Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Jehobah ne Yake Ja-gorar Aikin Koyarwa da Muke Yi a Dukan Duniya

Jehobah ne Yake Ja-gorar Aikin Koyarwa da Muke Yi a Dukan Duniya

“Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda yake koya maka zuwa amfaninka, wanda yana bishe ka ta hanyar da za ka bi.”—ISHA. 48:17.

1. Waɗanne ƙalubale ne Kiristoci na zamani suka fuskanta?

ƊALIBAN Littafi Mai Tsarki * da suka soma wa’azi sama da shekaru 130 da suka shige sun fuskanci ƙalubale da yawa. Kamar Kiristoci na farko, suna wa’azin saƙon da mutane ba sa son su ji. Ba su da yawa kuma mutanen duniya sun yi musu kallon marasa ilimi. Ƙari ga haka, sun fuskanci “hasala mai-girma” daga wurin Shaiɗan Iblis da shigewar lokaci. (R. Yoh. 12:12) Ban da hakan, a “kwanaki na ƙarshe” na wannan ‘mugun zamani’ ne za su yi wa’azin bishara.—2 Tim. 3:1.

2. Mene ne Jehobah yake yi don wa’azin bishara ya yi tasiri a zamaninmu?

2 Duk da haka, Jehobah yana so a yi wa’azin bishara sosai a zamaninmu kuma babu abin da zai hana shi cika wannan manufar. Jehobah ya ceci bayinsa na zamani daga “Babila Babba,” wato dukan addinan ƙarya, kamar yadda ya ceci al’ummar Isra’ila ta dā daga ƙasar Babila. (R. Yoh. 18:1-4) Ya koyar da mu don mu amfana,  kuma ya taimaka mana mu koyar da nufinsa ga wasu. (Karanta Ishaya 48:16-18.) Hakan ba ya nufin cewa Jehobah yana hangen abin da zai faru don ya sarrafa yanayin a yadda za mu ji daɗin yin wa’azin bishara. Hakika, a wasu lokatai mun ji daɗin wa’azin bishara, amma Jehobah ne ya taimaka mana mu jure mawuyacin hali kamar tsanantawa da kuma wasu ƙalubale da ya sa yin wa’azi ya kasance da wuya a duniyar nan na Shaiɗan.—Isha. 41:13; 1 Yoh. 5:19.

3. Ta yaya “ilimi” ko kuma koyarwa ta gaskiya ta bunƙasa?

3 Jehobah ya hure annabi Daniyel ya annabta cewa “ilimi” ko kuma koyarwa ta gaskiya za ta bunƙasa a kwanaki na ƙarshe. (Karanta Daniyel 12:4.) Jehobah ya taimaka wa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki su tantance ainihin koyarwar Littafi Mai Tsarki daga koyarwar jabun Kiristoci. Yanzu haka, yana amfani da mutanensa wajen sanar da koyarwa ta gaskiya a faɗin duniya. A yau, muna ganin cikar annabcin Daniyel. Wajen mutanen 8,000,000 sun koyi gaskiyar kuma suna koyar da wasu game da ita. Shin waɗanne abubuwa ne suka taimaka mana a yin wa’azin bishara a faɗin duniya?

YADDA FASSARA LITTAFI MAI TSARKI TA TAIMAKA MANA

4. Ka bayyana yadda fassara ta sa Littafi Mai Tsarki ya bunƙasa a ƙarni na sha tara.

4 Wani abin da ya sa wa’azin bishara ya sami ci gaba shi ne kasancewar Littafi Mai Tsarki a ko’ina. Limaman Kiristoci na ƙarya sun hana karanta Littafi Mai Tsarki kuma sun yi gāba da waɗanda suka yi hakan a ɗarurruwan shekaru da suka shige. Har ma sun kashe wasu mutanen da suka fassara Littafi Mai Tsarki. A ƙarni na 19, ƙungiyoyin fassara Littafi Mai Tsarki sun tanadar da Littafi Mai Tsarki gaba ɗaya ko sashe a cikin harsuna ɗari huɗu. A ƙarshen wannan ƙarni na 19, mutane da yawa suna da Littafi Mai Tsarki amma ba su fahimci ainihin abin da yake koyarwa ba.

