Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Mene ne za a iya yi don a taimaka wa ’yan’uwa da ƙamshin turare yake damunsu?

Duk wanda ƙamshin turare yake damunsa yana fuskantar ƙalubale sosai. A yawancin lokaci, ba abin da za su iya yi don guje wa ƙamshin turare sa’ad da suke harkokin yau da kullum da mutane. Duk da haka, wasu sun yi tambaya ko zai yiwu a gaya wa ’yan’uwa su daina amfani da turare sa’ad da suke halartar taron ikilisiya da kuma manyan taro.

Hakika, ba Kirista da zai so ya sa halartan taro ya kasance wa ɗan’uwansa jan aiki. Dukanmu muna bukatar ƙarfafa da ake samu a taronmu. (Ibran. 10:24, 25) Saboda haka, duk waɗanda ƙamshin turare yake damunsu sosai da har yana hana su halartar taro suna iya tattauna batun da dattawa. Bai dace a kafa dokoki game da yadda waɗanda ke halartan taro za su riƙa amfani da turare ba kuma Littafi Mai Tsarki bai hana shafa turare ba, amma dattawa za su iya ba da bayani don ’yan’uwa a ikilisiya su fahimci matsalolin da wasu suke fuskanta game da wannan batun. Bisa ga yanayin, dattawa za su iya sa a ba da jawabi bisa ga bayanin da aka wallafa a littattafanmu game da turare a sashen bukatun ikilisiya na Taron Hidima, ko kuma su yi sanarwa a kan batun a yadda ba zai ɓata ran waɗanda suka halarci taro ba. * Amma, ba zai dace dattawa su riƙa yin irin wannan sanarwa a kai a kai ba. Waɗanda suka saurari wa’azi da baƙi suna halartan taronmu, kuma ba su da masaniya game da wannan batun. Muna so su ji daɗin taronmu. Idan mutum ya shafa turare daidai wa daida, bai kamata a sa shi ya ji wani iri domin hakan ba.

Idan akwai waɗanda suke da matsalar a ikilisiyarku, rukunin dattawa za su iya yin shiri don waɗanda turare yake damunsu su riƙa zama a wani wuri da aka keɓe a cikin Majami’ar Mulki idan hakan zai yiwu. Alal misali, suna iya zama su saurari taron a wani ɗaki a Majami’ar Mulki da ke da lasifika. Idan ba za a iya magance batun ba kuma ƙamshin turare yana damun wasu ainun, dattawa za su iya shirya a ɗauka musu jawaban taron da rakoda ko kuma a shirya su saurari taron ta tarho a gidajensu, kamar yadda ake wa waɗanda ba sa iya fita daga gidajensu saboda wata larura.

A kwanan nan, an ƙarfafa ’yan’uwa a cikin Hidimarmu ta Mulki su riƙa yin la’akari da waɗanda wannan matsalar ta shafa yayin da suke halartan taron yanki. An shawarci ’yan’uwa su riƙa rage yawan turare da suke shafawa musamman a taron yanki, da yake ba zai yiwu a hana mutane shafa turare a waɗannan taron ba. Amma, ba a ba da wannan shawarar da niyyar mai da ita dokar da za a riƙa bi a taron ikilisiya ba, kuma bai kamata a bayyana shi hakan ba.

Yayin da muke zama a wannan zamanin, dukanmu muna shan wahalar sakamakon ajizancin da muka gāda. Muna godiya ga waɗanda suke yunkurin sauƙaƙa mana wahala. Ko da yake, idan wasu ’yan’uwa suka daina yin amfani da turare domin suna son wani ko wata ta ji daɗin halartar taron ikilisiya, hakika hakan sadaukarwa ce ƙwarai. Amma za mu iya yin hakan don muna ƙaunar ’yan’uwanmu.

 Masanan tarihi sun tabbatar da zaman Bilatus Ba-bunti ne?

Dutsen da aka rubuta sunan Bilatus a kai da yaren Latin

Masu karanta Littafi Mai Tsarki sun san da zaman Bilatus Ba-bunti don abin da ya yi a lokacin da aka wa Yesu hukunci kuma aka kashe shi. (Mat. 27:1, 2, 24-26) Amma sunan Bilatus Ba-bunti ya bayyana a wurare da yawa a wasu rubuce-rubucen ’yan tarihi. Ƙamus mai suna The Anchor Bible Dictionary, ya ce littattafan tarihi da suka yi magana game da shi “suna da yawa sosai kuma sun yi bayani dalla-dalla a kansa fiye da duk wani gwamnan Roma da ya yi mulki a Yahudiya.”

Sunan Bilatus ya bayyana a yawancin rubuce-rubucen ɗan tarihin Yahudiya mai suna Josephus. Ya ambaci takamammun abubuwa uku da suka shafi matsalolin da Bilatus ya fuskanta a lokacin da yake mulkin Yahudiya. Wani ɗan tarihi Bayahude mai suna Philo ne ya ambata na huɗun. Wani ɗan Roma marubuci mai suna Tacitus ne ya rubuta tarihin sarakunan Romawa kuma ya tabbatar da cewa Bilatus Ba-bunti ne ya ba da izinin kashe Yesu a lokacin da Tiberius yake sarauta

A shekara ta 1961, ƙwararru masu tonon ƙasa da suka yi aiki a gidan wasannin Romawa da ke Kaisariya, a Isra’ila, sun gano wani dutse da yake ɗauke da sunan Bilatus da aka rubuta a yaren Latin. Wannan rubutun ba cikakkensa ba ne amma an ce a asali rubutun yana cewa: “Gwamnar Yahudiya, Bilatus Ba-bunti ya saɗaukar da wannan ginin ga alloli masu girma.” Wannan gini da ake maganarsa wataƙila yana nuni ga wani haikali da ke ɗaukaka Sarkin Roma mai suna Tiberius ne.

Wajibi ne ’yar’uwa ta ɗaure ɗankwali kafin ta gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki a gaban ɗan’uwa?

An rubuta a wani talifin “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” na Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2002, ta Turanci cewa ya kamata ’yar’uwa ta ɗaura ɗankwali idan tana nazarin Littafi Mai Tsarki a gaban mai shela, ko da ya yi baftisma ko bai yi ba. An sake bincika wannan batun kuma an ga cewa ya dace a yi gyara.

Idan mai shelan da ke tare da ’yar’uwar sa’ad da take gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki ya yi baftisma, zai dace ’yar’uwar ta ɗaura ɗankwali. Ta hakan, tana biyayya ga umurnin Jehobah ga tsarin shugabanci a cikin ikilisiyar Kirista, don koyarwa aiki ne da ya kamata ɗan’uwa ya yi. (1 Kor. 11:5, 6, 10) A wani ɓangaren kuma, za ta iya gaya wa ɗan’uwan ya gudanar da nazarin idan ya cancanta kuma idan zai iya yin hakan.

Amma idan tana tare da mai shela wanda bai yi baftisma ba kuma ba mijinta ba, bisa ga ƙa’idar Nassi, ba wajibi ba ne ta ɗaura ɗankwali. Duk da haka, ’yar’uwa za ta iya ɗaura ɗankwali a wannan yanayin ma idan ta ga dama.

^ sakin layi na 2 Don samun ƙarin bayani, ka duba Helping Those With MCS,” a mujallar Awake! na 8 ga Agusta, 2000, a Turanci shafuffuka na 8-10.