Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Kasance da Karfin Zuciya da Basira Kamar Yesu

Ka Kasance da Karfin Zuciya da Basira Kamar Yesu

Kuna ƙauna[rsa], ko da ba ku gan shi ba; kuma ko da ba ku ganinsa yanzu . . . , duk da haka, kuna ba da gaskiya gareshi.1 BIT. 1:8.

1, 2. (a) Mene ne za mu yi don mu sami ceto? (b) Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da bin hanyar da za ta sa mu sami ceto?

SA’AD DA muka zama almajiran Kristi, kamar mun soma wata tafiya. Wannan tafiyar za ta sa mu sami rai a sama ko kuma a duniya. Yesu ya ce: “Wanda ya jimre har matuƙa [ƙarshen rayuwarsa ko kuma ƙarshen wannan mugun zamani] shi ne za ya tsira.” (Mat. 24:13) Hakika, idan muka ci gaba da kasancewa da aminci, za mu sami ceto. Amma, ya kamata mu yi hattara don kada wannan duniya ta raba hankalinmu. (1 Yoh. 2:15-17) To, ta yaya za mu ci gaba da wannan tafiyar?

2 Yesu ya kafa mana misali mai kyau. An rubuta irin tafiya ko rayuwar da ya yi a cikin Littafi Mai Tsarki. Ta wajen yin nazarin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Yesu, za mu san shi. Hakan zai sa mu so shi kuma mu ba da gaskiya gare shi. (Karanta 1 Bitrus 1:8, 9.) Ka tuna cewa manzo Bitrus ya ce Yesu ya kafa mana misali mai kyau don mu bi shi sau da ƙafa. (1 Bit. 2:21) Idan muka bi sawunsa da kyau, za mu sami ceto don shi ne burinmu na kasancewa da bangaskiya. * A talifin da ya gabata, mun tattauna yadda za mu zama masu tawali’u da tausayi kamar Yesu. Bari mu bincika yadda za mu kasance da ƙarfin zuciya da basira kamar Yesu.

YESU MAI ƘARFIN ZUCIYA NE

3. Mene ne ƙarfin zuciya, kuma ta yaya za mu kasance da shi?

3 Ƙarfin zuciya zai iya ƙarfafa mu kuma ya taimaka mana sa’ad da muke fuskantar mawuyacin hali. Ƙarfin zuciya yana nufin “dauriya sa’ad da ake fuskantar mawuyacin hali,” “ɗaukan matakin yin abin da ya dace” da kuma “kasancewa da bangaskiya sa’ad da ake shan wahala.” Ƙarfin zuciya yana da alaƙa da tsoro da bege da kuma ƙauna. Ta yaya? Tsoron Allah zai sa mu kasance da ƙarfin zuciya kuma zai sa mu daina tsoron ɗan Adam. (1 Sam. 11:7; Mis. 29:25) Tabbataccen bege zai taimaka mana mu daina damuwa ainun kuma mu kasance da ra’ayi mai kyau game da nan gaba. (Zab. 27:14) Ƙauna za ta sa mu kasance da ƙarfin zuciya ko da hakan zai sa mu cikin hadari. (Yoh. 15:13) Idan muka dogara ga Allah kuma muka yi koyi da Ɗansa, za mu kasance da ƙarfin zuciya.—Zab. 28:7.

4. Ta yaya Yesu ya kasance da ƙarfin zuciya sa’ad da yake “zaune a tsakiyar malamai” a cikin haikali? (Ka duba hoton da ke shafi na 10.)