5. Mene ne Shaidun Jehobah suka cim ma a fassara Littafi Mai Tsarki?

5 Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun san cewa wajibi ne su yi wa’azi, kuma sun sanar wa mutane abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa da ƙwazo. Ƙari ga haka, bayin Jehobah sun yi amfani da Littafi Mai Tsarki dabam-dabam kuma sun rarraba su. A shekara ta 1950, sun fassara New World Translation of the Holy Scriptures gaba ɗayansa ko sashensa zuwa harsuna sama da ɗari da ashirin. Juyin New World Translation na Turanci da aka fitar a shekara ta 2013 zai sa fassara wannan juyin zuwa wasu harsuna ya kasance da sauƙi. Ƙari ga haka, yin amfani da Littafi Mai Tsarki mai sauƙin fahimta yana taimaka mana mu yi wa’azin bishara.

YADDA KWANCIYAR HANKALI YA TAIMAKA MANA

6, 7. (a) Waɗanne yaƙe-yaƙe ne aka yi a zamaninmu? (b) Ta yaya kwanciyar hankali da aka yi a wasu ƙasashe ya amfani wa’azin bishara da muke yi?

6 ‘Akwai lokacin da aka yi zaman lafiya a zamaninmu kuwa?’ Wani zai iya yin wannan tambayar don a ƙarni na 20 miliyoyin mutane sun mutu sanadiyyar yaƙe-yaƙe, musamman ma yaƙin duniya na ɗaya da na biyu. Amma yayin da ake Yaƙin Duniya na Biyu a shekara ta 1942 ne Ɗan’uwa Nathan Knorr da ke ja-gorar Shaidun Jehobah a lokacin ya ba da wani jawabi mai jigo: “PeaceCan It Last?” (Salama, Za Ta Dawwama Kuwa?) A jawabin, an bayyana wasu ayoyi daga Ru’ya ta Yohanna 17 da ke nuna cewa yaƙin da ake yi a lokacin zai kai ga zaman lafiya, ba Armageddon ba.—R. Yoh. 17:3, 11.

7 Hakan ba ya nufin cewa an sami kwanciyar hankali a ko’ina bayan Yaƙin Duniya na Biyu. Wani bincike ya nuna cewa daga shekara ta 1946 zuwa 2013, an yi wasu  yaƙe-yaƙe guda 331. Miliyoyi mutane sun rasa rayukansu. Amma a cikin waɗannan shekarun ƙasashe da yawa sun sami kwanciyar hankali kuma bayin Jehobah sun yi amfani da wannan zarafin wajen yin wa’azin bishara. Mene ne sakamakon? A shekara ta 1944, Shaidun Jehobah a faɗin duniya ba su kai 110,000 ba. Amma a yau Shaidun Jehobah sun kai wajen 8,000,000! (Karanta Ishaya 60:22.) Ya kamata mu gode cewa za mu iya yin wa’azin bishara a waɗannan lokatan da ake kwanciyar hankali, ko ba haka ba?

YADDA SAUƘIN SUFURI YA TAIMAKA MANA

8, 9. Wane ci gaba ne aka samu a fannin sufuri, kuma ta yaya hakan ya taimaka a wa’azin bishara?

8 Ci gaba da aka samu a sufuri ya taimaka sosai a wa’azin bishara. A shekara ta 1900, wato shekaru 21 bayan da aka wallafa Hasumiyar Tsaro ta farko, ƙananan motoci guda 8,000 kawai aka san da zamansu a Amirka kuma babu isashen hanyoyi masu kyau da za a tuƙa waɗannan motocin a kai. Yanzu, a faɗin duniya, akwai motoci fiye da biliyan ɗaya da rabi da aka yi musu rajista kuma akwai hanyoyin kusan mota ko’ina. Hakan ya taimaka wa da yawa daga cikinmu mu kai wa’azin bishara zuwa ƙauyuka. Amma, ko da ba mu da mota kuma ya zama mana wajibi mu yi doguwar tafiya, muna ɗaukan matakan da ake bukata don mu taimaka wa mutane su zama almajiran Yesu.—Mat. 28:19, 20.

