Ayyukan Manzanni 10:1-48
-
Karniliyus ya ga wahayi (1-8)
-
Bitrus ya ga wahayi na dabbobin da aka tsabtace (9-16)
-
Bitrus ya ziyarci Karniliyus (17-33)
-
Bitrus ya yi wa mutanen alꞌummai waꞌazin labarin mai daɗi (34-43)
-
“Allah ba mai nuna bambanci ba ne” (34, 35)
-
-
Ruhu mai tsarki ya sauko a kan mutanen alꞌummai kuma an yi musu baftisma (44-48)
10 Akwai wani mutum a Kaisariya mai suna Karniliyus, shi jamiꞌin soja* ne a rukunin sojojin Italiya.*
2 Shi mai bauta wa Allah ne, kuma shi da dukan iyalinsa suna tsoron Allah. Yana ba da kyauta sosai ga talakawa, kuma yana adduꞌa ga Allah kullum.
3 Wata rana, wajen ƙarfe uku na yamma,* ya ga wani malaꞌikan Allah sarai a wahayi, ya zo wurinsa ya ce: “Karniliyus!”
4 Karniliyus ya zuba wa malaꞌikan ido cikin tsoro, kuma ya tambaye shi: “Ubangiji, mene ne kake so in yi?” Sai malaꞌikan ya ce masa: “Adduꞌoꞌinka da kyautar da kake ba wa talakawa, sun kai gaban Allah, kuma yana tunawa da su.
5 Don haka, ka aika mutane zuwa Joffa don su kira wani mutum mai suna Siman, wanda ake kira Bitrus.
6 Mutumin baƙo ne a gidan Siman, wanda shi mai aikin fatar dabbobi ne, kuma gidansa yana bakin teku.”
7 Da malaꞌikan da ya yi masa magana ya tafi, sai ya kira bayinsa biyu da wani soja mai tsoron Allah daga cikin waɗanda suke yi masa hidima,
8 sai ya gaya musu kome, kuma ya aike su zuwa Joffa.
9 Washegari, yayin da suke kan hanya, kuma suka yi kusa da garin, sai Bitrus ya haura saman gida a wajen ƙarfe sha biyu na rana* don ya yi adduꞌa.
10 Amma sai yunwa ta kama shi sosai, kuma ya so ya ci abinci. Yayin da suke kan dafa abincin, sai ya ga wahayi,
11 ya ga sama ya buɗu, kuma ya ga wani abu kamar babban yadin lilin da ake saukar da shi zuwa duniya ta gefe huɗu na yadin;
12 kuma a cikinsa akwai dabbobi iri-iri masu ƙafa huɗu, da masu rarrafe, da kuma tsuntsaye.
13 Sai wata murya ta ce masa: “Ka tashi Bitrus, kuma ka yanka ka ci!”
14 Amma Bitrus ya ce: “Aꞌa, Ya Ubangiji, ban taɓa cin wani abu marar tsabta kuma mai ƙazanta ba.”
15 Sai muryar ta sake masa magana a karo na biyu, cewa: “Ka daina kiran abin da Allah ya tsabtace, abu mai ƙazanta.”
16 Hakan ya faru har sau uku, kuma nan da nan aka ɗauke abin zuwa sama.
17 Yayin da Bitrus yake kan mamaki da tunani a kan abin da wahayin da ya gani yake nufi, sai mutanen da Karniliyus ya aiko suka tambaya ina ne gidan Siman yake, kuma suka tsaya a bakin ƙofa.
18 Sai suka kira mai gidan, kuma suka tambaya ko Siman, wanda ake kira Bitrus yana gidan.
19 Yayin da Bitrus yake kan tunani a kan wahayin, sai ruhun ya ce masa: “Ga shi! Mutane uku suna neman ka.
20 Don haka, ka tashi, ka sauka ƙasa, kuma ka bi su. Kada ka yi shakka ko kaɗan, domin ni ne na aiko su.”
21 Sai Bitrus ya sauka ƙasa, ya sami mutanen, kuma ya ce: “Ga ni nan, ni ne wanda kuke nema. Me ya sa kuka zo nan?”
22 Sai suka ce: “Wani jamiꞌin soja mai suna Karniliyus ne ya aiko mu. Shi mutum ne mai adalci, mai tsoron Allah kuma, wanda dukan Yahudawa suna faɗin abubuwa masu kyau game da shi. Wani malaꞌika mai tsarki ya umurce shi ya aika a kira ka ka zo gidansa, don ya ji abin da za ka ce.”
23 Sai Bitrus ya shigar da su ciki, kuma ya ba su wurin kwana.
Washegari, sai ya tashi ya bi su, kuma wasu ꞌyanꞌuwa daga Joffa sun tafi tare da shi.
24 Washegari kuma, sun shiga Kaisariya. Karniliyus kuwa yana sa ran zuwansu, sai ya kira danginsa da kuma abokansa na kusa.