4 Yesu ya kasance da ƙarfin zuciya a lokacin da yake ɗan shekara goma sha biyu. Ka lura da abin da ya faru sa’ad da Yesu yake “cikin haikali, yana zaune a tsakiyar malamai.” (Karanta Luka 2:41-47.) Waɗannan malaman sun san Dokar da aka ba da ta hannun Musa da kuma al’adun Yahudawa sosai. Kuma waɗannan al’adun sun sa bin Dokar ya yi wuya. Amma hakan bai sa Yesu ya tsorata kuma ya yi shiru ba, a maimakon haka, ya “yi masu tambayoyi.” Ba irin tambayoyin da yara suke yi ne Yesu ya yi ba. Ka yi la’akari da yadda Yesu yake yi musu tambayoyi masu muhimmanci da suka sa malaman nan su saurare shi kuma su yi tunani. Wataƙila malaman sun yi ƙoƙari su ƙaryata Yesu ta wajen yi masa tambayoyi da za su jawo gardama, ba su yi nasara ba. Domin dukan waɗanda suka saurare shi, har da malaman sun “yi mamaki da fahiminsa da magana da yake mayarwa.” Hakika, ya ba da amsoshi da suka nuna cewa Kalmar Allah gaskiya ce.

5. A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya nuna ƙarfin zuciya a lokacin da yake hidima a duniya?

5 Yesu ya nuna ƙarfin zuciya a hanyoyi dabam-dabam a lokacin da yake hidima a duniya. Ya fallasa yadda shugabannin addini suke yaudarar mutane da koyarwar ƙarya. (Mat. 23:13-36) Yesu bai bar mugayen abubuwa da ake yi a duniya su yi tasiri a kansa ba. (Yoh. 16:33) Ya ci gaba da yin wa’azi duk da yadda ’yan adawa suke tsananta masa. (Yoh. 5:15-18; 7:14) Da gaba gaɗi ya tsabtace haikalin sau biyu ta wajen koran duk waɗanda suke ɓata bauta da ake yi a cikin haikali.—Mat. 21:12, 13; Yoh. 2:14-17.

6. Ta yaya Yesu ya yi gaba gaɗi a rana ta ƙarshe na rayuwarsa a duniya?

6 Bincika yadda Yesu ya kasance da ƙarfin zuciya sa’ad da yake shan wahala zai sa mu kasance da bangaskiya sosai. Ka yi la’akari da abin da ya faru a rana ta ƙarshe ta hidimarsa a duniya. Yesu ya san abin da zai faru idan Yahuda ya ci amanarsa. Duk da haka, a lokacin da suke cin jibin Idin Ƙetarewa, Yesu ya gaya wa Yahuda: “Abin da kake yi, ka yi shi da hanzari.” (Yoh. 13:21-27) A lambun Jathsaimani, Yesu ya bayyana kansa gaba gaɗi ga sojoji da suka zo don su kama shi. Ko da yake rayuwarsu tana cikin hadari, ya kāre almajiransa. (Yoh. 18:1-8) Sa’ad da ’yan Majalisa suka yi masa tambayoyi, ya amsa cewa shi ne Kristi Ɗan Allah gabansa gaɗi, ko da yake ya san cewa babban firist yana neman abin da zai sa a kama shi da laifi don a kashe shi. (Mar. 14:60-65) Yesu ya kasance da aminci ga Allah kuma ya mutu a kan gungumen azaba. Sa’ad da yake so ya ja numfashinsa na ƙarshe, sai ya yi kuka ya ce: “An Gama.”—Yoh. 19:28-30.

KA ZAMA MAI ƘARFIN ZUCIYA KAMAR YESU

7. Matasa, yaya kuke ji game da zama Shaidun Jehobah, kuma ta yaya za ku nuna cewa ku masu gaba gaɗi ne?

7 Ta yaya za mu zama masu ƙarfin zuciya kamar Yesu? A makaranta. Matasa, idan kuna gaya wa abokan ajinku ko wasu cewa ku Shaidun Jehobah ne ko da za a yi muku ba’a, kuna nuna cewa ku masu ƙarfin zuciya ne. Ta yin hakan kuna nuna cewa kuna alfaharin zama Shaidun Jehobah. (Karanta Zabura 86:12.) Za a iya matsa muku ku amince da koyarwar juyin halitta. Amma kuna da ƙwararan dalilai na amince da abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da halitta. Za ka iya yin amfani da bayanin da ke shafuffuka na 7-11 na fitowar Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 2013, don ba da amsa ga waɗanda suke son su san “dalilin begen” da kake da shi. (1 Bit. 3:15) Ta yin hakan za ka yi farin ciki cewa ka koyar da gaskiya da ke cikin Kalmar Allah gabanka gaɗi.