9 Wasu hanyoyin sufuri sun taimaka mana a wa’azin bishara. Manyan motoci da jiragen ruwa da jiragen ƙasa suna taimakawa wajen kai littattafai wurare masu wuyan shiga a cikin makonni. Jiragen sama suna taimaka wajen jigilar ’yan’uwa masu hakki zuwa manyan taro ko kuma zuwa yin wasu ayyuka a ƙungiyar Jehobah. Waɗannan sun haɗa da masu kula da da’ira da membobin Kwamitin da Ke Kula da Ofisoshin Shaidun Jehobah da masu wa’azi a ƙasashen waje. Ƙari ga haka, mambobin Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah da kuma wasu sun bi jiragen sama zuwa ƙasashe dabam-dabam don ƙarfafa ’yan’uwa. Hakika, ci gaba da aka samu a sufuri ya taimaka wajen tabbatar da haɗin kai tsakanin bayin Jehobah.—Zab. 133:1-3.

YADDA YARE YA TAIMAKA MANA

10. Me ya sa za mu iya ce Turanci yare ne gama gari?

10 A ƙarni na farko, yaren girka da ake  kira Koine ne aka yi a Daular Roma. Shin akwai wani yare da ake yi a wurare da yawa a yau? Mutane da yawa sun amince cewa Turanci ne yaren da ake yi gama gari a yau. An bayyana a cikin littafin nan, English as a Global Language cewa “Wajen kashi ɗaya cikin huɗu na jama’ar duniya sun iya Turanci.” Turanci shi ne yaren ƙasar waje da aka fi koyarwa kuma ana amfani da shi wajen sadarwa tsakanin ƙasashe a harkokin kasuwanci da siyasa da kimiyya da kuma fasaha.

11. Ta yaya Turanci ya shafi ci gabar da aka samu a ibada ta gaskiya?

11 Da yake ana amfani da Turanci a kusan ko’ina a faɗin duniya, hakan ya taimaka wajen bunƙasa ibada ta gaskiya. Da farko, an yi shekaru da dama ana wallafa Hasumiyar Tsaro da kuma wasu littattafai a Turanci. Turanci shi ne yaren da ake amfani da shi a hedkwatar Shaidun Jehobah. Ƙari ga haka, ana amfani da Turanci wajen koyar da ɗalibai a cibiyar koyarwa ta Watchtower da ke Patterson, New York, a Amirka.

12. Cikin harsuna nawa ne bayin Jehobah suka fassara littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki, kuma ta yaya fasaha ta taimaka?

12 Da yake muna da hakkin yin wa’azin bishara ta Mulki ga mutanen dukan al’ummai, mun fassara littattafanmu cikin harsuna wajen 700. Ci gabar da aka samu a fasahar kwamfuta da manhajar MEPS (Multilanguage Electronic Publishing System) sun taimaka a wannan fannin da ake da bukata sosai. Waɗannan abubuwan sun taimaka mana wajen yaɗa bishara ta Mulki kuma ya kyautata haɗin kai tsakaninmu a faɗin duniya. Amma ainihin abin da ya sa muke da haɗin kai shi ne sanin “harshe mai-tsarki” ko kuma gaskiyar Littafi Mai Tsarki.—Karanta Zafaniya 3:9.

YADDA DOKOKI SUKA TAIMAKA MANA

13, 14. Ta yaya Shaidun Jehobah suka amfana daga dokoki da kuma hukunce-hukunce da kotuna suka yanke?

13 A talifin da ya gabata, mun tattauna cewa Kiristoci na farko sun amfana daga tsarin dokokin Roma da aka zartar a dukan masarautar. Hakazalika, a yau ma Kiristoci na zamani sun amfana daga dokokin ƙasashe dabam-dabam. Alal misali, kundin tsarin dokokin ƙasar Amirka, inda hedkwatarmu take, ta ba da ’yancin gudanar da addini da faɗar ra’ayi da kuma yin taro. Hakan ya ba wa ’yan’uwa a Amirka damar yin taro don su tattauna Littafi Mai Tsarki da kuma damar yi wa mutane wa’azi. Amma a wasu lokatai, muna zuwa kotu don mu kāre ’yancinmu. (Filib. 1:7)  Lokatan da aka kai ƙarar Shaidun Jehobah kotu a Amirka saboda wa’azin bishara, suna ɗaukaka ƙara zuwa manyan kotuna kuma a yawancin lokaci, sukan yi nasara.

