kakannina bisa ga wannan hanyar da suka kira ƙungiyar Nazarawa, kuma na ba da gaskiya ga dukan abubuwan da suke cikin Doka* da kuma abubuwan da annabawa suka rubuta.
15 Kuma ina da bege ga Allah, irin begen da mutanen nan ma suke da shi, cewa za a yi tashin matattu na masu adalci da na marasa adalci.
16 Saboda haka ne a kullum ina iya ƙoƙarina kada in yi abin da zai sa zuciyata ta dame ni a gaban Allah da kuma mutane.
17 Bayan shekaru da yawa, na dawo ƙasata don in ba wa talakawa kyauta kuma in miƙa hadayu.
18 Yayin da nake yin abubuwan nan, sai suka same ni na tsabtace kaina bisa Doka a haikali, ba tare da jamaꞌa, ko kuma ta da hayaniya ba. Amma a wurin, akwai wasu Yahudawa daga yankin Asiya
19 waɗanda ya kamata a ce suna nan a gabanka su kawo ƙara a kaina idan suna ganin cewa na yi laifi.
20 Ko kuma mutanen da suke tsaye a nan su faɗi laifin da suka same ni da shi saꞌad da na tsaya a gaban Sanhedrin,*
21 sai ko wannan abu ɗaya kaɗai da na ɗaga murya na faɗa yayin da nake tsaye a gabansu cewa: ‘Game da tashin matattu ne ake yi mini shariꞌa a gabanku yau!’”
22 Amma da yake Felis ya san gaskiya game da Hanyar Ubangiji, sai ya ɗaga ƙarar kuma ya ce: “Idan Lisiyas shugaban sojoji ya zo, zan yanke shawara a kan wannan batun.”
23 Ya kuma ba da umurni ga jamiʹin sojan cewa ya tsare Bulus, amma ya ba shi ꞌyanci, kuma ya bar mutanensa su biya bukatunsa.
24 Bayan ꞌyan kwanaki sai Felis ya zo tare da matarsa Durusila, wadda Bayahudiya ce. Sai ya aika a kawo Bulus, kuma ya saurare shi yayin da yake magana game da ba da gaskiya ga Yesu Kristi.
25 Amma da Bulus ya yi magana game da adalci, da kamun kai, da kuma hukuncin da za a yi a nan gaba, sai Felis ya tsorata sosai, kuma ya ce: “Yanzu kam ka tafi, in na samu zarafi, zan sake kiran ka.”
26 Yana kuma sa rai cewa Bulus zai ba shi kuɗi. Saboda haka, ya yi ta aika a kira Bulus a-kai-a-kai don ya riƙa tattaunawa da shi.
27 Da shekaru biyu suka wuce, sai Fokiyus Festus ya gāji Felis; amma domin Felis yana so ya samu farin jini a wurin Yahudawa, sai ya bar Bulus a kurkuku.
Hasiya
^ Ko kuma “mai fitina.” A yaren Girka, “annoba.”
^ Wannan ayar tana cikin wasu juyin Littafi Mai Tsarki, amma ayar ba ta cikin asalin rubuce-rubucen da aka yi a yaren Girka. Don haka, da alama ba ta cikin Kalmar Allah.
^ Ko kuma “Dokar Musa.”
^ Sanhedrin shi ne Kotun Ƙolin Yahudawa. Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.