8. Waɗanne dalilai ne suke sa mu yi wa’azi gabanmu gaɗi?

8 A lokacin da muke wa’azi. Da yake mu Kiristoci na gaskiya ne, muna bukatar “yin magana gaba gaɗi cikin Ubangiji.” (A. M. 14:3) Waɗanne dalilai ne za su sa mu yi wa’azi gabanmu gaɗi ko kuma da ƙarfin zuciya? Mun san cewa abin da muke wa’azinsa gaskiya ne domin tushensa daga Littafi Mai Tsarki ne. (Yoh. 17:17) Mun fahimci cewa mu “abokan aiki na Allah ne” kuma ruhu mai tsarki yana taimakonmu. (1 Kor. 3:9; A. M. 4:31) Mun san cewa ta wajen yin wa’azi da ƙwazo, muna nuna aminci ga Jehobah da kuma ƙauna ga maƙwabtanmu. (Mat. 22:37-39) Da yake Allah ya ba mu ƙarfin zuciya, ba za mu daina yin wa’azi ba. Maimakon haka, mun ƙuduri niyya mu ƙaryata koyarwa da ke hana mutane sanin gaskiya. (2 Kor. 4:4) Kuma za mu ci gaba da wa’azin bishara ko da mutane ba sa son sauraronmu ko suna mana ba’a ko kuma tsananta mana.—1 Tas. 2:1, 2.

9. Ta yaya za mu kasance da ƙarfin zuciya a lokacin da muke shan wahala?

9 A lokacin da muke shan wahala. Dogara ga Allah yana sa mu kasance da bangaskiya da ƙarfin zuciya a lokacin da muke shan wahala. Muna makoki sa’ad da ɗan’uwanmu ya mutu, amma muna da bege. Mun dogara ga “Allah na dukan ta’aziyya” ya ƙarfafa mu. (2 Kor. 1:3, 4; 1 Tas. 4:13) Idan muna rashin lafiya mai tsanani ko kuma mun ji rauni, muna iya shan azaba amma za mu ci gaba da kasancewa da aminci ga Allah. Ba za mu karɓi magani da zai saɓa wa ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba. (A. M. 15:28, 29) Idan muka yi sanyin gwiwa “zuciyarmu” za ta iya damunmu, amma da yake mun dogara ga Allah wanda yake tare da “masu-karyayyar zuciya,” ba za mu fid da rai ba.—1 Yoh. 3:19, 20; Zab. 34:18.

YESU MAI BASIRA NE

10. Mece ce basira, kuma ta yaya mutum mai basira yake magana da kuma yin abubuwa?

10 Mutum mai basira yana bambanta nagarta da mugunta kuma ya ɗauki matakin da ya dace. (Ibran. 5:14) Basira tana nufin “iya tsai da shawawari masu kyau a batutuwan da suka shafi ibada.” Mutum mai basira yana magana da kuma yin abubuwa da za su faranta wa Allah rai. Irin wannan mutum yana magana da za ta ƙarfafa wasu maimakon ya ɓata musu rai. (Mis. 11:12, 13) Shi “mai-jinkirin fushi” ne. (Mis. 14:29) Yana “daidaita tafiyarsa” wato, yana bin tafarki mai kyau a rayuwarsa. (Mis. 15:21) Ta yaya za mu zama masu basira? Wajibi ne mu yi nazarin Kalmar Allah kuma mu yi amfani da abin da muka koya. (Mis. 2:1-5, 10, 11) Da yake babu mai basira kamar Yesu, yana da muhimmanci sosai mu bi misalin da Yesu ya kafa.