14 A wasu ƙasashe har ila, mun kai ƙara kotu don neman ’yancin yin ibada da kuma wa’azi. Duk lokacin da ba mu yi nasara ba, mukan ɗaukaka ƙara zuwa kotunan ƙasa da ƙasa. Alal misali, a watan Yuni na shekara ta 2014, Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam ya ba mu nasara a ƙararaki guda 57 kuma hakan ya shafi dukan ƙasashen da ke cikin Ƙungiyar Ƙasashen Turai. Ko da yake mun zama “abin ƙi ga dukan al’ummai,” kotuna a ƙasashe da yawa sun yanke hukunci da ya ba mu ’yancin yin ibada ta gaskiya.—Mat. 24:9.

YADDA WASU ABUBUWA SUKA SHAFI AIKINMU NA KOYARWA

Muna wallafa littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki wa mutane a faɗin duniya

15. Wace ci gaba ce aka samu a buga littattafai, kuma ta yaya hakan ya taimake mu?

15 Ci gabar da aka samu a buga littattafai ya taimaka wajen yaɗa wa’azin bishara a faɗin duniya. An yi ƙarnuka ana amfani da irin na’urar buga littattafai na dā da Johannes Gutenberg ya ƙirƙiro a shekara ta 1450. Amma a shekaru ɗari biyu da suka shige, an sami ci gaba sosai a masana’antun buga littattafai. Maɗaba’o’in da ake amfani da su yanzu suna da girma da sauri kuma suna yin ayyuka dabam-dabam a lokaci guda. Samar da takardu da kuma yi wa littafi bango sun yi sauƙi. Tsarin buga littattafai da ake yawan amfani da shi yanzu, wato offset printing ya inganta buga littattafai kuma ya sa an daina amfani da tsarin letterpress. Tsarin offset printing ya sa buga littattafai ya bunƙasa kuma ya ƙara kyan hotuna. Ta yaya hakan ya inganta aikinmu? Ka yi la’akari da wannan: Hasumiyar Tsaro na farko da aka wallafa a Yuli ta shekara ta 1879 kofi guda 6,000 ne kuma babu hotuna. Ƙari ga haka, an buga shi a Turanci ne kawai. Yanzu, wato shekaru 136 bayan haka, ana buga da kuma rarraba sama da kofi miliyan 50 na kowace fitowa ta Hasumiyar Tsaro. Ana buga shi a cikin harsuna fiye da 200 kuma hotunan suna fitowa da kala masu kyau.

16. Waɗanne ƙere-ƙere ne suka taimaka mana a yin wa’azin bishara a faɗin duniya. (Ka duba hoton da ke shafi na 24.)

16 Bayin Allah sun yi amfani da abubuwa dabam-dabam da aka ƙirƙiro a shekaru 200 da suka shige don yin wa’azin bishara. Mun ambaci jiragen ƙasa da motoci da jiragen sama. Ban da waɗannan, mun yi amfani da kekuna da tafireta da na’urorin rubutun makafi da talgiram da tarho da kyamara da na’urorin ɗaukan sauti da bidiyo da rediyo da talabijin da silima da kwamfuta da kuma Intane. Waɗannan abubuwan sun taimaka mana a hanyoyi da yawa don mu cika umurnin da aka ba mu na yin wa’azi. Mun cika wannan annabcin nan da ke cewa bayin Jehobah za su sha “nonon al’ummai” ta wajen yin amfani da tanadodin ƙasashe kamar fasaha ta zamani don buga Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki a cikin harsuna da yawa.—Karanta Ishaya 60:16.

17. (a) Wane tabbaci ne muke da shi? (b) Me ya sa Jehobah ya ba mu damar kasancewa ‘abokan aikinsa’?

17 Babu shakka, muna da tabbaci cewa Allah yana goyon bayanmu. Ko da yake Jehobah ba ya dogara ga ’yan Adam don ya cim ma nufinsa. Duk da haka, Ubanmu na sama mai ƙauna ya ba mu damar kasancewa ‘abokan aikinsa’ kuma ta yin hakan, ya ba mu zarafin nuna cewa muna ƙaunarsa da kuma maƙwabtanmu. (1 Kor. 3:9; Mar. 12:28-31) Bari mu yi amfani da zarafin da muke da shi don yin aiki mafi muhimmanci a duniya, wato wa’azin bishara ta Mulki. Ƙari ga haka, mu riƙa godiya ga Jehobah don yadda ya yi mana ja-gora da kuma albarka a wannan aikin koyarwa da muke yi a faɗin duniya!

^ sakin layi na 1 A shekara ta 1931 ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka canja sunansu zuwa Shaidun Jehobah.—Isha. 43:10.