HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI fabrairu 2015

Kyauta da Ta Sa Mutanen Japan Farin Ciki

An fitar da sabon littafi mai suna ‘The Bible—The Gospel According to Matthew’ a kasar Japan. Wadanne abubuwa ne ke cikin wannan littafin? Me ya sa aka wallafa shi?

Ka Kasance da Tawali’u da Tausayi Kamar Yesu

1 Bitrus 2:21 ya umurce mu mu bi sawun Yesu. Ko da yake mu ajizai ne, ta yaya za mu kasance da tawali’u da tausayi kamar Yesu?

Ka Kasance da Karfin Zuciya da Basira Kamar Yesu

Za mu koya game da Yesu ta wurin bincika abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Ka yi la’akari da yadda za mu iya bin misalinsa ta wajen zama masu karfin zuciya da basira kamar shi.

Kada Ka Yi Sanyin Gwiwa a Hidimarka

Mun san cewa yin wa’azi shi ne aiki mafi muhimmanci da za mu iya yi a yau. Mene za mu yi don mu kara kwazo a wa’azi?

Shirya Al’ummai don Koyarwar Jehobah

Wane sakamako ne almajiran Yesu na karni na farko suka samu a wa’azi? Wadanne abubuwa ne suka sa wa’azin bishara ya sami ci gaba a karni na farko fiye da wasu lokatai a tarihi?

Jehobah ne Yake Ja-gorar Aikin Koyarwa da Muke Yi a Dukan Duniya

Wadanne abubuwa ne a shekarun baya suka taimaka wa bayin Jehobah su yi wa’azin bishara sosai a fadin duniya?

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Ta yaya za a iya taimaka wa ’yan’uwa da turare ke damunsu? A wane yanayi ne ya kamata ’yar’uwa ta daura dankwali?

DAGA TARIHINMU

“Lokaci Mai Muhimmanci Sosai”

Hasumiyar Tsaro ta kira lokacin Tuna Mutuwar Kristi ‘lokaci mai muhimmanci sosai’ kuma ta karfafa masu karatu su yi taron. Ta yaya aka yi taron Tuna da Mutuwar Yesu a lokacin?