11. Ta yaya Yesu ya nuna basira a furucinsa?

11 Yesu ya nuna basira a dukan abubuwan da ya faɗa da kuma yi. A furucinsa. Ya nuna basira a lokacin da yake wa’azin bishara, don ya yi amfani da “zantattukan alheri” da suka burge masu sauraronsa. (Luk. 4:22; Mat. 7:28) Sau da yawa, yakan yi amfani da Kalmar Allah, wato yana karanta ko ya yi ƙauli ko kuma ya ambata nassosi da suka dace don ya koyar da wani darasi. (Mat. 4:4, 7, 10; 12:1-5; Luk. 4:16-21) Yesu ya kuma ba da bayanin Nassosi, ya yi hakan a hanyoyi da za su motsa masu sauraronsa. A lokacin da yake magana da almajirai biyu da suke tafiya zuwa Immawus bayan ya tashi daga matattu, Yesu ya bayyana “musu al’amura na bisa kansa” kamar yadda aka ambata a cikin Nassosi. Bayan haka almajiran suka ce: “Zuciyarmu ba ta yi ƙuna daga cikinmu ba, sa’anda . . . yana bayyana mamu littattafai?”—Luk. 24:27, 32.

12, 13. Waɗanne misalai ne suka nuna cewa Yesu mai jinkirin fushi ne da sanin yakamata?

12 A ra’ayinsa da halinsa. Basira ta taimaka wa Yesu ya kame kansa, kuma ya zama “mai-jinkirin fushi.” (Mis. 16:32) Shi “mai-tawali’u” ne. (Mat. 11:29) A koyaushe yana haƙuri da almajiransa duk da kasawarsu. (Mar. 14:34-38; Luk. 22:24-27) Ya kame kansa ko a lokacin da aka yi masa rashin adalci.—1 Bit. 2:23.

13 Basira ta taimaka wa Yesu ya kasance da sanin yakamata. Ya fahimci ainihin abin da Dokar da aka ba da ta hannun Musa yake koyarwa, kuma hakan ya shafi yadda ya bi da mutane. Alal misali, ka yi la’akari da labarin da ke cikin Markus 5:25-34. (Karanta.) Wata mata mai zuban jini ta shiga cikin jama’a, ta taɓa tufafin Yesu kuma ta warke. Bisa Doka ba ta da tsabta, saboda haka bai kamata ta taɓa kowa ba. (Lev. 15:25-27) Amma Yesu wanda ya fahimci cewa “muhimman jiga-jigan Attaura” sun ƙunshi “jinƙai da aminci” bai tsauta mata ba don ta taɓa rigarsa. (Mat. 23:23, Littafi Mai Tsarki) Maimakon hakan, ya ce: “Ɗiya, bangaskiyarki ta warkar da ke; ki tafi lafiya, ki rabu da azabarki.” Babu shakka, basira ce ta sa Yesu ya yi wannan alherin!

14. Mene ne Yesu ya yi a rayuwa kuma ta yaya ya ci gaba da wannan aikin?

14 A rayuwarsa. Yesu ya nuna basira ta wajen zaɓan tafarkin da ya dace a rayuwarsa kuma bai bijire ba. Ya ba da kansa ga wa’azin bishara, kuma ya sa hakan ya zama sana’arsa. (Luk. 4:43) Yesu ya tsai da shawarwari da suka taimaka masa ya mai da hankali ga aikin har ya cim ma wannan aikin. Ya yi rayuwa mai sauƙi don ya ba da lokacinsa da ƙarfinsa ga yin wa’azi. (Luk. 9:58) Ya fahimci cewa yana bukatar ya koyar da wasu su ci gaba da aikin bayan ya mutu. (Luk. 10:1-12; Yoh. 14:12) Ya yi wa mabiyansa alkawari cewa zai ci gaba da goyon bayansu a wannan aikin “har matuƙar zamani.”—Mat. 28:19, 20.