25 Da Bitrus ya shiga gidan, Karniliyus ya haɗu da shi, sai ya rusuna a gaban Bitrus kuma ya yi masa sujada.
26 Amma Bitrus ya ɗaga shi, yana cewa: “Ka tashi, domin ni ma mutum ne kamar kai.”
27 Yayin da yake magana da Karniliyus, sai ya shiga ciki kuma ya sami mutane da yawa sun taru.
28 Sai ya ce musu: “Ku da kanku kun sani cewa bisa ga dokarmu, bai kamata Bayahude ya yi tarayya ko ya kusaci wani mutum daga wata ƙasa ba. Amma Allah ya nuna mini cewa kada in ce da kowa marar tsabta ko mai ƙazanta.
29 Saboda haka, da aka ce in zo, ban ƙi ba. To, yanzu, ina so in san abin da ya sa kuka kira ni.”
30 Sai Karniliyus ya ce: “Wajen wannan lokacin, kwanaki huɗu da suka shige, ina adduꞌa a gidana wajen ƙarfe uku na yamma,* sai wani mutum sanye da kaya mai haske ya tsaya a gabana,
31 kuma ya ce: ‘Karniliyus, Allah ya amsa adduꞌarka, kuma ya tuna da kyautar da kake ba wa talakawa.
32 Don haka, ka aika mutane zuwa Joffa, su kira Siman wanda ake kira Bitrus. Shi baƙo ne a gidan Siman, wanda shi mai aikin fatar dabbobi ne a bakin teku.’
33 Sai nan take na aika a kira ka, kuma ka kyauta da ka zo nan. To, ga dukanmu mun taru a gaban Allah don mu saurari dukan abubuwan da Jehobah* ya umurce ka ka gaya mana.”
34 Da jin haka, sai Bitrus ya soma magana kuma ya ce: “Yanzu na gane cewa Allah ba mai nuna bambanci ba ne,
35 amma a kowace alꞌumma, yana amincewa da duk mutumin da yake tsoron sa kuma yake aikata abin da yake daidai.
36 Ya aika a yi wa mutanen Israꞌila shelar labari mai daɗi na salama ta wurin Yesu Kristi, wanda shi ne Ubangijin kowa.
37 Kun san batun da aka yi ta magana a kai a dukan Yahudiya, an fara daga Galili bayan baftisma da Yohanna ya yi waꞌazin sa:
38 game da Yesu wanda ya fito daga Nazaret, da yadda Allah ya naɗa shi da ruhu mai tsarki da iko, kuma domin Allah yana tare da shi, ya zagaya ƙasar yana yin alheri da warkar da dukan waɗanda Ibilis yake wahalar.
39 Kuma mu shaidu ne na dukan abubuwan da ya yi a ƙasar Yahudawa, da Urushalima; amma sun kashe shi ta wajen rataye shi a kan gungume.*
40 Allah ya ta da shi a rana ta uku, kuma ya sa mutane su gan shi,
41 ba kowa ba ne ya gan shi, sai dai mu, wato mu da Allah ya zaɓa tun dā don mu zama shaidu, mu da muka ci muka sha tare da shi bayan da aka ta da shi daga mutuwa.
42 Ƙari ga haka, ya umurce mu mu yi wa mutane waꞌazi, kuma mu ba da shaida sosai cewa shi ne Allah ya naɗa ya yi ma waɗanda suke da rai, da kuma matattu shariꞌa.
43 Dukan annabawa sun ba da shaida game da shi cewa, duk wanda yake ba da gaskiya gare shi, za a gafarta masa zunubansa ta wajen sunansa.”
44 Yayin da Bitrus yake kan magana game da abubuwan nan, sai ruhu mai tsarki ya sauko a kan dukan waɗanda suke saurarar maganar Allah.
45 Kuma Yahudawa masu bi* waɗanda suka zo tare da Bitrus sun yi mamaki sosai, domin waɗanda ba Yahudawa ba ma, an ba su kyautar ruhu mai tsarki.
46 Gama sun ji su suna magana a yaruka* dabam-dabam kuma suna ɗaukaka Allah. Sai Bitrus ya ce:
47 “Akwai wanda zai hana a yi wa mutanen nan baftisma da ruwa, tun da su ma sun sami ruhu mai tsarki kamar yadda muka samu?”
48 Sai Bitrus ya ba da umurni cewa a yi musu baftisma a cikin sunan Yesu Kristi. Bayan haka, suka roƙe shi ya zauna tare da su na ꞌyan kwanaki.
Hasiya
^ Ko kuma “jamiꞌin da ke da sojoji ɗari a ƙarƙashinsa.”
^ Ko kuma “rukunin sojojin Roma mai ɗauke da sojoji ɗari shida.”
^ A yaren Girka, “wajen awa ta tara.”
^ A yaren Girka, “wajen awa ta shida.”
^ A yaren Girka, “awa ta tara.”
^ Ka duba sashen Maꞌanar Kalmomi.
^ Ko kuma “itace.”
^ Ko kuma “Masu bi da aka yi musu kaciya.”
^ A yaren Girka, “harsuna.”