KA ZAMA MAI BASIRA KAMAR YESU

Ka fahimci bukatun waɗanda kake musu wa’azi kuma ka faɗi abin da ya dace da kowannensu (Ka duba sakin layi na 15)

15. Ta yaya za mu nuna basira a furucinmu?

15 Ka yi la’akari da wata hanya da za mu iya kasancewa kamar Yesu. A furucinmu. Sa’ad da muke tattaunawa da ’yan’uwa, ya kamata mu faɗi abin da zai ƙarfafa su maimakon ɓata musu rai. (Afis. 4:29) A lokacin da muke wa mutane wa’azi game da Mulkin Allah, ya kamata furucinmu ya kasance “mai daɗin ji.” (Kol. 4:6, LMT) Ya kamata mu fahimci bukatun waɗanda muke musu wa’azi kuma mu faɗi abin da ya dace. Mu tuna cewa idan furucinmu ya kasance da daɗin ji, mutane za su saurare mu kuma wa’azinmu zai motsa su. Ƙari ga haka, ya kamata mu yi amfani da Littafi Mai Tsarki a lokacin da muke bayyana koyarwarmu. Saboda haka, ya kamata Littafi Mai Tsarki ya zama tushen koyarwarmu kuma mu riƙa karanta shi a duk lokacin da zai yiwu. Mun fahimci cewa saƙon da ke cikin Littafi Mai Tsarki yana da iko fiye da abin da muke faɗa.—Ibran. 4:12.

16, 17. (a) Ta yaya za mu nuna cewa mu masu jinkirin fushi ne da sanin yakamata? (b) Ta yaya za mu ci gaba da mai da hankali ga yin wa’azi?

16 A ra’ayinmu da halinmu. Basira tana taimaka mana mu kame kanmu, kuma mu “yi jinkirin yin fushi.” (Yaƙ. 1:19) Idan wasu suka ɓata mana rai, muna ƙoƙari mu fahimci dalilan da suke sa su yi wasu abubuwa. Irin wannan basira za ta taimaka mana mu kame kanmu kuma mu riƙa gafarta wa mutane. (Mis. 19:11) Basira tana taimaka mana mu zama masu sanin yakamata. Hakan zai sa mu bi da ’yan’uwanmu yadda ya kamata, da yake wataƙila suna fuskantar ƙalubale da ba mu sani ba. Mu kasance a shirye mu saurari ra’ayinsu kuma a lokacin da ya dace mu bi abin da suka faɗa.—Filib. 4:5.

17 A rayuwarmu. Da yake mu mabiyan Yesu ne, mun san cewa babu gatan da ya fi yin wa’azin bishara. Ya dace mu tsai da shawarwarin da za su taimaka mana mu ci gaba da wa’azi. Muna saka abubuwa da suka shafi ibadarmu kan gaba kuma mu yi rayuwa mai sauƙi don mu ba da kanmu ga aikin wa’azi da ya fi muhimmanci kafin ƙarshen zamani.—Mat. 6:33; 24:14.

18. Ta yaya za mu ci gaba da tafiya a hanyar da za ta sa mu sami ceto, kuma mene ne ka ƙuduri niyyar yi?

18 Mun yi farin cikin tattauna wasu cikin halayen Yesu masu kyau. Babu shakka, za mu amfana ta wajen nazarin wasu halayensa kuma mu yi koyi da shi. Bari mu ƙuduri niyya mu bi sawunsa sosai. Ta yin hakan, za mu ci gaba da tafiya a hanyar da za ta kai mu ga samun ceto, kuma za mu kusaci Jehobah wanda Yesu ya yi koyi da shi sosai.

^ sakin layi na 2 An rubuta 1 Bitrus 1:8, 9 don Kiristoci da suke da begen zuwan sama. Amma waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya za su amfana daga darasin da ke waɗannan ayoyin har ila.